← Book details Hatsabibiya Ramlat Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 44 OF 152

Sashe 44

Hatsabibiya Ramlat Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

Lumshe idanta tayi ta Dora kanta agirjinsa ta sa hannuta saman fuskarsa tana shafawa murmushi yayi ya dukota cak kamar baby ya zaunar da ita saman kujera ya zauna kanta ta Dora saman kafadarsa hannuta saman sajan fuskarsa tana shafawa " my angel ina yan uwanki kallonsa tayi tana dariya

Hancinta ya lakata yana murmushi ina jawa ko tana wanka janyeta yayi daga jikinsa " kai zauna bari nayi wanka kafada ta makale tana turo baki har ta fara hawaye hannuta ya kama suka nufi bangaransa suna shiga yaji kamshi mai dadi ya lumshe ido ya zaunar da ita bakin gado ya dauki towel ya nufi bathroom ya cire kayan jikinsa ya sakarwa kansa shower aransa ya kecewa inama da angel dita Muke wanka nan amma akwai lokaci

Yakima sosai Kafin ya gama ya fito daure da towel ruwa na diko daga kansa Ramlat na ganinsa ahaka ta rufe fuskarta dariya yayi " yarinya zaki Sanine kawai lokaci jikinsa ya goge ya murza mai ya saka jallabi kasancewar magrib ya kusa ya fesa turaruka masu kamshi ya tsaya gabam mirrror ya taje sumar kansa wace ke kwance luf luf ya nufi gunta ya Sanya tattausan hannusa ya dagota cikeda shagwaba tace" Abbie " ya akayi Mrs Abdallah janyota yayi jikinsa yana shafa fuskarta

Jikinsa ta shige tana cusa hannuta cikin kwantacciyar suman kansa murmushi yayi ya kamo fuskarta yayi mata kiss agoshi ya janyeta " my Ramlat yanda kike mahaukacin sona nima haka nake sonki to wlh ni kaunata agareki tafi wace kikemin hannuta ya kama suka fito parlour ya zaunar da ita ya bashi wayasaa tashiga yin geme tana dariya dakin jawa ya nufa ta fito daga toilet

gunta ya nufa yana murmushi da gudu ta karaso ta rungumesa tana dariya rungumeya yayi ya shafa bayanta" jawata nayi fushi shine ko kizo tarbata kina daki abinki sai kanwarki ta tarbeni" I'm sorry my love wlh ina shiryawa ne sannu da zuwa ya gajiya ya hanya " Alhamdulillah zaunar da ita yayi ya daga rigarta yana shafa cikinta ya kai bakinsa saman cikin yayimasa kiss yana lasar kasan cibiyata dariya tayi

Ta janye murmushi yayi yana kallonta " da fatan bakya cin maiko dayawa kai ta girgiza" ina kiyayewa kallonsa tayi wlh my love kayi kyau sosai ka Kara kiba murmushi yayi " ai kema kinyi kyau abinki rungumesa tayi ta Dora kanta girjinsa tana dariya " to yanzu sai asakeni natafi masallaci nice su shirts daga nazo na kaisu gida dariya tayi " to kabari mana sai gobe ka kaisu

janye jikinta ya Mike suka fito yana rikeda hannuta Ramlat hankalinta kan waya ya ficewasa jawa ta karaso tana kallon Ramlat amma batayi maganaba ta zauna tana kiran shaffah sai gasu " wai bazaku ma yaya sannu da zuwaba kuka wani shige uwar Daka " wlh bamu San ya shigoba murmushi tayi

" yazo ya tafi masallaci kallonsu Ramlat tayi tana turo baki jawa tace" my love me kuma mukayi jawa ta kirawo Ancima tazo jikinta na rawa " gani hajiya" yauwa ki doramin dan wake kadan please kiyi sauri Karin nayi sallah " to ranki shi Dade" kutash muyi sallah mik'ewa sukayi" my love tashi muyi sallah mik'ewa tayi ta nufi

bangaran soja tayi Alwala tayi sallah ta ta fito har lokacin basu fitoba zamanta tayi tana geme suka fito jawa ta kira Ancim " ina dan waken " nakusa gamawa " to kiyi maza ya koma kitchen suka ci gaba da hira har aka gama sallah isha Abdallah ya dawo Ancim bata gama ba yana zaune kusan jawa sai hada sai take anki kawo mata danwake ya kalleta " kekuma keda wa" danwake nakejira taki ta kawomin murmushi yayi,

" bata gama bane zata kawo miki muje ki zubamin abinci Ramlat ta sowa tayi tazo kusansa ta zauna tana turo baki ya gani sarai ya basar dan yana cewa ya lalabata to tabara zata

fara masa ya kalli shaffah " kushirya da safe zan kaiku gida, mik'ewa jawa tayi " muje kaci abinci ni na hakura da danwaken dede lokacin Ancim ta Iso da plate a hannuta tana rawar jiki garin ta mikawa jawa tsautsayi ya plate din ya kubce mata sai jikin Ramlat ido Ancim ta zaro jikinta yana karkarwa ta shiga bata hakuri Ramlat wace idanta ya gama rufewa da masifa dama ga haushinta na cinta tayi kukan kura ta damki wuyan Ancim ta shiga duka

