← Book details Hatsabibiya Ramlat Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 26 OF 152

Sashe 26

Hatsabibiya Ramlat Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

Da misalin karfe shida ya yanma duk an gama shirin zuwa Dinner Ramlat tayi muguwar haduwa tayi kyau har tagaji sai kace itace Amarya ankon Dinner tasaka wani tsadadan material ne sukayi duka yan matan kalar blue ne dinkin riga da skirt ta zubo kitsonta har gadon bayanta tayi daurin ture kaga tsiya tayi wanka turare ta dauki karamar haka ta fito a parlour suka gamu da shaffah sun saka nasu ankon" to sai mun hadu nida safna muntafi gun jawa " ok kuje dani saarkuce nifa miji

gareni ya zan rika yawo daku dariya suka suka fita fitowa tayi tana rausaya ta nufi part din Dada ta jira Ahmed karfe shida da minti ashirin wasu dakadakan motoci farare tass dayace baga wulwuleliya sukayi parking akofar gidansu jawa lokacin an gama shiryata cikin wani arnan material kalar pink dinkin doguwar Riga an mata make up tayi kyau masha allah

Fito da ita akayi har gun motocin acikin bakar motar aka sata sauran duka suka shiga sauran motocin har su shaffah tana zama taji wani niimatancan kamshi ya daki hancinta kallonta takai gun yana zaune ya hade cikin tsadadan soweet baki fuskarnan tam ba rahama bakinta na rawa ta gaishesa " yaya ina yini saida ya sha kamshi ya amsa har suka zo bai yi magana ba akofar Sharaton hotel motocin sukayi

parking tin daga kofar kakejin tashin kida duk sauran jama'a suka firfito motar da suke ciki aka bude Ana watsa musu franni fitowa yayi itama ta fito hannuta ya kama matanan na biye dasu suna watsa musu franni har tsakiyar hall din babban abokin ango ya tarbesu ya kaisu har wasu kujeru na alfarma da aka tanada dan zaman ango da Amarya can sama hawa sukayi suka zauna hall din ya dauki ihuu aka Saki sauti a hankali kida ke tashi su jameela sai Tara baki ake Ana raba abin motsa baki habeeb soweet bakine ajikunsa irin na ango da sauran abokaninsa na daga gefan ango " Amarya kirawo babbar kawarki lumber

Ramlat takira bugo daya ta daga " ke gamufa mun shigo " ok to sai kin karaso suna shigowa kallo ya komai kan Ramlat saboda wani masifar kyau da ta zuba hall sai ihuu GA irin matan da ake yayi itako cikin takon kasaita take takawa sai karwa Ahmed murmushi take har suka zo tsakiyar hall din sai lokacin soja ya ganta saida gabansa ya fadi hango

Jawa tayi dabda soja a zaune ta nufo gun fuskarta a sake ta karaso " kai sister Ashe da gaske ke kika auri soja kai gaskiya ina tayaki murna murmushi tayi " thanks kanwata zo ki zauna gaba daya kowa Ramlat yake kallo " my Ahmed nazauna nice babba kawa kafin afara casu gira ta daga masa

Murmushi yayi" to my babyna bari in koma gefe nayi tsaronki " gud na kudin, habeeb tinda ramlat tashigo hankalinsa ya tafi akanta yazuba mata ido saida ta kamashi yana kallonta ta hararesa taja tsaki taro aka fara budewa da Adu'a habeeb ya bada takaitacan tarihin ango wanda kowa saida ya dara akace babbar kawar amarya ta bada tarihin amarya cikeda nutsuwa Ramlat ta bada tarinhin jawa shima andara sosai soja yayi mamakin yau ramlat yada ta tsaya sak tayi Abu na gaskiya Ana gamawa

