← Book details Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 133

Sashe 33

Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Umma ta ce,"babu komai."

Ya girgiza kai ya ce, "da girman ki, da shekarun ki, da ƴaƴan mata duk sun kai munzalin aure, ke da kanki kike so ki tsallake su ki bar ƙasa saboda abin duniya Maimuna?."

_Shikenan, ta faru ta ƙare._

Umma ta faÉ—a a zuciyarta, cike da jin haushi da takaici, dan ta san tunda mutanen Katsina suka ji maganar ta shiga uku.

Alhaji Yakub ya ce, "Wallahi ko a mafarki ban yi tunanin zaki aikata wannan ɗanyen aikin har haka ba, ban yi tunanin shirmen ki da rashin girman naki ya kai haka ba sai yanzu. Ke yanzu za ki iya ɗaukar ƙafa ki bar ƙasa, ki bar mijin ki da ƴaƴan ki saboda duniya don Allah?."

Umma ta sunkuyar da kai bata ce komai ba, dan ta san bazai taɓa bata damar magana ba, ko ta faɗa bazai fahimce ta ba ko kaɗan.

Cikin faɗa ya ce, "dan tsabar shirme da neman duniya? Ki rufe ido ki ɗauki ƙafa ki tafi wata ƙasa ki bar yaran ƴan mata a Nigeria, in ba shirme da rashin hankali me meye amfanin wannan?."

Nan ma bata tanka ba ya ce, "kin rasa ci da sha a gidan nan?."

Ta girgiza kai alamun a'a ya ce, "faɗa min dalilin ki na tafiya, faɗa min dalili mai ƙarfi da ya saka ki ke son barin ƙasar nan ki tafi aiki wata ƙasa."

Umma ta kasa cewa komai, dan duk da Baba bashi da kuɗi amma yana ƙoƙarin ganin ya tsare musu komai na rayuwa. Ilimi, abinci, suttura da sauransu duk basu rasa a gidan ba, in ta faɗi wani abu makamanincin haka ta yi masa ƙarya.

Ya ce, "ina jin ki."

Umma ta ce, "babu komai."

"Haka kawai ki ke neman ɓata rayuwar ki, da girman ki da shekarun ki kike son mayar da kan ki baya?. Abinda baki yi da kina ƙarama ba, shi zaki yi yanzu da ki ka isa ajjiye jika? Kar ki manta, an saka kawo kuɗin auren ƴarki Safeera, ko kunyar hakan bakya ji za ki saka wannan shirmen da ya zama ruwan dare a zuciyar ki?."

Umma ta ce, "Yaya da farko ban yi niyar zuwa ba, sai da na faɗa masa ya ƙyale Safeera ta je amma sai ya ce indai shi ya haife ta wallahi bazata je."

"To faɗa miki aka yi shi mahaukaci ne irin ki? Ko an faɗa miki bai san abinda yake yi ba kamar yadda baki sani ba?. Haka kawai ki ɗauki yariya budurwa ki sahale mata ta tafi wata ƙasa aiki? Ba tare da kin san da wa ki ka haɗata ba, baki san a ina zata sauka ba, baki san a hannun wa zata zauna ba? Kedai kawai ta je ta samo miki kuɗin da baki san ta hanyar da za a samu ba ko?."

Umma ta kalle sa ta ce, "Aiki ne fa kawai Yaya, aikin gida ne irin na gidan larabawa ko gidan turawa, ba wani abu ake aikatawa a can ba."

Ya yi shiru kawai yana kallon ta bai ce komai ba dan bai san me zai ce ba, dan shima ya ga lamarin nata da gaske take ba da wasa ba.

Jin ya yi shiru sai ta É—ago ta kalle sa taga ita yake kallo, ta sunkuyar da kai sai kuma ya ce, "Mahaifi. Safeera ya hanata zuwa ne saboda ya isa da ita, tunda shine ya haife ta babu mai iko da ita kamar sa."

"Ni kuma Yayanki ne, na girme miki da shekaru masu yawa, iyayenmu basu da rai, dan haka ni ne uba a gare ni. Dan haka nima na hana ki zuwa saboda na isa dake, zan gani in na isa dake in ban isa dake ba."

"Banda lalacewa da shirme, da girmanki da shekarun ki zaki ɗauki ƙafa ki ta fi wata ƙasa aikin gida? Anya kina da hankali kuwa?."

Baba dai yana zaune ya yi shiru bai ce komai ba, Yaya ya kalle sa ya ce, "Anya tana da hankali?."

Baba ya É—an murmusa ya ce, "tana da hankali, kawai wani abun ne ya rufe mata ido."

"A'a, mai hankali bazai aikata abinda take aikatawa ba. In da ace tana da hankali baza ta yi kwatankwacin wannan shirmen ba. Tafiya aiki fa take tunanin yi wani waje, ba cikin yola ko cikin nigeria ba, jirgi zata hau ta bar ƙasa. Kuma wai ita irin huce haushin nan zata yi, wato an hana Safeera tafiya ita bara ta je da kanta, tunda kaine ka haifi Safeera kuma ka hanata zuwa, to ita ai baka haife ta ba. Abinda take nufi kenan, shiyasa take wannan maganar."

Baba dai ya yi murmushi kawai bai ce komai ba, dan kuwa haka Umman ta faÉ—a masa, Safeera ya haifa ba ita ba.

Yaya ya ce, "in ban da lalacewa ma, ƙasa kamar Nigeria amma ace wai matan cikinta ne suke fita su tafi wata ƙasashen larabawa yin aikii kamar wasu gantallalun mutane?. Tsakani da Allah wanne farar fatar ne ya taɓa zuwa nigeria yake aikin wanke-wanke da shara a gidan baƙaƙe fata ƴan Nigeria?."

