← Book details Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 105 OF 133

Sashe 105

Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya É—aga kai ya ce, "a wannan karon bana so a samu matsala."

"an gama ranka ya daÉ—e" ta faÉ—a tana É—aukar handbag É—inta ta fita.

Ya bita da kallo har ta ɓace sannan ya ce, "Meyasa bata so sauran mutanen ƙungiya su san za a kashe Islaha? Me amfanin hakan zai yi mata?."

Babu mai amsa masa sai Maman kawai, kuma ta ce zata faÉ—a masa ba yanzu ba. Ya sauke numfashi yana girgiza kai, dan zai iya aikata komai indai aka ce za a lalata masa kasuwancinsa.

Tofa! Labari ya sake fita, waye ya sake fitar da sirrin Islaha ne? Meyasa ba a so mutanen ƙungiya su san za a kashe Islaha?😱😱

_Don girman Allah ku shiga Youtube ki yi searching littafin KIRAN RABO, ku danna like ku yi comments a kan ko wanne episode.🙏🏻😭_

Nana Haleema.
[7/22, 10:15 AM] KRBBK: RDB2P77
Nana Haleema.

_Don girman Allah ku shiga Youtube ku yi searching littafin KIRAN RABO, ku danna like ku yi comments a kan ko wanne episode.🙏🏻😭_

A hankali Islaha take ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin Saheer kamar babu jini a jikinta. Bata jima a tsaye ba ya buɗe suka haɗa ido, sai ta ɗan ja baya shi kuma ya fito ya jingina da ƙofar yana kallonta.

Ta ɗan kalle sa sai ta ɗauke kai sannan ta ce, "Daman saƙo na kawo maka."

Saheer ya karɓi abinda take miƙa masa yama juyawa a hannunsa ya ce, "na meye?."

Ya buÉ—e yana kallon abubuwan da suke ciki, ya sake kallon ta ya ce, "waye ya ba ki ki kawo min?."

Ta juyo ta kalle shi ta ce, "ni na baka."

"Ke ki ka bani!" Ya maimaita yana kallon ta, sannan ya sake kallon kayan ya ce, "na meye?."

Ta É—an sauke numfashi ta ce, "Tsarabar ka ce na taho da ita daga Jeddah."

Ya zuba mata ido bai ce komai ba, har sai da ta É—ago ta ga ya zuba mata ido yana kallon ta, itama ta zuba masa turo tana turo baki gaba.

Ya miƙa mata kayan da ta ba shi ya ce, "Na gode."

Ta ƙi kallon kayan sai kallon fuskarsa da take yi ta ce, "Ba ka so?."

Ya É—aga kai fuskarsa a É—aure ya ce, "eh bana so."

Har lokacin kallonsa take yi, ta É—an buÉ—e ido waje ta ce, "Kyauta ce fa."

"Kuma na ce bana so."

"Amma meyasa ba ka so? Ni ce fa na baka, kuma itace kyauta ta farko da na fara yi mata, ko dan hakan ya kamata ka karɓa ko da baza ka yi amfani da abubuwan da suke ciki ba."

Ya ajjiye mata a kusa da ita ya ce, "Bazan karɓi abinda ban san da wanne kuɗin da aka siya ba."

Ta buÉ—e baki cikin mamakin kalamansa ta ce, "Hamma....!" Ta faÉ—i sunan cikin yanayi na mamakinsa.

Sai kuma ta nuna kanta da yatsa ta ce, "Zargina ka ke yi Hamma?."

Yadda ta yi maganar sai da zuciyarsa ta karye, dan ko kaɗan ba ya zarginta, kawai yana so ta faɗa masa gaskiyar abinda ya faru kuma ta ƙi. Bai nuna mata ba ya ce, "Ke ce ki ke ƙoƙarin dasa min zargin ki a zuciyata."

"Amma Hamma na faÉ—a maka komai ko?."

"kina tunanin zan yarda da wannan dramar ne?."

