← Book details Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 133

Sashe 27

Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"KuÉ—i na É—auko masa Safeera, kuÉ—i masu yawa na na É—auko a gidan har rafar dala É—ari."

Safeera ta ce, "kamar ya kin É—auko masa kuÉ—i? Shi wa ki ka É—aukarwa kuÉ—in?."

"Shi wanda ban san shi ɗin ba mana. Na faɗa miki a inda na san shi, shine wanda ki ka tarar ina yiwa masifa a car park ɗin asibitin da Baffa yake a kwance, kafin haɗuwar mu a asibiti mun taɓa haɗuwa dashi a diamond hotel, lokacin da muka je ganin Mr Rehaan."

"Ni fa ban gane me ki ke nufi ba"

"Shi É—in da nake faÉ—a miki, shine ya saka aka É—auke ni."

"dan kawai kun haɗu sau biyu saɓani ya shiga tsakanin ku sai ya ɗauke ki?."

"Haka ne wallahi. Haƙuri yake so na basa ni kuma ba ƙi, dan ban ga laifin da na yi masa da zai bani haƙuri ba. A lokacin da yace a dawo dani gida sai naga kuɗin, kawai sai aikin Baffa yazo raina, na fara tunanin ko an samu kuɗin aikin ko ba a samu ba. Kuma sai na yi mafarki, aka nuna min rashin kuɗin aikin ya saka Baffa ya rasu....."

Ta yi shiru tana ajiyar zuciya, ta rufe ido ta buÉ—e ta ce, "shine na É—auko rafa É—aya na biya kuÉ—in aikin Baffa. Amma wallahi ba da niyar sata na É—auko masa kuÉ—i ba, ara nayi, kuma zan nemo kuÉ—in a duk inda zan nemo na biya sa in sha Allah."

Safeera ta zuba mata ido cike da mamaki ta ce, "ki biya wa?."

"Shi baturen mana."

"A ina zaki gansa keda baki san sunansa ba?." Islsha ta yi shiru bata ce komai ba.

Ganin kallon ban yarda dake ba da Safeera take yi mata, sai ta rikice ta ce, "Wallahil azim da gaske nake, iya abinda ya faru kenaan Safeera."

Safeera sai a lokacin ta gamsu, dan ta san baza ta taɓa yi mata rantsuwa akan ƙarya ba. Safeera ta ce, "ke meye ya kai ki aikata sata? In akwai cctv a gidan ya gano ki fa? In ya saka aka yaɗa ki a duniya fa? Ko kuma ya saka kama ki da laifin sata, laifin waye?."

"Wallahi Allah ba da niyar sata na É—auka ba, da niyar aro ne, kuma ni ban san haka kuÉ—in suke da yawa ba, nayi tunanin basu kai yawan haka ba. Kuma sai da na É—auko na dinga danasani."

"Rafar dala É—ari ki ka ce, faÉ—a min a gidan da zaki samo kuÉ—in nan, kuÉ—in da sun kai miliyan goma? A ina za ki samo su?."

"Miliyan sha bakwai ne Safeera."

"FaÉ—a mina gidan da za ki samo waÉ—annan kuÉ—in Islaha."

Islaha ta yi shiru bata ce komai ba tana tunanin mafita, dan ita kanta bata san a inda zata same su ba. Safeera ta ce, "tunda baki da hanyar su sata ki ka yi masa. Ke ko kina da hanyar da zaki biya shi wallahi sata ki ka aikata, ba wani rance, tunda ba shi ne ya baki da kansa ba, baki tambaye shi ba ki ka É—auka. Kawai kin gani ya ajjiye, ke kuma ki ka É—auka, kinga kenan satar masa kuÉ—i ki ka yi."

"Kuma yadda ki ke faÉ—ar bature ne zai iya sakawa a kama ki, wannan laifin zai shafe wanda ya yi miki, domin ke baki da hujjar shine ya sace ki, amma shi na san bazai rasa cctv da ta É—auke ki a lokacin ba. Da yawan gidajen masu kuÉ—in nan akwai cctv a falon su, in hakan ta kasance wannd abin kunya ki ka É—auko mana?."