MC ya bada umarnin ango da Amarya su yanka cake mik'ewa yayi cikin nutsuwa ya kama hannuta suka sabko hall din ya dauki ihuu yankawa yayi ya bata abaki fuskarasa cikeda murmushi ya boye damuwarsa ihuu aka dauka itama ta yanko Cake din cikeda nutsuwa ta bashi abaki ya amsa hannuta ya rike saida ya sude ya tsarta tass aikuwa aka Kara sakin ihuu sai kunyi masoyan asali kidi aka Saki masifar dadi

cikeda farin ciki Ramlat ta Mike tana goge hawayan da batasan ta inda suka fitowaba tamkar an kunna fanfo filin tashiga ta fara taka rawa gashi hall din ya cika makil da jama'a manyan samari masu jida kansu sai barin kudi suke mata Ahmed yazo yana zuba mata nera ya tatare yada ba wanda zai raban

masa mata sai ta tsinci kanta a farin ciki sauran tan gidansu suka shigo taron suna murmushi dan ta burgesu yau anutse take komai rawar ma ahankali takeyi kamar daga sama taji Ana kwasa mata Mari anajan hannunta ihuu ta kwarara" wayyo za,a saceni afilin taro mijina kawomin dauki Kara wanka mata Mari akayi anajan hannuta ihuu take tana tirjewa..... ✍🏼

✍🏼✍🏼✍🏼Rahma ummu Fareesa😘
♀HATSABIBIYA🤷🏻‍♀
💖💖RAMLAT💖💖

*_?KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION_*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

Story & Written by
✍🏼
Ladin'go ikon Allah
yar mutam Niger🇳🇪

🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣😆😆NI KAM BANIDA BAKIN MAGANA JIYA SHIYASA NAFECE ALQURAAN JIYA NAGA TAKAI🤦🏻‍♀ALLAH YA BAKU HAKURI🤣👏🏻👏🏻👏🏻

Bismillahir Rahamanir Raheem

🅿👉🏻3⃣9⃣&4⃣0⃣

......dake gun jama'a tayi yawa mutane kalilan ne suka lurada abinda ke faruwa ihuu take tana tirje bai tsaya ko ina sai bayan hotel gun bakowa sai kukan tsuntsaye da da franni shar hankadata yayi ya hadata da bango yana hushi, ya mata rumfa da fafadan girjinsa cikeda tsoro ta dago kai

Tana kallonsa yanayin da tagansa acikine ya tsoratata amma, sai ta cije ta basar da tsoran ta hade face " malam lfy karaboni da mijina da jama'a kakawo ni nan shakarta yayi tin karfi "dan uwarki ko ina sai kin Nuna ke karuwace ko kunya bakiji kina tsakiyar kartin maza kina rawa ke ga yar iska ko shikuma sakari da baisan ciwon kiba yayi tsaye wasu kartin banza suna zuba miki

,kudi ko to ubanwa yace kizo, gun bukina bana bukatar ganinki agun tinda ya fara magana take kallonsa ranta yayi masifar baci sai huce take idanta yayi jawur ya Kara kankancewa " ok to sakeni ni kuma daga yau zan nuna maka na haihu uwa da uba tinda har tsanar takai haka to karubuta ka aje ni Hassana Ramlat hamza usman buzun Bagayyah,

Nafita daga harakar Abdullahi Mustapha usman Buzun Bagayyah insha Allah daga yau bani ba kai zan kiyaye duk wani Abu da zai hadamu Amma kasan matarka yar uwatace wada muka shaku duk da tafini shekaru amma ba wada tafi so sama dani acikin Family dan haka bazaka rabani da ita ba takai karshan maganar tana sakin kuka sakeni na kira mijina mubar gun taron tinda

baka bukatarmu fuskata ya kamo ya hade face dinsu suna shakar numfashin juna haka kawai yakejin bai kyauta mataba kuma yauce rana ta farko daya taba jin tausayinta har cikin ransa kallonta yake ko kiftawa babu lumshe idanta tayi zuciyarta na mata zafi ahankali cikin irin wata murya yarika mata magana tamkar mai rada,

