Sashe 133
Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Jazy ya ce, "Okay let me call him, ya kawo min ita. Ka san Abba ya wakiltani na je na É—auko amaryar ka, da ita za a É—auko ta."
Ray ya yi shiru bai ce komai ba har ya gama kiran Shams. Bayan ya gama wayar Jazy ya ga Ray yana kallonsa suna haÉ—a ido Ray ya ce, "meyasa ba ka É—auki private get ba sai RR?."
Jazy ya yi dariyar shaƙiyanci ya ce, "ai wallahi da ace Islaha a wajen Yola ta ke ba cikin Yola ba, da private get za a ɗauko ta, yanzu ma dan abin ya zo late ne, da hilicopter zan tasa ya ɗauko ta, Matar Ray ce fa."
"Mtsww! Yanzu me ya hana ka tashi helicopter É—in? ÆŠan neman suna" ya faÉ—a yana miÆ™ewa tsaye tare da saka hannu a gashin kansa yana yamutsawa.Â
Shima ya miƙe ya ce, "na faɗa maka lokaci ne ya ƙure, amma da wallahi bazata zo gidan nan a mota ba, sai a jirgi."
"Ta zo a iska ma."
Jazy ya ƙyalƙyale da dariya ya ce, "lallai ka ji hausa mutumina, baki yana ta buɗewa....."
"Zan je na dawo, ka san ina da amarya sabuwa da za a kai min ita in anjima, bazan ɓata lokaci ba. Matsayina da naka yanzu da banbanci, ni auren sadaki na yi, kai kuma auren yarjejeniya ne, bazan ɓata lokaci a nan ba." Banza ya yi masa ya shige ɗaki bai ce masa komai ba, shi kuma ya yi dariya ya fita.
Baffa ne ya saka Safeera shiryawa Islaha kaya Æ´an kaÉ—an da zata tafi dasu, ta dole aka saka ta yi wanka dan gabaÉ—aya ta fita hayyacinta, tana jin daÉ—i da Hamma yake bacci tunda ya sha magani.
A haka ta shirya cikim atamfa doguwar riga da veil É—inta mara tsaho sosai. Safeera ta bita da kallo ganin mayafin da ta É—auko ta ce, "wannna mayafin bazai rufe miki fuska ba, babban mayafi ake sakawa."
Islaha ta harare ta da jajayen idanunta da suka kumbura ta ce, "sai aka ce miki zan rufe fuska ne daman?."
"Haka amarya take zuwa gidanta fuska a buÉ—e?."
"Wace amaryar?."
"Shafa ki ji."
Islaha ta share ta ta É—auki handbag É—inta kamar wacce zata je unguwa, sai kuma ta ajjiye jakar ta ce, "ai gobe ma zan fito, ba sai na É—auki wani abun ba."
Safeera dai tana kallon ikon Allah kawai take yi, ganin yadda Islaha take yin abubuwnta kamar ba amarya ba. Har sai da Baffa ya shigo da kansa sannan suka fita daga É—akin.
Tana fitowa daga É—akin Saheer yana shigowa falon yana tafiya a hankali cikin yanayin rashin lafiya, zuciyarsa tana tuna masa abubuwa da yawa a can, yana ta tunanin amanar da aka bari a hannunsa, wacce ya taho ya bari a hannun masu garkuwa da mutane.
Saheer ya tsaya yana kallon Islaha, ganinta tare da Baffa da kuma Safeera. Bai yi tunanin komai ba, dan ya yi tunanin fita zata yi.
Baffa ya kalle sa ya ce, "Saheer ka tashi kenan?."
Ya É—aga kai cikin dashewar murya ya ce, "na tashi."
Baffa bai ce komai ba ya kalli mutanen falon da suke zaune, sannan ya ce, "ku yi mata fatan alkhairi, yau Allah ya É—aga darajarta zata bar gidan nan zuwa gidan mijinta."
