← Book details Hatsabibiya Ramlat Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 36 OF 152

Sashe 36

Hatsabibiya Ramlat Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

zakiyi kuka kici gaba da cizawa indai zakiyi farin ciki zaunar da ita yayi ya saka mata yatsar abakinta kin cizawa tayi ta fashe masa da kuka ta kifa kanta acinyasa " Ya Salam please abar kauna kibarni haka ya kikeso namiki nifa ban hanaki ba to kukan na menene kinsa zakiyi kuka kika cijeni ni banjo zafi ba tana yuwa muguntar kice ta motsa amma

Wayarsa ce tayi ringing da Sauri ya kalli idan take aje hannu ya beka ya dauki suna Abbie ya gani saman screen din gabansa na faduwa yayi picking " hello Abbie " Abdallah ku uku fa kadai ake jira kowa yazo har

mijin Ramla da iyayansa " to Abbie gamunan tini zufa ta fara karyo masa ya kalli Ramlat ya dago kanta fuskarsa tab da hawaye kallonsa tayi tana ganin hawaye ta fashe da kuka. Ta kamo fuskarsa tana girgiza kai

Baice mata komaiba ya Mike tsaye ya dagota ya goge mata hawayen fuskarta yana girgiza mata kai itama hawayen fuskarsa ta goge masa tayi murmushi tana girgiza masa kai

boye damuwarsa yayi yamata murmushi ya sumbaci goshinta itama ta sumbaci karan hancinsa tana dariya hannuta yaja suka fito a harabar gida yaga jawa " jawa tin yaushe kike nan murmushi tayi " yanzu ne

nazo kiranku Ramlat sai baki take turowa bai kulataba ya kama hannu jawa da hannu daya suka fito saida suka zo kusan jama'a ya saketa Ramlat ko tacika tayi fam yana lure da ita murmushi yayi aransa yace tab kina hakama kinsan zafin kishi to ina GA lafiyaki lau dakin taron suka shigo masha Allah

an hallara kwansu da kwarkwata wajan Naseer ya nufa sulaiman sai boye dariya da takamosa yake dan yaga irin tijara da Ramlat ke sonyi masa sai hararasa take Naseer ma gintse dariyasa yayi

Dayake tanajin haushinsa sai taki binsa tayi tsaye tana kallansu sai turo baki take yinma tace khairat taje ta janyo Ramlat zauwa tayi ta kama hannuta batayi musuba ta bita ta kawota gun yinma ta zauna nuratu na mata magana tayi banza da ita sai bankawa soja da jawa harara take, Ahmed kuwa tamkar ya sace Ramlat

yakeji yada ta Kara kyau akwana hudun da bai gantaba. Da Adu'a aka bude taro tsoho mai ran karfe yace "

inaso ku bani hankalinku da kyau bakomai bane yasa akayi taron gagawa sai dan saboda Ramlatu da kuma halin da take ciki yananuna Ahmed dan haka ni usman Mani buzun bagayyah

nayanke hukuncin kuma inji wanda ya isa yaja dani yaga bacinran cikeken buzun Agadez dan haka na yanke hukuncin zan daurawa Ramlatu Aure gobe bayan sallah juma'a Da... bai idasa maganar ba yaga mutum agabansa tamakar an jefushi daga sama..... ✍🏼

✍🏼✍🏼✍🏼Rahma ummu Fareesa ce😘
I *?‍♀HATSABIBIYA🤷🏻‍♀*
*💖💖RAMLAT💖💖*

*_?KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION_*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

Story & Written by
✍🏼
Ladin'go ikon Allah
yar mutam Niger🇳🇪

*Bismillahir Rahamanir Raheem*

🅿👉🏻5⃣3⃣&5⃣4⃣

....."dan Allah mai ran karfe ka taimake ni ka daurawa Ramlat aure dani wlh bata yada da kowa sai ni aganinku wa zai rike Amanar mai dauke da laruru irinta Ramlat in ba nataba,