Gaban Islaha ya faÉ—i, ta shiga tuna lokacin da ta kalli camera ta yi magana, hakan yana nufin an É—auke ta kenan.

Islaha ta rikice, ta girgiza kai tana ɓoyewa Safeera gaskiyar akwai camera a falon ta ce, in sha Allah babu camera Safeera, in Allah ya yarda bai gani ba......"

"Na shiga uku! Safeera a ina zan samu kuÉ—in nan na biya shi? Wallahi ko meye zan aikata indai zan biya shi kuÉ—in nan. In na mutu ban biya shi bashin nan ba ya kenan?."

"Ni mamaki ma ki ke bani, ina jinjina ƙarfin halin ki wallahi. Ke da aka sace, har kina da damar ɗauko kuɗi? Yaushe ki ka koyi ki gani ki ɗauka Islaha?."

"Ni dai tsoro nake ji."

"Da ba ki yi wannan tunanin ba ki ka É—auko masa kuÉ—in?."

"Wallahi Baffa ne a raina, kuma na yi nadama wallahi."

"Sata sunan ta sata, kin gani kin É—auka sata ce ba rance ba. FaÉ—a min ta hanyar da zaki biya shi kuÉ—in sa."

Islaha ta yi shiru, cikin sanyin jiki ta ce, "ina jin na canja wajan aiki kawai, zan nemi inda a kwanaki kaÉ—an zan haÉ—a masa kuÉ—insa na nemi duk inda zan gan shi na mayar masa."

"Ai indai ba turai za ki koma da aiki ba, babu inda zaki samu waÉ—annan kuÉ—in a kwanaki kaÉ—an. Ki faÉ—i abinda zai yu, ba wannan maganar ba."

Ta É—an yi shiru tana nazari, ta rufe ido ta buÉ—e kafin ta ce, "film zan shiga."

Safeera ta harare ta cike da takaicin maganar ta, Islaha ta ce, "in na shiga film zan iya haÉ—a kuÉ—in na biya shi, daga nan sai na daina."

Safeera ta bita da kallon up and down ta ce, "Islaha anya ƙalau ki ke?."

"Lafiya ta lau wallahi."

"To an faɗa miki ana shiga film ɗin ake samun kuɗi? Ko su ƴan film ɗin sai sun yi haƙuri da juriya sannan suke samun ribar abun, ba da an shiga ake tara kuɗi mai yawa ba, sai kin yi aiki da jikin ki sannan za ki samu."

Islaha ta dafe kai ta rasa abinda yake yi mata daÉ—i, kawai ta fara hawaye ta ce, "Safeera ban san ya zan yi ba, ban san me zan yi na samu kuÉ—in nan na biya shi ba. Saboda wannan dalilin bana so a yi bincike akan case É—in nan, saboda haka bana so a É—aga maganar, dan na san dole maganar kuÉ—in nan ta fito. Da wanne ido zan kalli Hamma in ta bayyana na yi aron kuÉ—i masu yawan wannan? Da wanne ido za a cigaba da kallona a gidan nan?."

Safeera ta riƙe hannunta ta ce, "dan kuskure kin yi kuskure babba Islaha, sai dai a kiyaye gaba a yi ƙoƙarin gyarawa. Kuma duk waɗanan hanyoyin da ki ke faɗa babu wacce zata baki kuɗi lokaci guda wallahi, dole sai kin yi a hankali, kin ƙara da haƙuri. Baki da wata mafitar da za ki samu wannan kuɗin indai ba sassan jikin ki zaki siyar ba. Ni a shawara ta, kawai ki neme shi ki ba shi haƙuri ya yafe miki, sannan ki bar case ɗin sace ki da ya yi ya wuce, shima ya rufe miki asirin satar da ki ka yi masa."

"Ni fa ba sata na yi ba, aro na yi."

"Wallahi sata ki ka yi, ki daina faÉ—ar wannan maganar hajiya. Sata ce mai lasisi."