Ita kanta Ialaha sai da gabanta ya faÉ—i, ta kalli Saheer ta gefen ido ta ga ya zubawa Baffa ido yana kallon sa. Baffa ya kalli Saheer ya ce, "ka jira ni, in na dawo zan yi maka bayanin komai."
"Wanne bayani za a yi masa da ya wuce wanda ya gani yanzu? Da kai da Islaha kun zaɓi kuɗi akan halacci, kun ɗauke ta kun aurar da ita bayan ka san yadda yake tsananin ƙaunar yarinyar nan. Me za a ce masa kuma?."
Saheer ya ji kalaman Mama kamar an doka masa guduma a tsakiyar kansa, daman ga rashin ƙarfin da yake fama dashi, ya dafa bango jin jiri yana ƙoƙarin kayar dashi, ya kalle ta ya ce, "aure kuma Mama?."
Mama ta ce, "eh aure, ya aura mata É—an gidan AbdulAziz Yola. Wani yaro mahaukaci, shi ya aura mata saboda ya fi ka kuÉ—i. Maganar da nake yi maka yanzu matar aure ce a gabanka!."
Saheer ya buɗe ido tana kallon Mama, ya dawo da kallon sa ga Islaha da kanta yake a ƙasa, sannan ya kalli Baffa alamun ƙarin bayani.
Baffa ya ɗaga masa kai alamun tabbatarwa ya ce, "eh gaskiya ne, shiyasa na ce zan yi maka bayani. Yanzu zan saka ta a motar da zata kai ta gidan miiinta, in na dawo sai mu tattauna. Islaha mu je" ya faɗa yana riƙo hannunta suka fara tafiya.
Saheer ya dafe kai da hannayensa duka biyun ya ce, "Baffa wai da gaske ka ke?."
"Da gaske nake Saheer."
Saheer ya ji ɗakin yana juya masa, ya dinga maimaita salati a bayyane yana kalle-kalle dan ji yake kamar ana juya ɗakin da yake ciki, kamar ana juya duniyar tana sama da ƙasa.
Baffa ya sake riƙe hannun Islaha da ta sunkuyar da kai ta ƙi ɗagowa, bata son haɗa ido da Saheer dan bata san me zata ce masa ba.
Saheer ya ji kamar numfashinsa zai ƙwace, ya runtse ido yana kallon Islaha ya ce, "Islaha da gaske gidan wani za ki tafi ko wasa ku ke yi min? Kin san bana jure wannan wasan ko? Kin san bana son wasa da zuciya, ki faɗawa Baffa ya ce min wasa yake yi."
Islaha ta tsaya cak ta kasa cigaba da tafiya, ta É—aga ido tana kallonsa da idanunta da suka canja amma ta kasa magana.
Baffa ya ce, "Saheer ba wasa nake yi maka ba, ka jira na saka ta a mota na dawo ko meye za aka ji."
"Baffa wasa ne wannan, na san tsokanata ka ke yi. Kai da kanka ka faÉ—a min ka fini son na auri Islaha, meyasa za a yi min wasa a daidai irin wannan lokacin?. Baffa likita ya ce ina buÆ™atar hutu, meyasa ka ke yi min wannan wasan a daidai wannan lokacin?.â€
Baffa ya kalli Saheer ya ga in ya tsaya sauraren Saheer zasu ɓata lokaci sai ya ce, "Islaha mu je."
A hankali take take bin bayan Baffa, ko gabanta bata kallo janta kawai yake yi tana tafiya tana kallon ƙasa tana kuka. Saheer ya biyo bayansu yana fitowa harabar ya ce, "Islaha!."
Ta tsaya cak ta ƙi bin Baffa, jikinta ya hau rawa, raunin zuciyar ta ya bayyana, ta kasa cigaba da daurewa, ta zube guiwar ta a wajen ta ɗurƙushe tana kuka.
Baffa ya waiwayo ya ce, "Saheer matar wani ce, ka daina karya mata zuciya, zan zo mu yi magana."
