← Book details Hatsabibiya Ramlat Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 84 OF 152

Sashe 84

Hatsabibiya Ramlat Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

" my love tunanin me kike dariya tayi" wlh tunani babyna ina sonta sosai " to ai yarki ce ba tawaba murmushi Anty saudat tayi " kude bako rabo da shirme Ko kunyata ba kwaji,, hirasu sakaci gaba dayi har sukazo gida parlon sai zuba kamshi yake su Ancim sun gyara Ko ina tsaf Ramlat aparlo ta zauna Jawa suna cikin daki Soja baima shigoba yace direba yakaishi bariki sai waya yake yana fadawa abokanan sa da na aiki da babban aboki Habeeb matarshi ta haifo masa baby girl kyakyawa,, Ramlat tana zaune a parlo baby ta fara kuka tana jijigata ta Mike " muje kisha mama idan bazata bakiba mama ba ni nabaki kisha abinki wlh bazan yada abarmun yata da yunwa ba.... ✍🏻

Rahma ce ummu Fareesa😘

✍🏻✍🏻✍🏻

*This is the beginning of the part 2*

*🤷🏻‍♀HATSABIBIYA🤷🏻‍♀*
*💖💖RAMLAT💖💖*

*_🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION_*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

Story & Written by
✍🏻
Real Ladingo😉
yar mutan Niger🇳🇪

*👏🏻👏🏻👏🏻DON GIRMAN ALLAH KARKUMANTA DA GIRMAN ALKAWARI DA AMANA KARKU FITARMUN DA BOOK WAJE KUKARANTA KYAUTA RUWAN ALLAH AMMA ARIKE AMANA👏🏻👏🏻👏🏻*

*Bismillahir Rahamanir Raheem*

*Book 2* 🅿👉🏻1⃣&2⃣

...lokacin da tashiga dakin jawa tana cikin bathroom zama tayi har ta fito baki ta turo " zo ki bata mama yunwa takeji murmushi tayi " kikaki bata " wlh dan babu ruwa da yaushe zamu jiraki zama jawa tayi kusan Ramlat ta amshi baby ta janye rigarta ta fara shayar da baby Ramlat kallon jawa take yada take cije baki " my dear akwai zafine " me kika gani " naga kina cije bakine " cikina yake dan murdawa amma

da sauki " ayya sannu to baby bari naje na dawo" my love tsaya tasha ku tafi please sonake nayi bacci na huta dariya Ramlat tayi " wlh bazaama yata shayarwar ha'inciba barmun ita tasha ta koshi kafin na dawo murmushi jawa tayi " to shikenan je ki dawo sai na kwanta " yauwa my dear Thanks tafiya tayi sama ta haura dakin soja ta bude ta shiga komai tsaf tin gyaran jiya da safe da tayi bedroom tashiga ta fada saman bed dinsa tayi kwanciyata ta rumgume katon pillow mai fitar da kamshin soja saboda agajiye ga bacci da takeji wayarta ta aje kusanta bata jimaba da kwanci tayi bacci can kasa, dakin jawa mutane sun fara ciki dakin yan zauwa ganin baby harda su anty jaleema da hadeeza da su zakiyyah hadeeza tace

" ina mamar baby jawa" tace ta tafi ta dawo maybe fa tayi bacci dariya sukayi uwar yan rigima Saudat tace" wai bani da rigimaba amma dotana tayi hankali yanzu jawa mikewa tayi ta dauki wayarta ta fito dakin soja ta nufa a parlon sa ta kwanta ta kirasa buga biyu ya daga" my jawana ykk ya jikinki nakira baki dagaba murmushi tayi" Abban Suhailat ina lapia lokacin ina bathroom Allah yau kewarka nake murmushi yayi ok to yanzu ya kikeso ayi kinsanfa yanzu gidanmu yazama na kowa " my love wanan katon gidan wama zaisan kananan please dadyn Suhailat kazo mana " my jawa ina cikin wata haraka ne bari da nagama zanzo ki shafamun kan babyna amma jawa wacece Suhailat " babyna mana " yaushe aka goge sunan da na bayar a hospital Ko ban Fada miki nasa sunan Ramlat ba idanu ta zaro " wai da dagaske kake? " ina wasa da Kene ai dama na fada miki idan

kinga ansaka sunan suhailat to twins kika haifa daya Ramlat daya suhailat yanzu ina babyna " tayi bacci yanzu nagama shayar da ita ok zan ganki bari na dawo da kinga kirana to ina bangarena kizo namiki tausar gajiya kinyi kokari masha Allah baby katuwa haka baki karuba shiru tayi my jawa bakya jina " nace to sai ka dawo ina jiranka ta tsinke K'iran tana juya wayar a hannuta tsaki tayi ya mike ta fito dakinta ta koma

sukaci gaba da hirasu Ramlat tayi dai daya tana sharara baccin wayarta ta dauki kuka sai ana uku taji cikin bacci idanuta ta bude a hankali ta meka hannu ta janyo wayar tayi picking ta kara akunne" yayana bacci " sorry my zumatyna kin gaji ko" my sojana gani a dakin ka ina kwance ina shakar kamshinka " wow zumatyna kiyi baccinki anjima zan kiraki kiss ya sakar mata bye my kanwata"bye my jinin jikina please karkayi dare " bazanyi ba ina babynki " tana gun my dear na bata aro kafin na tashi abacci dariya yayi ya tsinke k'iran wayar ta aje tana shigewa cikin blanket ta rufa tana lumshewa baccinta ta koma sai bayan sallah azuhur ta farka tayi wanka tayi sallah

