← Book details Hatsabibiya Ramlat Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 100 OF 152

Sashe 100

Hatsabibiya Ramlat Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 7 min read

har fa zanyi bacci " oh my baby bakiji murya sojanki ba zakiyi bacci shagwabe masa tayi" to ba kai bane ka manta dani " Ashe kuwa da na manta da kaina kinci abinci ko " naci yayana yaushe zaka dawo " kiyi hakuri zan dawo my bugun zuciyata " to nayi yayana banajin dadin bacci idan ba saman k'irjinkaba murmushi yayi " wlh nima haka hakuri nake dan yazama dolene kukan sangarta ta fara masa tana k'iran sunansa "yayana Abdallah " baby kiyi hakuri mana ku sokike ki tayar mun da hankali nakasa ciki abinda ya kawoni lallabata yayi tayi da kalamai masu dadi har tayi shiru yashiga bata labarai masu dadi tana dariya daga karshe yayi ta gaya mata tsadadun kalamai na soyayya yana sakar mata kiss ta waya har ta fara jin bacci har ya dauketa wayar ta fadi can gefe murmushi yayi yanajin sabkar numfashinta " rigimamiya kawai idan kinsa ina garin Abuja tin jiya da kin sakani tashin hankali dan bazan iya jure ganinki adamuwaba sorry babyna idan zanyi wata général Garba bai shigo hannumu ba to bazaku ganiba katse Kiran yayi, ya kira wata number bugo daya aka " captain inaso yanzu kaje mambila ka gabatar da abubuwan da nasaka " ok an gama amma fa dare ya tsala sosai " ina ruwanka da dare kaje kawai" OK insha Allah katse Kiran yayi yaci gaba da aikinsa sai karfe biyu yayi shirin kwanciya

****************************************

Washe gari tin Asubahi aka radawa dan gidan Naseer suna Abdullahi saboda Naseer nason halin kanasa kowa a Family yayi farin ciki saboda wanan ya nuna kaunar junan ga yan uwan Abdallah da yinma ta kirasa ta gaya masa yayi murna sosai Ramlat tinda taji labari gurin su Shaffah a gagauce tayi wanka ta shirya ta tafi part dau Naseer ta rumgume Abdallah ta hana kiwa daukarsa sai ita suna mata tsiya tayi banza dasu Nabeela tace" wlh kin fiye son miji ai muma muna farin ciki tinda sunah yayamune " kanku akeji ni ai biyu nahada mai wuyaa salu yayana kuma miji kuma kamarmu daya tamkar tagwaye dariya jameela tayi" da kyau Nabeela kinja gori sai kiyi shiru shaffah tace " ai shiyasa na iyawa bakina " aikuwa kin huta da gori masha Allah gidan haka yacika fal da mutane dan dangin Nuratu ma ba bayaba ainyi suna cikin kwanciyarya hankali taro yayi kyau anci ansha babu laifi Ramlat tayi ta k'iran soja wayarsa akashe ta hakura duk tashiga damuwa wuni guda basu wayaba tin Kiran Asuba da ya mata

Da marece bayan la'asar yinma ta lallabata tace ta koma gidanta ta shirya badan tasoba tayi sallama da yinma take part dinsu tama mummy sallama ta hada mata irin abubuwan da take anfani dasu take part din Dada da su safna tafito tashiga motarta sai turo baki take ta tafi cikin nutsuwa take driving direct gidansu Jawa ta nufa zuciyarta fal tunanin sojanta ko lafiya wayarsa akashe tana zuwa akofar gidan tayi parking ta fito ta rufe mota ta tura get shiga suka gaisa da mai gadi ta wuce ciki da sallama tashigo parlo Jawa na zaune tana shayar da baby ta shigo " my love namiki fushi tinda soja yayi tafiya shikenan kika dane zuwa zama tayi tana murmushi " Afuwa bani babyna ina momy ko bata isoba " tazo sun tafi kasuwa iyada Anty " OK y KK ya ruwan zafi little Ramlat ta bata tana kallonta sai taji kamar taga soja zuciyarta tayi sanyi ta rumgumeta Jawa na lure da ita azuciyata tace " uwar jaraba yanzu haka wuni dayanan da bata samesa a wayane takasa dauré tabiyo taga fuskar babyna " my love yanzu muka gama waya da my love yake cemun kina gida tunjiya gaban Ramlat ya fadi da karfi amma ta dauré tayi murmushi " wlh haka yacemin ya kiraki kunsha hira ai shiyace nazo na ganku dede kofar parlo na kashe K'iran yau duk ya rufe Numbubinsa sai ta sirri Ashe yakiraki da ita Jawa kasa boye bakin cikinta tayi " to me zai hana yakirani kema karama ya kirani bare ni dariya Ramlat tayi " aishine ina su tuwis " suna islamiyya " amma