Jawa tanufota da niyar rabawa ai kuwa ta hada da ita tana shirin jibgarta da Sauri soja ya janye jawa ya maidata bayansa tana rike da rigar Ancim amma so take ta kamo jawa wace tsoro ya gama ratsata sai in a talatu tana labe taki zauwa, rabiya "ai wlh da ancemin da mahaukata agidan Allah da banzo

karkarwa take shaffah tace" yaya kayi mata magana kar ta kashe yar mutane " Ramlat Saki yar mutane kuma wlh idan kiki kuskura kika dukarmin mata da ciki kema sai jikinki ya gaya

miki ita bata San bama yanayi ganin batada niyar sakin wuyan Ancim ya karaso ya banbare Ancim daga hannuta tanaga ya rabasu ta Ari ta mate dagudu ta nufi bangaransu ta danna sakata in a talatu tana" kibude mutsira tare dan Allah jar takomo kai amma ina takiya kitchen ta shige ta rufo kofar, ai

kuwa Kafin soja ya juya takai kan jawa ta damki wuyanta da gudu ya karaso ya dauketa da Mari Wanda saida jinta da ganinta ya dauke ya banbare hannuta daga wuyan jawa ya ja hannu jawa ya nufi dakinta Ashe abin ya mata ciwo

Kafin sukai kofar dakin ta wawuri plate din da danwake ya zube tayi kansu da gudu tana kuka nabeela tace" yaya ku kauce karta sameku aikuwa cikin Sauri ya kamo jawa suka Duke plate din yabi ta samansu ya bugi kofar dakin mik'ewa yayi ransa a bace ya yace " jawa shiga daki ki rufe. Cikin rawar jiki ta fada daki da gudu ta rufe Ke shaffah maza

dauko kayanku mutafi na mayar daku wanan masifar dame tayi kama wai haukane like ko minene tana ganin jawa ta rufo kofar ta nufo soja da gudu ta fada girjinsa tana kuka tana dukansa banza ya mata ya ja hannuta ya dauki hijabin dayagani kan kujera ya saka mata yaja hannuta suka nufo harabar gida.... ✍🏼

✍🏼✍🏼✍🏼Ladingo ummu Fareesa ce😘
*?‍♀HATSABIBIYA🤷🏻‍♀*
*💖💖RAMLAT💖💖*

*_?KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION_*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

Story & Written by
✍🏼
Ladin'go ikon Allah
yar mutam Niger🇳🇪

*Bismillahir Rahamanir Raheem*

🅿👉🏻5⃣9⃣&6⃣0⃣

.....Har suka zo yatsarsa abakinta sai zuba masa sangarta take iriri yana lalabata abakin get motocin suka tsaya su shaffah suka ficewarsu cikin gida kallonta yayi yana murmushi ya janyeta jikinsa ya bude motar ya fito ya bata hannu ta kama hannusa ta fito

ciki suka shigo yana rike da hannuta har kofar parlour da sallama ya shigo parlour jawa ta amsa tanufo gunsu" my love naji dadi harda my love one ka kawomin ta fada tana jinginuwa da jikinsa ta rike hannuta tana murmushi yayi, kanta ya shafa

" kenan nine my love two ko Ramlat one to keko fa love wa zance miki dariya tayi ta shafa fuskarsa hannu ta mika ta rike Ramlat takiya tana boyewa bayan soja tana turo baki ta ture jawa ta rungumesa sosai tana cusa kanta agirjinsa yada jawa bazata iya tabashi ba abin yama jawa ciwo mutika tin shigowarsu yada tags yariketa gam daurewace take kallon jawa yayi ya mata magana da ido barin wajan tayi idanta

har yaciko da kwalla janye Ramlat yayi daga jikinsa ya janyo hannuta suka zauna yana murmushi " Mrs Abdallah kifa zauna dam banda rigima koreshi tayi da idanta Wanda ke cikeda ruwan hawaye tana turo baki Alamar fushi take hannuta ya kamo yana murzawa ya kafeta da ido Su shaffah tashi sukayi sukabi bayan jawa dan dariya ta kamosu yanaga sun tashi ya rungume Abarsa yana mata rada akunne cikin wani

Irin salo nerke masa tayi hawaye sharkaf afuskarta fuskarata ya kamo yasa harshensa yana lashe hawayen " my Ramlana kiyi hakuri wlh kin fiye kishi dayawa to yazanyi da raina itama matatace Dole zata rabu jikina ririkeshi tayi ta fashe da kuka tana kiran Abbie tana tusa kanta akirjinsa ya rasa abinda ke masa dadi daukarta yayi cak ya nufi bedroom dinsa da ita,

Saman makeken royal bed dinsa ya kwantar da ita ya mata rumfa da faffadan girjinsa ya zuba mata mayatatun idanunsa itama shi take kallo ido cikin ido suke kallon junasu lumshe idanta tayi face dinsu ya hade ya kamo tafin hannuta yana murzawa ahankali ya Dora bakinsa saman kunanta " my ange wallahi ina sonki sosai duk bugon da zuciyata zatayi da

sonki da kaunarki take bugawa bakinsa ya maido saman lips dinta yana lasa murmushi tayi itama ta fara yin yada yake mata wani irin salo ya rika mata cikin dubara har yasamu tayi bacci Wanda shine kadai hanyar da zai samu ya tafi hankalinsa kwance batare da ya tunanin ko tana can tana kukaba janye jikinsa yayi yana murmushi ya gyara mata kwanciya yamata kiss saman goshinta da lips dinta ya gyara mata gashin kanta ya lulubeta da blanket ya kunna Ac

Ya feshe dakin da turarukan daki ko ina ya dauki sanyi dadi da kamshi gadon ya Kara hayowa ya janye blanket din ya kamota ya jinginata da jikinsa ya sa hannu ya zage zip din rigarta ya cire rigar ya shimfideta " kiji dadin bacci abinki my Ruhina lulubeta yayi ya sabko kofar ya janyo ya fito fuskarsa dauke da murmushi bangaran jawa ya nufa su Nabeela suna parlour kallonsu yayi" ina jawa mik'ewa sukayi shaffah tace " tana cikin bedroom shigewa yayi ciki sukuma suka fito suna dariya
Chapter 44 · 0% Book details