← Book details Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 133

Sashe 75

Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta yi murmushi, ba dole son Hamma ya cigaba da ninkuwa a ranta ba, ko maganar ta ya ji ta canja sai ya tambaya. Wani lokacin sai ta ɓoye masa damuwar ta, amma da ya ga fuskar ta sai ya ce me yake damun ki. Kulawar da yake bata tana sakawa ta ji ta kai wani mataki a zuciyarsa, tana jin ta kamar sarauniya, tana jin ta kamar gimbiya.

Ta sauke numfashi ta ce, "na samu attack, ban jimawa da dawowa daga asibiti ba."

"Subahanallahi! Ya jikin naki, kin samu sauƙi?."

"Na ji sauƙi sossi. Har test aka yi min, kuma ka san an ga asthma ɗin, amma bata da yawa. Har inhaler an bani."

"Kin ga banbancin ƙasar mu da ƙasar waje kenan. Amma sun baki magani ko?."

"Sun bani Hamma, har da inhaler. Mutanen gidan suna kirki sosai wallahi, ba ka ga yadda hankalin matar gidan ya tashi ba. Yanzu ta shigo ta duba ni ta tafi."

"Larabawa ai suna da tausayin mara lafiya, kuma dan kin kasance mai yi musu hidima bazasu ƙi taimakon ki ba."

Ta É—an sauke nunfashi ta ce, "Ya batun Zainab? Ana bibiyar ta kuwa Hamma?."

Ya É—an yi shiru sannan ya ce, "ina bibiya Islaha, amma gaskiya kwana biyu hankalina ba ya kai tunda na koma Niger, sai na koma zan É—ora daga inda na tsaya sha Allah."

A sanyaye ta ce, "To Hamma, Allah ya taimaka."

"Amin ya rabbi. Bara na bar ki ki huta tunda ba ki da lafiya." Ta amsa ya kashe wayar ta yi shiru.

Tana son bibiyar lamarin Zainab amma bata san ya zata yi ba, kwana biyu ko wayar Suraj bata samu balle ta yi masa magana a kai. GabaÉ—aya zaman ya ishe ta, tana so ta koma gida, kuma tana so ta je Madina ta ga Umma.

•••••••

   Mama Atika ta yi shiru tana sauraren abinda Safeera tazo mata dashi, ta sunkuyar da kai tana jin maganar Safeera kamar a mafarki, kwata-kwata bata taɓa tunanin Safeera zata same ta da maganar ba, ko kaɗan bata kawo a ranta hakan zai faru nan kusa ba.

Safeera ta ce, "Mama kin yi shiru ba ki ce komai ba. Baba yana gani kamar yana takura miki, hidimar iyalansa da ki ka ɗauka ya yi yawa. In kuwa ki ka aure sa kin ga kema kin dawo ƙarƙashinsa, duk abinda ki ka yi baza a ce haka ba."

Mama ta ɗaga kai ta kalle ta ta ce, "Safeera dole na kasa magana. Baba mijin ƙawata ne fa, ta ya zan iya aurensa? Kuma ni duk abinda nake yi, ina yi mu ku shi tsakani da Allah ba dan baban ku ya aure ni ba, ban yi dan na auri baban ku ba."

"Na sani Mama. Alfarmar ki muke nema, kema za ki shiga inuwar aure, Kausar zata samu uba, mu ma zamu samu uwa, Baba zai samu mata. Kin ga kowa zai amfana da auren, ba kan ki za ki duba ba, ki duba mu da Kausar da baban. Don Allah ki amince Mama ."

Ta sauke numfashi a sanyaye ta ce, "Shi Baban naki ya amince ne?."

"Ya amince, amincewar ki kawai ake jira. Ba ma so a É—auki lokaci, ranar juma'a mu ke so a É—aura auren kawai."

Atika ta É—an yi murmushi ta ce, "da wuri haka?."

"To me za a jira? Kin halinsa, shima san halin ki, ba yau ki ka saba jin halinsa a bakin Umma ba, ba yau ki ka san abinda Baba yake yi a bakin Umma. Tunda haka ne ba sai ayi auren a wuce wajan ba?."

Ta É—an yi shiru tana murmushi, ta kalli Kausar da take kallonsu ta ce, "Kausar ba ki ce komai ba."

Kausar wacce bata wuce agemate ɗin Rukayya ƙanwar Safeera ba ta ce, "ki amince Mama, ina goyan bayan hakan."

"Bakwa ganin na ci amanar ƙawata? Ta yarda dani, ta bar min amanar gidanta, kuma ta dawo ta ga na auri mijinta?."

Safeera ta yi caraf ta ce, "babu wani cin amana, ko tana nan dan kin auri Baba ai ba laifi bane, balle kuma bata nan."

Ta ɗan yi murmushi tana jin daɗi a ranta, dan yadda ta san halin Baba yana tsarewa iyalansa komai na rayuwa, zata so ace ta aure sa ɗin. Bai ragi iyalansa da komai ba, duk ƙarfinsa akan ya nemo ya kawo musu yake ƙarewa. Za ta so ta rayu a ƙarƙashin wanda zai riƙe ta hannu biyu, ya girmamata kuma ya san darajar ta. Mama Atika ta ce, "shikenan Safeera, na amince."

Safeera ta rungume Mama cikin farin ciki ta ce, "mun gode sosai Mama, Allah ya saka miki da alkhairi, Allah ya ba ki haƙurin zama damu."

Ta shafa bayan Safeera tana murmushin jin daɗi, dan gaskiya abin ya zo mata bazata, kuma ta ji daɗi, ta karɓi auren hannu biyu.

Safeers ta miƙe ta ce, "bara na je na sanar da Baba, sai ya zo ku yi zance ko?."