ta gyara masa shimfidar gadonsa ta feshe dakin da turaruka masu kamshi ta rufo kofar bedroom ta rufo tafito parlo kofar parlon ta rufe ta nufi dakinta ta canza kaya ta sabko kasa lokacin karfe uku ta kusa tana shiga dakin jawa su hadeeza zasu tafi " lah yaushe kukazo shine Ko nemana baku yiba " ai munsa kina bacci shiyasa ya gajiya gun baby ta nufa ta daukota adonta mai masifar kyau da tsada ta rumgumeta " Anty jameela kinga babyna Ko " nagani ku tabiyu ai Dole taci sunanki dariya Ramlat tayi " A'A suna mai dadi zamu samata na zamani ko my dear ta kalli jawa kafada ta daga irin oho "duk yada kukayi duk daya dariya sukayi zakiyyah

tace" wlh sunanki yayamu yasa fa " ni bawani nan tsokana fitowa sukayi sukama Saudat sallama suka tafi Ramlat tayi zaune tana rumgume da baby sai lasar harshe take " ummana kalli babyna lasar harshe take "yarku tayi kwadai saudat ta Mike ta tafi tawa jawa wanka Ramlat na zaune da baby har akayi Kiran sallah la'asar ta Mike tashiga dakin jawa tafito daga wanka Kenan tanasa kaya" my dear amsata naje nayi sallah bata juyoba tace" ajeta inda kika dauketa baki ta turo "Allah nono takeso fa kalli tana lasar baki banza tamata tagaji da jira ta amsheta bata juyoba " Allah ni natafi da abuta muyi sallah tare ta fice tana dariya

Sama ta haura da baby yanzuma dakin Abdallah ta shiga ta kwantar da ita saman gado setin da zata rika ganin babyn ta tayar da sallah dama da alwallata tana gamawa bata tsaya doguwar adu'aba ta tashi gadon ta hayo ta kwanta kusan baby sai kallonta take " babyna ina miki son so Allah ya barni dake naga auranki yatsotsin hannuta ta kamo komai irin nasu da Abdallah ta dauko babyna babu ruwanki da rigima ko uwar kwadai yatsar me kikesha wayarta ta dauka tayi ta mata pic iri iri misalin karfe biyar soja ya shigo gidansa dakin ya shiga ya kira jawa bata jimaba sai gata tazo yana zaune a parlo hannu ya bata ta kama ya dorata acinyarsa " my jawa

Sannu ya kafin jiki " Alhmdllh tayi shiru fuskarta ya kamo yana kallonta " my jawana ya naga kamar ranki abace murmushi tayi ta shafi fuskarshi " haba my love yau ranar farin ciki me zai sani bacin rai rumgumeta yayi yana danna mata jikinta dariya tayi " my love wlh bana ciwon jiki " ina babyna saida tayi jimm tace" tana gun mamarta me sunanta ko " muga ya babyna tana koshi da kananu mama bude rigar yayi yana shafawa yanzu babu zafi idan tanasha ko narke masa tayi ajiki " babu zafi my love " OK bari muga ruwan anesa ko a kusa baki yasa yana lasarsu lumshe idanu tayi tana shafa wuyansa " my love karka tsotso akwai ruwa fa saida yayi minti daya ya cire bakinsa yana murmushi ya kalleta " to sai me ai sai na zubar ko dariya tayi ta rumgumeshi " my love

Allah yabarmun kai " Amin kafin lokaci yayi tashi tayi daga jikinsa " wlh ka tadomun ruwan nono natafi neman yata " ki gaishesu ficewa tayi tana dariya mikewa yayi ya shiga bathroom yayi wanka ya shirya cikin kananun kaya ya fito babban parlo ba kowa sama ya haura yaga kofar dakinsa abude ya shiga babu kowa a parlo bedroom d'insa ya shiga tana kwance rumgume da baby ahanka ya karaso bakin gadon ya hayo ya kwanta bayanta ya rumgumota ihu tasa aikuwa baby ta fashe da kuka baki ta turo " haba my sojana sai, kabamu tsoro baby ta dauka. Tana jijigata
hakuri abar kaunata

Kara sautin kukan tayi ta harari soja tayi narai narai da idanu " sorry ni karkimun kuka tashi ki kaita mamarta mikewa tayi ta fice tana zizigata aparlonta ta same tana zaune tanacin abinci " my dear kinga yayana ne ya tsoratamu shine take kuka batace mata kalaba hannu ta bata ta amshi yar ta janye riga ta kafa mata nono a baki tana tsotsa kusanta ta zauna "my dear zanci abincin nunu ta mata da taci hannu tasa tanaci ta kalli jawa wai har yanzu cikinne ke miki ciwo" A,A da sauki

dagashi batace komaiba kadan Ramlat taci taje ta wanko hannuta tazo ta zauna suna hira da umma bata koma bangarantaba saida aka kira sallah magrib ta tafi wanka tayi tayi sallah tana zaune saman sallah har akayi isha, tayi ta tashi ta shirya cikin Riga da skirt ta saki kitson kanta tayi kwalliya ta hadu iya haduwa ta fesa wani rikitattan turare ta sabko kasa dakin jawa ta shiga suna hira da umma ta zauna kusan jawa " my dear kallonta tayi" ya de " babu komai babyna bacci take ko " e mikewa tayi ta shiga bathroom "ummana na tafi parlo nayi fushi tunda baby tayi bacci ta barni dariya tayi " ai wa zai shiga tsakanin uwa da yarta ficewa tayi ta dawo parlo ta zauna tana kallon Tv jawa tayi baki sai kusan karfe goma soja ya shigo ya sameta ita daya azaune " my zumatyna baki kwantaba baki ta turo " kanaga baby tayi bacci ta barni hannuta yaja suka tafi kan dining ya zaunar da ita ya zuba musu abinci a plate daya yanaci yana bata har suka koshi
Chapter 84 · 0% Book details