Tinda ya fara magana kowa kallonsa yake cikeda mamaki tsoho mai ran karfe kallonsa yayi yana murmushi " to ai kayi gajan hakuri ai dama dakai zan daura duba da halin da take ciki Dole sai da nata shi zai iya hakuri da ita amma da sharadi

duk lokacin da ta dawo haiyacinta mutikar tace bata raayin zama dakai to fa bana, cikin masu ta kurata dan haka kuma ina gargadarku da babbar murya Ramlatu idan idan tashi daga bacci da take to idan tana raayin zama dashi to ta zauna idan bataso to tasu ta rage dariya,

Yabasu dayace dogon bacci kallon Ahmed yayi " to Ahmadu dan Allah nayi hakuri kaga a halin da take ayanzu tofa bazaka iya zaman aure da itaba kuma itama bazata yada dakaiba saboda ahalin da take da Abdullahi kawai tasani saboda hakane na yanke shawara daura musu aure saboda yawan shiga jikinsa da

Take hakan bai daceba dukda dan uwanta ne amma hakan bai kamataba yakali iyayan Ahmed da jikinsu ya riga yayi sanyi " inaso kumana Afuwa idan ba haka ta faruba to da babu abinda zai hana auransu mu bamayi da fasawa amma GA shaffah nan idan babu wata Matsala to nabashi auranta,

Ahmed fashewa yayi da kuka" dan Allah kumin rai wlh inason ahaka zan zauna da ita karku rabamu wlh ni take so " yi hakuri babu yada zamuyi mu dauki diya mubaku cikin halin larura bayan bamuda tabbacin warkewarta sani na GA Allah gashi tana yawan shiga jikin dan uwanta wanda hakan bai daceba dukda ba ahaiyacinta take a gwara adaura musu aure,

mahaifin Ahmed ya kamashi yana lalashinsa " haba my son kamar bakasan kaddara ba kayi hakuri ka fahimcesu ni nagane ahalin da take ciki idan ba soja ba to bata yada da kowa tayaya zaka ayi zama da ita bayan ayanzu bata sankaba, ya Kalli tsoho mai ran karfe,

Abban mun amince da auran yar uwata hannu yasa a aljihun wandonsa yaciro kudi ya aje gaban tsoho mai ran karfe gashi muna nemawa yaranmu sauran shaffah hamza ya task ya dauki kudin " mun amince mun baka amma karike kudin sai abayar da nawajan Ramla " a haba ai bazaayi hakaba wanan mun yafesa ai nima yatace zan iya aurata gawanima dan haka indai,

An bamu ita to Kurile wanan kudi akan kudin tambaya hamza yada kudi aljihunsa yana dariya " to nabaku Allah yasanya Alheri " Ameen tsoho yaci gaba da magana " to Alhmdllh naji dadin yada ka fahimta sosai Allah yabar zumunci dan haka gobe idan Allah ya kaimu zan daurawa

Abdullahi aure shida Ramlatu bayan sallah juma'a sai kutayata da adu'a Allah yabata lafiya ke kuma jawuhir kike kowa sai kisawa zuciyaki hankori murmushi tayi ta boye hawayan fuskarta " ai babu komai tsoho Allah yasanya Alheri kowa saida ta bashi tausayi yada ta nuna bata kishin Ramlat Soja ranshi fari,

Kal yasami abinda yakeso sai lokacin ya zauna dan tunda ya wontsulo aduke yake duka dakin taron saida sukayi dariya da iron gurfanar da yayi gaban tsoho mai ran karfe duk abinda suke Ramlat da ido take binsu dan basanin abinda sukayi tayiba haka taron ya watsa masu farin ciki nayi masu nuna jin haushi nayi suna fitowa Ramlat tabi shaffah taki ta kalli ko inda soja yake suna shigowa