Mama ta kai mata duka tana dariya, Safeera ta kauce ta fita tana dariyar farin ciki.

A zaune ta samu Baba, ta shiga kamar an cillo ta tana kiran sunansa, ya É—aga kai ya kalle ta ya ce, "Safeera lafiya?."

Ta zauna a kusa daahi ta ce, "Baba ina da wani albishir da zan yi maka."

Ya kalle ta ya ce, "ina ji Safeera."

"Mama Atika dai ta amince."

Baba ya girgiza kai cikin mamaki dan ko kaÉ—an tunaninsa bai kai wajen ba ya ce, "ta amince da me?."

Ta ɗan ɓata fuska ta ce, "auren mana."

Ya riƙe haɓa ya ce, "Yanzu Safeera zuwa ki ka yi ki ka same ta? Ni na ce miki ki je ku yi maganar nan ne?."

"Baba ai ka amince, itama amincewar ta na je nema kuma na samu. Yanzu kawai ayi magana a É—aura auren ranar juma'a a huta."

Ya kalle ta ya ce, "Ranar juma'a! Har kin yanke lokaci?."

"Eh mana, to me za a jira?."

"an faÉ—a miki haka ake auren ba a bada komai ba?."

"To Baba ai kana da abinda zaka bata É—in, kawai ka je ku yi magana."

Ya yi murmushi bai ce komai ba, dan bai san me zai cewa Safeera ba. Safeera ta ce, "Ni sai na raka ka ma." Ya kalle ta, sai ta miƙe da sauri ta fita tana dariya. 

Ya girgiza kai yana murmushi, zai yi ne kawai dan ya ga suna farin ciki da hakan, kuma danginsa gabaÉ—aya sun bada goyan baya a kai, kuma yana so ya aure ta É—in ko dan ta kula yaransa in ya bar garin.

Baba ya sauke numfashi, ya cigaba da abinda yake yi yana tuna Umma, zuciyarsa tana faÉ—a masa ko tana ina yanzu, ko ta samu kuÉ—in da take nema bai sani ba. Ya É—an sauke numfashi yana tuna kishin Umma, duk da ba matarsa bace a yanzu, in ta ji labarin Atika zata aure sa sai ta yi jinyar kanta. Ya É—an yi murmushi, ya cigaba da abinda yake yi.

         •••••••

Suna zaune zaman meeting na ƙungiya, sun yi shiru ana sauraren abu a cikin wayar. Yadda suka nutsu da kyau zai baka tabbacin abin mai mahimmaci suke ji, dan daga yadda suka ba da hankali su a kai ba za ka san ba ƙaramin abu bane.

Sai da aka gama jin muryar tass, aka juyo ana kallon juna, kowa da abinda yake tunani. Babban cikin su ya kalli Mama, ta É—an tsorata ta ce, "ya ku ke kallona kuma, laifina ne?."

Wanda yake zaune a gefe ya ce, "in ba laifin ki ba laifin waye? Ace yarinya ƙarama har ta samu damar yi miki recording kina yi mata irin wannan maganar? Yanzu ba dan ya zo hannunmu ba ya kenan?."

Mama a kiÉ—ime ta ce, "ban yi tunanin tana da wannan wayon ba, kuma wallahi Islaha ce ta saka ta."

"Komai ki ce Islaha, komai Islaha. Ita wacece da baza a ɗauki mataki a kanta ba? Haka zamu zuba ido ta ɓata mana gari?."

Mama ta kalle sa ta ce, "babu yadda ban yi ba, har sace ta na saka a yi, amma yarinyar nan duk abinda na haÉ—a mata kaucewa take yi."

Ɗaya daga ciki ya ce, "Zainab ce a gabanmu yanzu ba Islaha ba. Me ya kamata a yi? Na tabbatar akwai masu recoding ɗin nan da yawa, ba a san iya adadin mitanen da aka turawa dan su ajjiye ba. Tunda har bincike Islaha take yi baza a bar recording ɗin a wajen mutum ɗaya ba, za su rarraba shi inda ba a yi tunani ba, ko da ya ɓace daga wajen ɗaya, ɗaya yana dashi."

Mama ta ce, "wa zata turawa in ba Islahan ba, ita ce dai kawai. Yarinyar nan har hotunan Hafsa ta É—auka a hotel, ba dan Allah ya kiyaye ba da yanzu muna prison."

"Kina prison dai, wa za a É—aure in ba ke ba? Ke ce uwa a gidan, kuma ke ce ki ke fito mana da yaran nan, ke gwamnati zata kama ba mu ba" ÆŠaya daga ciki shima ya faÉ—a yana kallonta.

Mama ta dafe kai cikin takaici da tashin hankali ta ce, "wai ni Zainab zata yiwa recording, ni zata nemi tonawa asiri?. Na rantse da Allah bazan bar yarinyar nan ba, sai na yi mata abinda nata taɓa tunani ba. Ni zata naɗa a waya? Ni zata wulaƙanta?."

Baban cikinsu ya ce, "kawai ku yanke shawara, me ya kamata ace an yi?."

"A ɓatar da yarinyar kawai, dan zaman ta ba ƙaramin bazarana zai zamar mana ba. Ita kanta ma shaida ce, ko babu wannna muryar shiada ce mai girma. Magana ake ta gidan nan na gwamnati ne, ko ya ya gwamnati ta san da maganar nan ba za a tsaya neman wata hujja mai ƙarfi ba, ko Zainab ɗin ce kaɗai ta ba da shaida shikenan mun gama yawo. Tunda an kasa mallake ta har ta amince da ƙudurin mu, kawai a san yadda za a yi da ita."

Mama sai jikinta ya É—an yi sanyi jin ana zancen za a kashe Zainab, murya a sanyaye ta ce, "a kashe ta kenan?."
Chapter 75 · 0% Book details