" my angel ba nace ki bar barin idonki nayin ja dayawa ba ahankali ya fara hura mata iskar bakinsa acikin idanta yana shafa fuskar ya koreta da ido tinda ya kirata da angel ya tado mata mikin son Aljaninta amma da ta tuna cin fuskar da yake mata ta ingijeshi amma ta kasa fashewa tayi da kuka " wlh ka sakeni hakan bai daceba kai mijin jawa ne kuma ni wlh jinake hannuka kamar garwashin wutane yake tabani cikin tsawa

tace Abdallah I hate you ka matsa na tafi kuma allah ya isa ban yafeba da karabani da my Aljanina cikin zafin zuciya ya hankadata ta fadi kasa" Ramlat nima na tsaneki kijira sakamakon takalmin da kika bugamin ina tune kinci bashi yar iska tantiriya kawai

Fuuu ya huce yabar gun nan ta Duke tana kuka saida tayi mai isarta kafin ta Mike tana jero masa allah ya isa " mugu allah hadaka da cutar ibola, wlh ni yanzu na tsaneka Ahmed ko ya bazu neman Ramlat dan yaga Abdallah ne yajato hankalunsa atashe yake nemanta adede kofar sukaci Karo da soja " yauwa soja ina matata allah yasa ba wani laifi tamaba kasan ya saita ya kakalo murmushi " ai tana na kofa da baki kaje cikin Sauri yanufi kofar agun motarsa ya ganta atsaye ta goge fuskarta

Tamkar batayi kuka ba" my baby ina kika shiga duk kin tadamin hankali cikeda shagwaba tace" bayan mugun sojane yaci zalina " dakika masa me " haka kawai ai nabarsa da allah my Ahmed my tafiyarmu gida muyi hira wlh na tsani gun taron " muje damage nagaji yada ake kallemun ke murmushi tayi ya bude mata mota ta shiga ya kewa ya shiga,

Yaja suka tafi yana mata hira barkwanci sai dariya take kyakyatawa " wlh my Ahmed zaka kasheni da dariya " my babyna idan na kasheki na rayu da wa haka suka tafi suna hirasu cikin wasa da dariya

Lokacin da Abdallah ya koma cikin hall din cike yake anata neman amarya da ango sufito fili habeeb ya kalesa " soja wait ina kashiga ne anata nemanka ta " bakaga yar iskar yarinya nanba na fitar tantiriya kawai " wlh nikuma ta burgeni zakubani ita please wlh ina sonta face ya hade " uhm allah kyauta da kasha fama kuwa an mata miji wanan da kagansu tare shine mijin auran baya wuce 1 mount"

Wlh naso ace ba,a riganiba basar da zancan yayi yaje ya kamo hannu jawa suka shiga filin rawa dangi sai barin kudi suke musu da Abokaninsu yanayin yada yake juyawa da ita abin gwanin ban shawa kowa abin ya burgesu sosai safna sai ciza baki take su khairat sai like sukemusu tare da mazansu Nabeela ranta fari tass Family su abin burgewa sai takawa take ahankali angota yazo yana mata barin nera nan dangi suka

shiga neman Ramlat amma babu labarin taron gaskiya ya kayatar sosai dangi sun cashe anci ansha kuma soja yayi kokarin faranta ran amaryasa abin gwanin ban shawa kowa na San barka baatashiba sai wanan karfe goma na dare duk Ana akayi sallahr magrib da isha, jawa ta Kafa masa rigima ina Ramlat batajin dadi banza,

Yayi mata har suka iso akofar gidansu aka ajiyeta tare da sauran danginta sukuma suka kama hanyar gida dama ance kai amarya sai gobe zaakawo ta ido na gani suna shigo ya fito abokaninsa suka rufa masa baya hango Ramlat yayi atsakiyar compound ita da Ahmed sai gagaba dariya take hada rike ciki tsaki yayi " mahaukaciya ai ka hadu da hauka in ba iskanci meye har warhaka Ana fira fuuu ya fice dan su basu ma
Chapter 26 · 0% Book details