Parlour tayi zamanta tana kallon Tv shaffah ta shiga ciki tana Rusa kuka dan Allah yagani batadon Ahmed anwar takeso parlour ba kowa sai ita daya su yinma sun tafi part din anty Rahma domin sukara jajantawa da sallama ya shigo jawa na biye dashi ko kallon inda suke batayi ba, zama yayi

" jawa kawomin ruwa mai sanyi kitchen ta nufa kallon Ramlat yayi " my angel baki ganniba ba ko magana jawa takawo masa ruwa mai sanyi gora ruwan har zufa ke fitarwa ya amsa ya bude " ngd matata kinada kirki murmushi tayi " ba komai yayana wai me muka mutuniyar naga taki kallon inda Muke,

Murmushi yayi " a to ni ina zan sani zoki zauna " bara na shiga na duba shaffah shi sai lokacin ya tuna da abinda aka mata wanda ba lallai bane tana so shigewa tayi tana murmushi dan ta harbour jirginsa soyake ya fara ba Ramlat ruwan Tasha kafin shi yasha, dawowa kusada Ramlat yayi ya zauna gora ruwan yakai bakinta taki sha kanta ya rike ya kafa mata gora ruwan ya tsareta da manyan idanunsa lumshe idanta tayi ta shiga shan ruwan,

Saida Tasha kudan Rabin gora ta cire bakinta sakin kanta yayi ya matsa gefa ya Kafa bakinsa saida ya shanye tass yayar da gora yana kallonta " Abar kaunata I love u baki taturo gaba ta kauda kanta gefe kusanta ya dawo ya mikar da ita tsaye " to shikenan tinda hushi kike dani na tafi shiga gun su shaffah banaso kina zama ke kadai zan dawo dadare nabaki magani Jan hannuta yayi ya rakota har kofar daki ya juya zai tafi fashewa tayi da kuka ta biyosa,

Ya Salam to ya zan miki kinki min magana bansan menayi ba kusansa tazo ta tsaya tana kuka hannuta ya kamo suka dawo parlour ya zaunar da ita shima ya zauna yana goge mata hawaye ahankali ta kirasa" Abbi "na'am Abar kaunata ya akayi hannusa ta kamo ta Dora kanta tana sabke ajiyar zuciya kanta ya shafa " my angel ina mugun sonki fiyeda komai dake wanan duniya Allah yasa duk ranar da kika tashi kici gaba da sona kamar yada nake gani sona a idonki can baya da kuma yanzu

dan na ganoki kishine ke damunki amma nasan da kina cikin hankalinki bazakiwa jawa hakaba saboda yarinya tanada kawaici da hakuri my angel jeki gun shaffah yanzu zan dawo kinji kafada ta make lalabata ya fara har ta dan sake yakaita gunsu shaffah ya fice daga gidan, mamah yau jitake kamar ta tashi gidan da yaki dan bakin ciki ace an dauki yan mata biyu Anba soja amma ba yarta safna

Duk bokayan da tabi da malamai sun tashi abanza haka safna tayi ta kuka tagaji mamah tace" ki kwantar da hankalin ki in sunsan wata ai basusan wataba so kiji ai kinsan jawa ba wani wayone da itaba rada ta mata akunne suka bushe da dariya suna tabawa,

Anty maimunatu ba karamin dadi tajiba da wanan hadi sai adu'a take Allah yaba yaransu zaman lafiya saboda tasan jawa batada Matsala anty rahma ko bataso ba dan babu yada zatayine saboda sanin halin yarta ita tsoranta daya ta dawo daidai tace batasan aauran shine damuwarta,

Tinda Abdallah ya fita bai dawoba sai wajan Tara na dare yana mambila da sallam yashigo parlour tana ganisa ta miki yinma tayi dariya" ikon Allah tin dazu take raba idanu amma kaga yau nasan yinwa takeji batawa kowa magana ba taje dinning taciko cikinta nayi nayi Tasha magani takiya hannuta ya kamo suka zauna
Chapter 36 · 0% Book details