daga kun karasa wanka zaku dawo gida kai ta daga batayi maganaba saboda tsabar haushi Ashe dagaske ya kirata itace bai kiraba da tasani dama bata kalalo zancenba sun jima suna hira karfin hira Ramlat ce jawa i ko A,A ne kawai tadan jima tayi mata sallama ta rakota har kofar gida tashiga motarta ta tafi tana cike da mamakin jawa dan tasan karya take wayoyin Abdallah akashe suke tayine da ta bata mata rai saide batasan ita ta batawa kanta raiba murmushi tayi taci gaba da driving dinta har ta Iso gidanta honr tayi aka bude mata get ta danno hancin motar gidan rumfar aje motoci ta shiga tayi parking ta bude mata ta fito ta rufe ta nufi ciki sojawan dasuke tsaron gidan suna gaisheta ta amsa ta shige da sallama ta shigo parlo Da gudu Ancim ta fito ta tareta " anti sannu kikayi kwancinki acan murmushi tayi " wlh to y KK ina inna talatu tana kitchen fitowa tayi tama Ramlat sannu da zuwa suka gaisa ta Haye sama dakinta tsaf kamar ba tin jiya bata gidanba cire kayan jikinta tayi ta shiga bathroom tayi wanka ta dauro Alwalla tana fitowa ana gama Kiran sallah magrib tasaka kaya ta tayar da sallah ko da ta gama bata tashiba ta bude al'qura'ani mai girma tana karatu har aka kira sallah isha'i ta tashi tayi da ta gama tajima tana Addu'a Allah yasa duk inda yayanta yake yasa yana cikin k'oshin lafiya ya kuma ganar da yar uwarta sukima kamar da Allah yasa ta gane abinda take ba mekyau bane duk da ta fuce mata arai sam yanzu bata ganinta da kima amma tana rokon Allah yasa ta gyara,

Mikewa tayi ta cire hijab ta sabko kasa ta zauna Kiran soja tayi cikin sa'a wayar tana ringing tana dabda tsinkewa ya daga " my baby " yayana ina ka shiga yau ciwin zuciya ya kusa kamani ta fada tana alamun kuka " my bugun zuciyata, wlh aiki ya sani agaba. kiyi hakuri karkiyimun kuka kinji babyna " to nayi ya fatan kaci abinci kuma kana lafiya" ina lafiya Mrs Abdallah kefa " nima yanzu ina lafiya bara naci abinci " yauwa matar soja kici sosai nima yanzu zanyi wanka naci abinci na kwanta " my sojana ka kwanta ka huta kaji " to my zumana bye " bye ta katse k'iran tana dariya ta kirawo Ancim ta kawo mata abinci taci suka taba hira ta meke dan yau bacci takeji sosai ta Haye saman tasanya kayan bacci tayi kwanciyata bangaran Jawa tun tafiyar Ramlat takejin wani irin bakin ciki na damunta da tsanar Ramlat Kenan da gaske kiranta yayi itace ya kashewa waya bakin ciki bai barta ko abinci taciba ta shige daki ta kira kausar tana dauka tayi mata bayani abinda ya faru hakuri ta bata tace tabari har ta koma tayi duk abubunwan da yasa lokacin da yake saduwa da ita inma shine yakesa tafi sinta zasu gane un kuwa bashibane zasu bulu ta wata hanya sai lokacin ta dan ajiye hankalinta dan tasan aski yazo gaban goshi tana kashe kiran soja ya kirata sukasha hira ta fara masa mita halan yanada wata number sirri ita baya kiranta cikin jin haushi yace" eh inada tunda ni munafukine taya zan kiraki da ita inada bana kiranki ko da abinda zakiyi jin yada ya dauki abun ta karkace" wlh wasane nakemaka my love Allah ya huci zuciyaka cikin dubara ta shawo kansa sukaci gaba da hira sun jima ya mata sallama ya katse K'iran tana cikeda jin haushin Ramlat ta kwanta bacci kusan sha biyun dare lokacin Ramlat ta tsufa da yin bacci..

****************************************

*bayan kwana goma*

Jawa ta zubar da ruwa tace bazata dawoba sai soja yadawo Soja ya sa aka turo da kaya na kece raini da nata da na yarta Abdallah yace ta koma gidan su zauna da yar uwarta yakusa dawowo nuna masa tayi tafi kowa son hakan dama ta damu Ramlat ita daya sai yan aiki tashirya kayanta tsaf ta koma gidan mijinta suna zaune kalau da Ramlat takasa na kasa tanaso soja yadawo ta dandana masa zumarta yaji ko tasamu hanyar hadasu da Ramlat yau kwanata biyar da komawa yanzu har sun cire rai da zuwan soja nan kusa Jawa ko ta matsu ya dawo yada take naso ita daya little Ramlat kace tayi wata biyu ko ukku saboda yada tayi girma yanzu ta aje hankalinta tayi tsaf da ita ga gyaran jiki da tasha maganin mata ya ratsata mai tsari dakyau tasha ba na haukaba sai sheki take hankalinta kwance sanin soja baya gari, Ramlat Abdallah na kwantar mata da hankali karta damu yana hanya tana masa korafi tana yawan jin kasala tace rashin sane akusa tace ta sani Allah ya kawo matashi lafiya
Chapter 100 · 0% Book details