"Drama ce Hamma?."

"Drama ce! Bazan yarda da wannan kalaman naki ba, tunda kin zaɓi ki ɓoye min gaskiya shikenan, ki ɗauki tsarabar ki na gode."

Ta yi shiru bata ce komai ba, ya juya zai shiga É—akin sai kuma ya kalle ta ya ga ta zuba masa ido bata ce komai ba, ya daure shige É—aki ta bar ta a wajan.

Islaha a fusace ta bar wajan ba tare da ta ɗauki kayan ba. Haka ta koma ɗaki cikin jin haushi, ko a mafarki bata yi tunanin Hamma zai iya zarginta ba, ta yi tunanin shine mutum na farko da zai fara shaidar halayyarta, sai ga shi shine yake yi mata mummanan zargi akan abinda ta faɗa masa gaskiya a kai. Bata taɓa jin haushinsa kamar ranar ba, bata taɓa jin ya bata haushi kamar a lokacin ba. Ta zauna a gefen gado tana tuna abinda ya ce mata, tana jin zafi sosai.

Haka ta kwana tana fushi dashi, ko da ta tashi da safe bata neme sa ba. Tana fitowa suka haÉ—u da Mama, ta gaishe ta bata amsa ba ta wuce, itama bata damu ba ta shiga wajan Baffa suka gaisa sannan ta fita daga gidan.

Baffa ya shirya ya fito da niyar tafiya wajan aiki ya haɗu da Alhaji Rufa'i a ƙofar gidan a tsaye. Baffa da mamaki yake kallonsa ya ce, "Alhaji Rufa'i."

Alhaji Rufa'i ya juyo da fara'a suka gaisa, Baffa ya ce, "Wani ka ke nema na ganka a tsaye a nan?."

Alhaji Rufa'i ya ce, "Kai nake nema, ina ta tunanin yadda zan same ka sai gaka ka fito."

Baffa da mamaki ya ce, "ni kuma?."

"Kai fa."

"Allah ya sa Lafiya."

"lafiya lau wallahi. Alkhairi ne yake tafe dani. Magana ce mai girma a bakina, kuma itace ta kawo ni gare ka."

Baffa mamaki ya sake mamaye masa zuciya, amma bai nuna ba ya ce, "To mu shiga daga ciki?."

Alhaji Rufa'i ya ce, "Ma sha Allah." Baffa ya yi masa iso har cikin falonsa.

Baffa ya ce, "Bara na saka a kawo maka ruwa daga cikin gida." Alhaji Rufa'i ya ce, "ba sai ka wahala ba, kar ka damu, na gode sosai."

Baffa ya zauna ya ce, "Babu komai. Abin farin ciki ne a gare ni ace yau ka zo gidana tafe da alkhairi."

Alhaji Rufa'i ya yi murmushi ya ce, "Gaskiya dai lamari ne mai girma ya kawo ni, alkhairi ne babba, wanda in ya kasance ba kai kaÉ—ai ba, duk dangin ka zasu san Allah ya saka maka albarka a rayuwar ka."

Baffa ya girgiza kai yana nazarin wannan wanne irin alkhairi ne haka, amma bai ce komai b sai murmushi da ya yi ya ce, "ma sha Allah!."

"Ban taɓa ganun wanda aka yiwa dashen ƙoda ya warke kamar ka ba, ni duk waɗanda na sani in aka yi dashen basa tashi, sai ka ga sanadin tafiya kenan, Amma kai gaka kamar ma baka yi ba."

Baffa ya yi murmushi ya ce, "haka mutane da yawa suke faɗa, ni kaina ban taɓa gani ba sai a kaina. Dan nima na yi tunanin lokacin ya zo, ban yi tunanin zan kawo haka da rai ba."

"Ma sha Allah, Allah ya ƙare mu da lafiya."

"Amin ya Allah."

"Na barka kana ta tunanin dalilin zuwana ko?" Ya faÉ— yana murmushi.

