← Book details Hatsabibiya Ramlat Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 88 OF 152

Sashe 88

Hatsabibiya Ramlat Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

tayi serving d'insa ta zauna kusansa ta dauki Spoon ta fara bashi abaki yanaci hadin dafafiyar shmkafa soyayiya wace ake had at a da nikeken nama asoye sunji kayan lambu kamshin ya hade gun " my zumana ke kika kirka ko murmushi tayi tana bashi yanaci shima yana bata abaki " my sojana gwada musu nayi yada zasuyi lokacin babyna na hannuna bazan ajiyeta ba murmushi yayi " kinaji da babyki my zumana suna hirasu cikin so da kaunar junansu har suka kusar da junansu ta kalleshi " my sojana Allah yabani abinda zan sakamuku kaida my dear murmushi yayi ya Dora dan yatsarsa abakinsa baki ta turo

" ni sai nagode muku mikewa yayi ya kamata ta Mike yaja hannuta suka shiga dakin jawa tanacin abinci Ramlat ta janye hannuta ta zauna kusan jawa baby na shan nono tasaka hannu zata dauketa tace "bakiga nono takeshba Abdallah ya zauna kusan jawa " yauwa my jawana kinyi yada nakeso kar kibamun yarinya da yunwa dariya tayi " to naji my love sannu da zuwa ya gajiya " tabi lafiya dariya Ramlat tayi yayana wata lafiya kuma Ido ya kashe mata " lafiya jikinsa mana shiru jawa tayi taci gaba da cin abincinta har ta gama taba soja baby taje ta wanko hannuta ta zauna kusan Ramlat " my love ya jikinki da sauki ko kanta ta Dora kafadar jawa " naji sauki dear

Mikewa Ramlat tayi " yayana bani babyna muje parlo bata yayi ta amsheta ta fita can parlour tayi zamanta ta kirawo su Ancim suna hira Ramlat tana fita jawa ta rumgume soja ta shige jikinsa matseta yyai jikinsa " my jawana nayi missing dinki ya fada yana shafa bayanta " my love Nima nayi missing dinka danma kana debemin kewa ta waya fuskarta ya kamo ya hade bakinsu yana kissing dinta sosai ta biyemasa suna tsotsar bakinsu kusan mitina biyu ya cire bakinsa yana murmushi " mmn Ramlat bakida dama baki ta turo

ta rumgumeshi " my love an kawomun material din na zaba " OK yayi bari zan baki zuwa gobe " tnx my love ina sonka da halinka mai kyau " wlh jawana nima ina sonki da halinki mai kyau mmn babyna hannuwata suka biyu tura cikin rigarsa tana shashafarsa takai bakinta cikin kunnesa tana masa rada murmushi yayi" my love yanzu ba'asaka sunan Suhailat dinba idan yaso daga baya Allah in ya kawo sai asaka na my dear janyeta yayi daga jikinsa ya kamo fuskarsa ya kora mata idanu fuskarsa daure tamkar bashi bane yake murmushi yanzu kallo daya ta masa hantar cikinta ta Kada ta sada kanta " jawa kina nufin bakya son sunan Ramlat da na sakama diyata maganar har ta zagaye dangi kowa na murna ita kanta afarin ciki take yanzu sai nabi dangi nace nafasa saka sunanta acemun wa ya hanani kina nufin bakyason sunan Ramlat gudan jininki da nasaka ma yata ya fada cikin daga murya idanusa soyi ja tsoronsa ya kamata duba da sauyawarsa lokaci daya rumgumesa tayi ta Saki kuka tana shafa bayansa " haba my love ya zakamun wanan fassara idan da mai son sunan bayanane nafika son sunan wallahi na gwada Kane dan naji me zakace da kace zaka sake sunan fushi zanyi dama fa inada niyyar nacema asaka sunan my lovelyna kayi hakuri wlh wasane ba da gaske nakeba ni kuje Kurike ma

yar na Baku nabata ita duniya da lahira ai batada uwar da tafita ko baga kamarta bace sak ta dauko ina sin Ramlat sosai nafika sonta taya zanki sunanta rumgumeta yayi yana murmushi ya fara sakar mata kiss ta ko ina yana shafarta bakinsa ya kai kunneta " my jawana I love u mmn little Ramlat" I love u too my love Abban Ramlat dariya sukayi atare ya janyeta jikinsa " natafi parlo zanyi aiki kadan " to agama lafiya murmushi yayi ya fice ta bishi da harara tana tsaki " wlh naji natsani babynan aikin banza kawai kana hakuri da Kara sai ankaika bango jiwani yanda kamaninsa suka cansa nace banason sunan yar gwal ai munafurcine itace zata sakaka kasaka sunanta kuma wlh nafasa gwada mata ankon kwanci tayi tana kuka haka kwai nayi wahala na haifo yata amma arika nunamun iko

da ita saboda baa kaunata wlh Ramlat kinci darajar ina tsoran soja saboda bashida kyau da sai na azabtar dake kamar yada kike azabtar dani agun soja, amma yanzu ma wlh sai kin gane kuranki wlh da nasan hakane tun farko bazan yada Abdallah aureta ba ni nafara gajiya yo da nace eh banason suna komeye nufinsa fasawa zaiyi ko dukana zaiyi itako harda kukan munafurci wai nama Abdallah godiya yasa sunanta lokacin da kuka kulla kitumurmuraku ina ina ko lokacin da kike matseshi adaki har yaji yanason sa sunanki ina ina tsaki taja ta mike ta shiga bathroom,