Baba ya ce, "babu."

"Amma mu mun mayar da kan mu baya, babu abinda ƙasashensu suka fi mu dashi, dan dai kawai lalacewa irin ta ƙasar ta mu, an ɗauki hakan a matsayin ba komai bane."

Ya juyo ya kalle ta ya ce, "Ahir Maimuna! Kar na ji kar na gani, kar na sake jin wannan maganar mai kama da wasan yara. Ki adana wannan shirmen a gefe, ki cire shi daga ranki ki kalli gaban ki. Wallahi in n kuma jin wata magana makamanciyar wannan sai na ɓata miki rai. Kin ji ko?."

Umma ta É—aga kai ta ce, "na ji."

"Yauwa, maganar ta tsaya iya haka, maganar ta ƙare a iya falon nan, maganar ta tsaya a nan wajan. In kina niyar tafiya ma ki tabbatar kin daina, wallahi in wani abun ya sake faruwa sai na saɓa miki, kin ji na rantse."

Umma ta ce, "in Allah ya yarda babu abinda zai kuma faruwa."

Ya ce, "ya fi miki. Kome ki ke hange da zai saka ki kai rayuwar ki can, in so ki san komai lalacewar nan ɗin shine dai jin daɗi ki, baza ki je ki ɗauko farin ciki da walwala ba, in kika sake ki ka bar gidan nan, wallahi kin yi bankwana dasu har abada. Abinda suke faɗa miki zaki samu a can roman baka ne, suna kwaɗaita miki abinda zai saka ki ji ranki yana so, amma in kin je akasin hakan zaki tarar. Kin girma, wannan shirmen duk ba naki bane, kin taso a gidan tarbiyya ,kin samu ilimi daidai gwargwado, wannan shirme da ɓata lokacin duk bai kamace ki ba."

Umma tayi shiru bata ce komai ba. Ya ce, "kin ji me nace ko?."

"Na ji Yaya, in sha Allah ta wuce."

"Haka ake so."

Ya kalli kunun ya ce, "zan tafi da kunun nan, in anjima zan bayar a dawo da flaks ɗin. Wannan ki bawa yaran" ya faɗa yana miƙa mata kuɗi. Ta karɓa fuskar ta babu walwala sosai, dan ji take an takura mata an matsawa rayuwar ta an hanata abinda take so. Sama-sama take amsawa, babu walwala ko kaɗan a tare da ita. Daga haka dai suka yi sallama Yaya ya tafi ya barta da tunani.

Nana Haleema.
[6/26, 12:30 PM] KRBBK: RDB2P23
Nana Haleema.

Islaha tunda Saleem ya taho kawo su gida daga asibiti wajan Baffa ta yi shiru bata cewa komai. Saleem da Safeera ne suke magana sama-sama, ita dai bata saka musu baki.

Saleem yana tsayar da motar Islaha ta ce, "Safeera zo mu je gida mu yi magana don Allah."

Safeera ta kalle ta ta ce, "me ya faru?."

Islaha ta ce, "ki zo mu je" tana faÉ—a ta buÉ—e motar ta buÉ—e gidan dan babu kowa duk basa nan ta.

Saleem ya kalli safeera bayan Islaha ta shiga gida ya ce, "ƙawar ki tana da damuwa, tun daga dawowar ta daga ɓacewar da ta yi, na tabbatar tana da wata matsala da take ɓoyewa."

Safeera ta ce, "nima naga hakan, in na tambaye sai ta ce min ita babu komai. Amma bara na je na ji me zata ce min. Ka gaishe da Mama don Allah."

Ya wani kalle ta ya ce, "ba wani na gaishe ta, ko sau ɗaya baki taɓa zuwa kin gaishe ta ba."

Ta buÉ—e ido waje ta ce, "bafulatana ce ni fa, da kunya aka san mu. Ina ni ina zuwa gidan ku gaida Mama?."

"Ko ba bafulatama ba" ya faÉ—a yana hararar ta cikin wasa da soyayya. Murmushi ta yi ta buÉ—e motar ta fita shi kuma ya wuce gida.

Safeera a zaune ta samu Islaha ta riƙe ciki tana cize bakinta, Safeera ta ce, "ya dai? Period ɗin ne?."

Ta girgiza kai ta ce, "ovalution ne."

"Tabɗi! Kina ƙoƙarin gane lokacin ovalution cycle ɗin ki, ni wallahi mantawa nake yi" ta faɗa tana zama a kusa da ita.

Safeera ta ce, "ina jinki, lafiya?."

Islaha ta É—an sauke numfashi ta kalli Safeera ta ce, "a duniya bani da wani daga ke sai Hamma. Bani da iyaye, inda na taso kuma gida ne na kowa da kowa, ba wani nake dashi da zan je na yi sirri dashi ba. Ke kaÉ—ai nake da ita wacce nake faÉ—awa damuwata na ji daÉ—i. Safeera..." sai kuma ta yi shiru bata ce komai ba.

Safeera a sanyaye ta ce, "ina jin ki, zaki jefa zuciyata cikin dogon tunani Islaha."

"Akan kuÉ—in mutumin nan ne, wallahi kullum sai na yi mafarki mara kyau akan hakan. Ban san tautsayin da ya kaini aikatawa ba, gashi gabaÉ—aya na kasa nutsuwa."

"Kin saka abin a ranki ne shiyasa ki ke mafarki akan abun. Wani mafarin yana zuwa ne in ka saka wani abu a zuciyar ka kana tunaninsa, yawan tunanin sai ya jawo ka yi mafarki akan hakan."

"Hanyar da zan biyasa kuÉ—insa nake nema Safeera. Ta wacce hanya zan samu kuÉ—in?."
Chapter 33 · 0% Book details