Baffa ya ce, "Gaskiya dai, ka barni cikin tunanin wanne irin abu ne haka?."

Ya yi murmushi ya ce, "Batu ne akan ƴar gidan nan da ka ke riƙo, Islaha."

Baffa ya girgiza kai ya ce, "Allah ya sa lafiya."

"Lafiya lau. Alhaji AbdulAziz Yola, shine ya yi min magana akan yana nemawa É—ansa aurenta."

Baffa ya buɗe ido yana riƙe haɓa jin maganar kamar a mafarki, ya girgiza kai ya ce, "Alhaji AbdulAziz dai na mu?."

Alhaji Rufa'i ya ɗaga kai alamun tabbatarwa ya ce, "shi fa, AbdulAziz Yola dai da ka sani, a kansa nake magana. Ya faɗa min ya yi bincike akanta kuma ya yaba da komai na ta, wannan dalilin ne ya saka yake yiwa ɗansa ƙwaɗayin aurenta. Shine da kansa ya taso ni, ya ce na zo na same ka na ji, in ba a yi mata miji ba auren bazai wuce nan sati biyu ba. Akwai bikin ƴarsa da za a yi, yarinyar zata auri ɗan Yayansa, yana so a haɗa lokaci ɗaya ayi."

Baffa ya girgiza kai cikin mamakin gingimemen abun da ya tunkarosu, sai maimaita sunan AbdulAziz Yola yake yi a ransa, yana maimaita sunan Islaha yana girgiza kai cikin mamaki mai yawa.

Baffa ya ce, "Alhaji Rufa'i ni na rasa abinda zan ce. Alhaji AbdulAziz da kansa shine ya ga Islaha ya yaba da ita, har ya yiwa ɗansa ƙwaɗayin auren ta?."

Ya yi murmushi ya ce, "Yarinyar ta taimaki mahaifiyarsa ne, ta taimake ta a lokacin da ba kowa ne zai taimake ta ba. Tun daga nan suka yaba da ita, kuma da ya bincika É—abi'unta sai ya ga halayenta da komai ya yi masa. Shiyasa yake yiwa É—ansa sha'awar aurenta."

Baffa ya yi murmushi, wani daÉ—i ya mamaye masa zuciya, yana ji kamar Allah ya kawo masa mafita lamarinsa, ya na ji kamar Allah ne ya aiko da haske dan ya haska duhun da ya mamaye shi gabaÉ—aya.

Baffa ya gyara zama yana murmushi ya ce, "Islaha dai ba a yi mata miji ba, da dai ɗan wajena Saheer zai aure ta, amma mahaifiyarsa ta nuna bata so, ta ce akwai wacce ta zaɓa masa ita zai aura, to maganar Saheer ta wuce, dan ya haƙura ma tuni. Ba a yiwa Islaha miji ba, za a iya shiga neman auren ta."

Alhaji Rufa'i ya yi murmushi ya ce, "Amma na ji daɗi sosai, dan ni kaina na yaba da halayen Islaha sosai, shiyasa yana faɗa min na ce bazan yi ƙasa a guiwa ba, sai na zo da kaina mun yi magana."

Baffa ya yi murmushi ya ce, "Gaskiya dai Islaha ba daga nan ba, ba dan ta kasance tawa nake yabonta ba, amma wani lokacin ina ji ina ma ni ne na haifi Islaha."

Alhaji Rufa'i ya ce, "dan ka yabe ta ai baka yi laifi ba, baka ji ance yabon gwani ya zama dole ba?."

Suka yi murmushi a tare Alhaji Rufa'i ya ce, "Zan sanar da kai saƙonsa, sannan za a turo yaro dan su daidaita kansu. Za ka iya bincike akan ahlin gidan gabaɗaya, dan a tabbatar da ingancin auren. In Allah ya sa sun daidaita dashi shikenan, in kuma ta ce bata so babu lallai babu dole."
Chapter 105 · 0% Book details