"Ni ba sata nayi ba, bashi ne kuma kowa yana ci."

"Sai ki yi ai, in zaki haƙura ki yarda kin sata ki haƙura, ki neme shi ki bashi haƙuri a wuce wajen. Kin ga jefi tsuntsun biyu da dutse ɗaya, kin biya kuɗin aikin Baffa, kuma kin sauke nauyin da yake kan ki."

"Ni yanzu a ina zan ganshi?."

"da ki ka É—auko masa kuÉ—in har ki ke zancen biya, a ian zaki ganshi ki bashi?."

Ta girgiza kai ta ce, "Safeera, ɗan rainin hankali fa, gaskiya ni bazan taɓa basa haƙuri ba."

Safeera ta bita da kallon mamaki ta ce, "a wannan gaɓar tsiwa ko masifa babu abinda zata amfana miki danasani, gwara ki yiwa kan ki faɗa, ki nema shi ku sasanta akan hakan."

"Bazan ba shi haƙuri ba, zan dai neme ko aiki ne nayi a ƙarƙashinsa."

"In ya ƙi fa?."

"Zan san hanyar da zan bi ganin na nemo kuÉ—in da zan biya shi, ko meye zan yi."

Safeera ta ce, "ki daina cewa ko meye zaki yi fa islaha, in kina faÉ—ar hakan wani zai É—auka kamar zaki fara bin maza ne dan ki biya bashi."

Ta É—ago jajayen idonta ta kalle ta, Safeera ta ce, "yes, gwara ki kwantar da hankalin ki ki daina wannan maganar, ki yi addu'a Allah ya warware wannan chakwakiyar.."

"Amma nima a yanzu bana goyan bayan bincike akan case ɗin na, tunda lamarin ba daga inda muke tunani ya zo ba, ba daga wajan cutarwa ya zo ba, kinga da sauƙi. Ko ni bazan so a yiwa sunan ki tambari da Islaha ɓarauniyar dala ba."

Islaha ta sake fashewa da kuka cikin takaici da ƙunar zuciya, danasani da raɗaɗi. Tabbas sai ta biya sa kuɗin sa, duk hanyar da zata bi zata bi dan ganin ta biya bashin nan, baza ta bar bashi akanta ba.

Safeera ta yi dariya ta ce, "To meye na kukan? Ko kin ƙi, ko kin so, sunan ki Islaha ɓaraumiyar dala."

Islaha ta sake fashewa da kukan takaici, Safeera ta yi dariya sosai ta ce, "Kar ki damu, komai zai wuce. Daman ance masu kuɗin nan da daloli suke yawo, yanzu an daina riƙe naira sai daloli." Islaha bata ce komai ba saboda takaici, tunanin ta ɗaya a ina zata samu kuɗinsa ta biya shi? Dan gaskiya baza ta bar bashi a kanta ba, dole ta sauke nauyin da ya hau kanta.

Har dare suna tare da Safeera, a lokacin Mama da Labiba da Hanan suka dawo gida.

Islaha da suke cikin É—aki suka fito suka yi mata sannu da zuwa, Mama ta amsa tana faÉ—in, "Asibiti kamar na kafurai, wai ba a zama jinya ma'aikatan ne suke jinyar mara lafiya." Islaha da Safeera suka koma É—aki basu tanka ba.

Sai da suka shiga sannan Safeera ta ce, "Asibitin Mr Ray É—in nan akwai abin mamaki, komai irin na turawa yake yi. Kin san asibitin turawa ne ba a ajjiye mai jinya, nurses ne suke jinyar marasa lafiya."

Ita dai Islaha bata ce komai ba tana zaune ta yi shiru. Ba Mr Ray ne a gabanta ba, kuÉ—in wanda bata sani ba shine a gabanta.

Safeera ta girgiza kai ta ce, "yaushe zaki dawo aiki?."

A sanyaye ta ce, "Gobe in Allah ya yarda."
Chapter 27 · 0% Book details