← Book details Hatsabibiya Ramlat Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 147 OF 152

Sashe 147

Hatsabibiya Ramlat Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

Family yau suna cikin tashin hankali su shaffah sun farfado itada safna mai ran karfe yace a basu gawar jawahir akaita gidanta ayi mata wanka a sallah ceta Soja baya magana da idanu kawai yake binsu Addu'a kawai yake jikinsa na kerrrma jameela ce da hadeeza suka Iso da yaran Ramlat sai kuka suke Yinma tace shaffah da Nabeela su shayar dasu haka ko akayi suka shayar dasu Soja ya kalli little Ramlat ahannu yinma sai wasanta take tana tsotsar yatsarta kawai sai ya fashe da kaku ya Mike ya nufi gun yinma ya amsheta ya rungumeta sai lokacin Aunty maimunatu ta fashe da kuka tin karfinta Anty Rahma ma kuka takeyi ta rungume maimunatu duka asibitin hargitsewa tayi da koke koke saida su Abbie suka tsawatar musu gaba daya suka tisasu gaba sukabar asibitin Naseer da Sulaiman kansu kuka suke wiwi ga Ramlat ance tayi doguwar suma wallahi yau idan kaga wannan Family duk Rashin imaninka sai kayi musu kuka Dada bata iya cewa uhumm bare uhumm uhumm Addu'a kawai take da godiyar Allah dan shine yaso ganinsu awanan hali haka su Abbie suka tusasu amotoci aka nufi gidan Soja wanda jama'ar duk ta watse sai abinda ba'a rasaba Wanda labari yazo musu sai rizgar kuka akeyi su Abbie na kawosu suka koma daukar gawa Habeeb da Sadeeq yinma tayi kira dan har yanzu suna nan su suka kama Soja dan tasan zaifi sauki Saki akan yan uwansa yana rike da yarsa ai sojoji naji abinda ya faru matar Oga ta rash suka shiga kwashe kayan da aka jera da Wanda za'ayi rabo akasa sallami sauran jama'a can cikima Ana ta gyaran ko ina su Ancim sai kuka sukeyi kamar ransu zai fita su Abbie suna komawa Dr yace suyi hakuri ko basuji sallah magrib akeyiba Dole gawa sai gobe da safe wlh sai lokacin suka tuna dan su kansu arudu suke suna danne tasu damuwarne dan su taushi iyalinsu Dole suka bari sai da safe sukaje suka yi sallah suka koma gidan soja wanda abun ba'acewa komai sai godiyar Allah yanzu duk

Sun nutsu bayan sunyi sallah kowa Addu'a yakeyi Soja tinda yayi sallah yake tama jawahir Addu'a da Ramlat Allah ya tasheta inko itama babu ita to Allah ya jikinta ya fashe da kuka gabaki dayan jama'ar masallacin kansa sukayo suna bashi hakuri dan sunada labarin komai Naseer ya rungumeshi yana bashi bakin da jadadda mashi yayi tawakali da Allah yayi ta maimaita Addu'a ahakade har akayi sallah isha suka dawo ciki parlon dam da mutane yan gidansu jikin yinma yaje ya kwanta saman cinyarta

Kanshi ta shafa muryasa na rawa yace" yinma ki rungumeni ki lallasheni banida kowa yanzu matana biyu yau Allah yayi hukuncinsa akansu yinmata ki rarasheni duk kuka suka fara yan parlon cikeda tausayinsa idan ka kalli Abdallah bazaka tab'a shine jajirtaccen Soja nanen mai jarumta kan aikiba Wanda bayada kasawa da gajiya idan ya fita fagen dagaba ko idan ya kamo mutum yana masa azaba bazaka tab'a cewa akwai abinda zai sakayi zama haka ba mutuwa ai daban take yau yazama abin tausayi daurewa yinma tayi ta kwantar da little Ramlat ta rungumeshi tana bubbuga bayansa" Abdallah kayi hakuri Addu'arka jawahir take so ba kuka ba Ramlat zata farka da yarda Allah shiru yayi yinma nayi masa nasiyya mai ratsa jiki Akan duk abinda ya samu bawa yayi tawakali da Allah kuma Allah da ya amsheta yafishi sonta Addu'a yayi ta maimaitawa Abakinsa tofah yau gidan Soja cike yake da yan uwa kowa yaki tafiya amma yinma ta kora su jameela da su shaffah da nabeela tace kawai su tafi abinda ya faru ya Rigada ya faru su dawo da safe kawai Dole suka tafi suna kuka amma manyan sunan

yaran Ramlat an rabasu ah Ukku safna daya shaffah daya Nabeena daya ance duk sutafi da su har aga abinda Allah yayi safna ita ba anemi Aminu ba saboda na gidane amma su shaffah saida aka nemi izinin mazajansu har dare ya tsala babu Wanda yakai

Ko da ruwa bakinsa Soja har yanzu na gurinsu yinma sai daket ta lallabashi ta kaishi har d'aki tasa yayi wanka ya dauro Alwalla ya fara Jero salloli to gidan haka ya kwana babu Wanda ya rumtsa Addu'a aka kwana anayi har Asubah Soja masallaci ya tafi ko bayan sallah bai dawoba saida gari yayi haskae lokacin gidansa yacika makil da Al'ummah yan uwa da abokan Arziki sojoji kuwa mota kusan biyar saida Soja yayi mamaki dan bai fadawa, kowaba haka suka taresa suna masa, gaisuwa yana amsawa rumfunan jiya na sunah sune yau na zaman makoki oh duniya ba gidaba zama yayi cikin jama'a masu jiran gawa wlh Duk Wanda ya kalli Soja sai yanashi tausayi su Abbie suka amsu gawa dan Dada tace akawota ayi mata komai agidanta hakako akayi da suka kawo ana aka gyarata su mummy sukayi mata wanka suka suturtata aka gyarata