Ramlat suna zaune da su Ancim suna kallo tana rumgume da babynta Ancim ta gaisheshi ya amsa ta Mike ta nufi bangaransu kusan Ramlat ya zauna " mmn baby kawota je dauko min Laptop bashi baby tayi taje ta dauko masa ta isko baby ta fara kuka shagwabewa tayi " haba yayana kuma bazaka bata hakuri ba " my angel kin dai gani ina jijigata ta kiya so take ta nuna ke tasani dariya tayi ta amsheta tana zizigata lips dinta na kasa ta bata ta amsa tana tsotsa tayi shiru " lallai kunada aiki je ta saka kiyi katon labba ba ruwana banza ta masa saida taji yana mata zugi ta cire aikuwa ta fashe da kuka " ai saiki maida mata wlh kinga yada sukayi ja baki ta turo ta Mike ta nufi dakin jawa suna zaune da umma suna hira " my dear wlh yunwa takeji duk ta tsotsemun lips sai zafi sukemun Saudat tayi dariya " ai yarnan taku akwai Saurin jin yuwan.

kema, haka kikayi jawa ko kala bata ceba ta amshi baby da haushi haushi ta dungura mata nono ta fara sha zama Ramlat tayi ta kwanta jikin umma Saudat " Allah ummata haka nayi" wlh haka, kikayi tsotsa, " gaskiya babyna ki ragawa my dear karki tsotsemun ita jawa ko cikinki bata ceba taci gaba da ba yarta nono Ramlat suna hirasu da umma baby na koshi jawa ta kwantar da ita tayi bacci itama ta kwanta Ramlat ta juyo " my dear bacci zakiyi " eh my love kuyi hiraku da umma dariya tayi " to munji hirasu sukaci gaba dayi sai karfe goma tayiwa umma sallama ta fito soja yana aiki a Laptop jikinsa ta zauna,

my sojana " ni baruwana dake kika tafi gun el uwarki kika bari kanta ta dora kirjinsa " sorry yayana wlh kana raini kanta ya shafa " na hakura tana jikinsa akwance tana bashi labarin wakar da ta kalla a tashar Arewa 24 ta mdm na Niger yana dariya " ai zamuje insha Allah " yauwa yayana hira sukaci gaba dayi har ya gama abun da yake ya kashe Laptop din " my zumata muje mu kwanta kai ta daga masa tashi tayi daga jikinsa ya dauki Laptop d'insa ta kashe kayan kallon suka tafi dakinsa suka shiga ya rage kayan jikinsa " babyna zo kiji gabansa ta tsaya tana kallonsa kamota yayi yamata rada akunneta dariya tayi ta janye jikinta ta fice bathroom ya shiga yayi wanka ya fito ya goge jikinsa ya shafa mai mai kamshi da taushi yasaka wando iya cinya ko Riga bai sakaba ya fasa turare yana tsaye gaban mirror yana taje kwantacciyar sumar kansa ta shigo,

da gudu ta karasa ta rumgumesa ta kwantar da kanta gadon bayansa " yayana kana burgeni wlh ina masifar sonka murmushi yayi ya juyo da ita gabansa " nima ina masifar sonki my habibtyna dariya tayi ta makalkaleshi daukarta yayi ya kwantar da ita saman bed yabi bayanta ya mata rumfa da Faffadan kirjinsa hannuta tasa tana shafa gajin kirjinsa kallonta yayi itama shi take kallo " my Ramlana "Yayana rumgume juna sukayi suna sabke ajiyar zuciya atare sun jima ahaka batare da sun iya maganaba kwancinsa ya gyara ya dauketa ya dorata saman kirjinsa ya gyara mata kwanciyarta ya kamo fuskarta " my zumana muyi baccinmu yau bana miki komai kwanciyarta ta gyara ta lumshe idanuta " thanks my sojana " shiru babyna yi bacci abinki bayanta ya shiga shafa mata yana mata susar kadangare tin tanajinsa har bacci ya dauketa sabkar Numfashinta yaji ya duba yaga tayi bacci Addu'a ya mata ya shafa mata shima yayi ya gyara mata kwancinta saman kirjinsa yaja blanket ya rufesu, Asuba yagari

****************************************

*Bayan kwana hudu*

cikin kwana hudan da ya wuce kullum gidan cike yake da jama'a yan barka da yan uwa Abdallah yau kwanashi biyu a Kaduna amma yau yake dawowo yabarma yayansa Naseer da sauran duk abin da zaayi cikin tsari kafin ya Iso yau, kulluma jawa cikin baki take dangi Abbanta da nasu momy ganin baby shiyasa har yanzu Ramlat ta kasa gano jawa irin sharetan da take ko idan tayi magana taki saka baki tinda basu cika zama su biyu ba a yanzu idan zasu shekara zaune idan ba itace ta mata maganaba to ko kallonta bazatayi ba sai ta danganta hakan da yanayin jego dan talura da baby ma ba wani kulata takeba ko idan zata bata nono tanajan tsaki shine yasa tace wlh idan tana mata tsaki sai ta fadawa yayata batason bata nono yanzu ya tsare ta ta bata agabanshi gidan yau masha Allah cike yake da yan uwa da abokan arziki takama gobe sunah sai kayan sunah ake gyarawa

Jawa tasha kitso da konshi tayi kyau sosai abinka da fara mace sai haskawa take Ramlat ma an mata konshi mai masifar kyau amma batayi kitso tsefe kanta tayi gyrashi ta daureshi har gadon bayanta tsaye take gaban mirror tana daurin dan kwali wayarta tayi ringing ta dauka tayi picking ta kara akunne,,
Chapter 88 · 0% Book details