Saheer bai kula Baffa ba ya ce, "Islaha da gaske ke matar wani ce ba ni ba ko wasa ake yi min? Islaha ki ce min mafarki ne, in kuma a gaske ne ki faÉ—a min film ake É—auka, ki faÉ—a min script ki ka karanta ki ke acting a kai, ba gaskiya bane.â€
Bata iya magana ba sai kukan da take yi a ɗurƙushe tana ji kamar Allah ya ɗauki ranta a take a wajen, Baffa ya ɗago ta taƙi motsawa ta ce, "Baffa na fasa, bazan tafi ba, don Allah ka bar ni a nan!."
Yadda jikinta yake rawa haka muryarta take rawa, Baffa bai fasa ba ya ɗago ta ya ce, "Islaha mu tafi" ya sake riƙe hannunta dakyau yadda baza ta iya ƙwacewa ba, ya cigaba da janta har suka fita daga gidan.
Suna fita ƙofar gidan suka tarar da motar a ajjiye, Jazy yana zaune a ciki yana danna waya. Ganinsu ya saka shi ya fito, ya yimurmushi suka gaisa da Baffa cikin girmamawa.
Baffa ya ce, "Gasu nan."
Jazy ya bi Islaha da kallo ganin tana yadda take kuka jikinta yana rawa sosai, sai ya yi mamaki sosai, dan bai yi tunanin haka ba tunda ta san a yadda suka É—ora auren nasu, a ganinsa meye na kuka?.
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!"
"Shikenan ta kashe min É—ana!."
"Saheer! Saheer!! Saheer!!!."
Lokaci ɗaya muryar Mama ta shiga kunnensu cikin ƙaraji mai nuni da tsananin tashin hankali.
Wata irin zabura Islaha ta yi zata koma, Baffa ya riƙo ta ya haɗe rai cikin ba da umarni ya ce, "shiga ki tafi."
Islaha cikin wani irin yanayi, ta girgiza kai murya tana rawa ya ce, "Baffa……â€
“Ham….ma…!."
"Na san da Hamman na ki na ce ki tafi, na san abinda nake yi, ba ki fini sanin daidai ba."
Baffa ya kalli su Mama Atika ya ce, "Safeera, Atika ku shiga ku rakata, Allah ya kiyaye ya sa an shiga a sa'a. Dan ma ban shirya zuwa bane, da ni zan kai ta da kaina."
Baffa ganin Islaha da gaske ta ƙi shiga motar, sai ta buɗe motar da kansa ya saka ta shiga ciki, ya rufe motar ya kalli Jafar ya ce, "Allah ya kiyaye hanya."
Jazy ya ce, "Amin Baffa. Mun gode Allah ya Æ™ara girma.â€
Safeera ce ta shiga gaba, saboda ta san dai Jazy ba driver bane balle ta shiga baya, kuma ta ga motar ta Æ´an gayu ce kamar mutum biyu kaÉ—ai ne suke zama. Mama Atika ta shiga kusa da Islaha, Jazy ya shiga motar ya ja ya suka bar unguwar a guje....
End of book 2
Tofa!😂🔥💃ðŸ»
_Wai ta zata kasance ne? Ya zaman Islaha zai kasance ita da Ray? Ya batun zaman nasu, zai ɗore ko zai lalace? Ya zata yi da Saheer?. Ya haɗuwar Mamy da Islaha zai kasance? Ina labarin Labiba da Umma? Ina labarin Zainab da ta ɓace?. Wacce irin rawa Islaha zata taka a gidansu Rehaan? Ya labarin Mama da take jiran shigowar Islaha gidansu Rehaan?. Shin zata auri Saheer ne ko a'a?. Ina labarin Alma? Ina labarin Ummi da Muslim?. Waye yake ƙoƙarin ganin bayan Rehaan? Za su yi nasara ko kuma baza su yi nasara ba?._
Mu haÉ—e a book 3. Ni dai ina ba ku shawara, ko ba ku karanta book 1&2 ba, to ku maÆ™alewa book 3.ðŸ˜ðŸ˜ðŸ”¥
Nana Haleema.