Aka fito da ita makara a parlo yinma tace akirawo mijinta yayi mata Addu'a Anty maimunatu tace!" wlh tunda Nike dake jawahir baki taba batamunba kuma ko kin batamun na yafe miki ta fashe Da kuka jaleel ma kan gawar ya duqa yana kuka yana Addu'a sai ga Soja ya shigo ya zube ganba gawar bisa gwiwarsa, ya kwantar da kansa saman gawar yana Addu'a yana kuka yajima sosai ya dago " jawahir Ashe haka zakimun Allah sarki meyasa kika kasa, cikamun Alkawalin da mukayi jiya dake jawahir da gaske mutuwa kikayi shikenan kinbarni nida Ramlat babba da Ramlat karama kuma kinsan munada bulatarki wlh jawahir ina masifar sonki ta yaya kika gujemu nida yarki mai bukatarki ayanzu ya fada saman gawar yana wani irin kuka ya rungumeta gama parlon ya rikice da kuka sai Abbie yazo ya banbareshi daga jikin gawar daket su Naseer suka rikeshi sauran jama'a suka yimata Adu'a aka fita domin yimata sallah yinma tace " Naseer jashi maza yaje ya sallahci gawar matarshi baiwar Allah Allah yasa halinki nagari ya biki duk mun yafe miki duniya da lahira mummy kam ita abubuwanne sunyi mata yawa sai gani sukayi ta zube asume akayi kanta Dada tace" Allah muna Mika godiyarmu kan irin wanan jaraba da, kabamu Allah kabamu ikon cinyewa Jawa yarinya mai hakuri da kirki da kawaici baki dayan Zuriarmu mun yafe miki duniya da lahira insha Allahu zaki sami Rahma gun ubangijinki barema mijikinki yace akwai cikinsa ajikinki

Ruwa aka zubawa mummy ta maido numfashi Dada ta rungumeta tana yimata nasiyya dan tasan harda damuwar yarta tun jiya itama tana tsakanin rayuwa da, mutuwa acan harabar gida an sallahci gawar jawahir an tafi kaita gidan gaskiya Wanda fadin Al'ummar da jawahir ta samu bata lokacine saide muce Allah yasa, Aljannace makoma haka aka kai jawahir gidanta na, gaskiya, anbarota daga ita sai halinta Allah yasa, mucika da imani agaskiya jawahir tasamu
Yabo sosai kallo daya zakama soja wlh sai ya baka tausayi kai duk yan gidansuma manyan suna daurewane kawai har yamma soja yakici yaki sha sai wanan dare da mutane suka rage yinma tasa aka kirawoshi da kanta ta hada masa tea mai kaurin gaske dan tasan ba abunci zai ciba ita tayi ta bashi abaki har ya shanye ya kalleta" yinma ina mareniyar Allah " Abdallah kayi hakuri tana cikin koshi lafiya tayi bacci zan kula da ita Allah ya temakemu bata kuka hawayen fuskarshi ya share " to marayun jaririn fah " Soja bansanka da sarauba ka kasance mai tawakali ka jure suna lafiya kannuka ke shayar dasu shiru yayi baisake maganaba

Ramlat ko har yanzu bata farkoba ta kwana ta wuni amma tana samun kulawa sosai hankalin yan gidansu atashe yake amma da Dr yayi masu bayanin komai sun gamsu zata iya farkawa akoda yaushe sun dan ji dama Addu'a suka kama suna mai godiyar Allah akan jarabawar da ya dora musu soja ya mikawa Allah lamarinsa yinma na kula dashi sosai tare da, kara tunatar dashi babu fah mai fushi da hukuncin Allah don duk abinda yayi to fah yana da dalili idan ko bawa bai amshi kaddara ba to zai karomaka jarabawar da tafi ta farkon yaga yada zakayi haka de take sakasa GABA da nasiyya yanajin dadin kasan cewa da yinma uwa ta gari haka akaci GABA da amsar gaisuwa kullum gidan cike yake da Al'ummah daban daban rundunar sojoji ba'a magana da manyansu da yaransu

****************************************
*Bayan kwana hudu*

Jiya akayi sadakar uku Wanda tunda akayi mutuwar Family d'insu agidan suke sai jiyane Abbie ya matsa duk suka koma gida da kwana amma yinma da mamah da mummy da Dada sunan yaran Ramlat suna cikin koshin lafiya little Ramlat ma tana lfy Soja ya Mika lamuransa ga Allah duk ya zama shiru dashi kullum cikin yima jawa Adu'a yakeyi ya dauki nasiyya da yinma tayi masa yana Adu'a Allah ya tashi Ramlat kullum su habeeb da Sadeeq na tare dashi suna kwantar masa da hankali yanzu tashin hankalinsu dayane Ramlat dan gani sukeyi kamar itama mutuwa tayi kawai sunki fitowa ne su fadi musu shiyasa Abubakar mutuwar jawa ta girgizashi sosai yana Lagos Abbie ya kirasa ya fada masa ya biyu jirgi yazo wlh yayi kuka sosai tinba yada yaji Ramlat tayi doguwar suka yara ukku jarirai abin tausayi babu uwarsu ga little Ramlat ga Soja duk ya Saki kamar ba soja mai kuzari ba da kazar kazar
Chapter 147 · 0% Book details