← Book details Hatsabibiya Ramlat Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 33 OF 152

Sashe 33

Hatsabibiya Ramlat Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

ina son ganinki araye matsawa yayi ya kifa kansa saman nata ya fashe da kuka ya rike hannuta gam anashi yana murza my Hassana ki tashi na miki Alkawarin zan rayu dake cikin wata irin duniya da bakowa yake zuwaba yajima sosai yana magana kamar zautace har saida doctor ya dawo ya janyesa ya rufo kofar suka fito " soja iron wanan fa sai anyi hakuri an gama da Adu'a shi sai yanzu yama tuna

bai mata adu'ar ba fitowa yayi ya nufi part din yinma a parlour ya samesu harda su anty maimunatu " wai Abdallah lafiya duk kabi ka rame kayi hakuri Iowa hakurin yake ba mai ja da ikon Allah jikin yinma ya zauna kansa akasa ya gaishesu " momyna ba komai ai ba maija da ikon Allah yinma ta kalleshi" jawa tashi ki hadawa mijinki wani abu mik'ewa tayi dan it am a tarame tunanin Ramlat ya hanata sakat tashi Abdallah ba wani sosai yake kulataba duk da bai mata walakanci ta nufi kitchen ta zubo masa abinci

Ta kawo masa a kasa ya zauna saman carpet yinma tarika bashi abaki yana ci badan yanajin dadiba har saida yaci dayawa tabarshi su hadeeza na dariya kasa Kasa anaba kato abinci agaban matarsa da suruka banza yamusu yana gamawa ya tashi ya, nufi part,

dinsa aparlour ya zauna yana tuna ranar da yafara iskota tana rawa da ta Gandhi ta Saki fitsari da ranar da ya ganta da kakinsa na soja nanma tayi fitsari sai ya tsinci kansa da yin murmushi

Tuna ranar da ya kuma kamata tana rawa akwance da taganshi tashiga borin karya wai aljanunta sun tashi kuma basason ganinsa nanma dariya yayi ya kalli inda pic dinsa yake da juyasa wai dan jawa tana kallo murmushi yayi " my Hassana I love u more ya tuna taje maids pic zata fado da ya tarota ta fado jikinsa ta rugumesa tana shafa wuyansa

tana masa magana cikeda n nutsuwa wai ai ita yarinyace yarika lalabata sai ta shiryu lumshe idansa yayi ya nutsa hannusa cikin gashin kansa yana shafawa " my angel bazan iya Rayuwa babu keba Ashe kece rayuwata ina sonki Ramlat jawa ce tashigo tazo ta zauna kusa dashi ahankali tashige jikinsa ta rugumesa, dan taji duk abida yake fadi

" yayana nayi hakuri duk tsanani yana tare da sauki insha Allah zata warke wlh dama nasan kana sonta tin ranar da aka daura mana aure dakai kuma ni bana kishin yar uwata wlh nima ina sonta kamar yada kake sonta Allah ya tashi kafadarta,

Rugumeta yayi a jikinsa sosai yana shafa bayanta amma baiyi maganaba idanta ta lumshe ta Kara shigewa jiknsa tana fitar da hawaye kai ya girgiza mata dan yaji dadi da tace tana son Ramlat duk yasan tana son nata dan ko abincin kirki bata iya ci ayanzu kulllum adu'arta Allah ya tashi Ramlat dan haka yanzu yarage jin haushinta,

*********************************

Haka rayuwa tafi gaba da tafiya yau satin Ramlat uku akwance kamar gawa har yanzu bata farfadoba zuwa yanzu duk subarwa Allah ikonsa sun dage da Rokon Allah ya tashi kafadarta yanzu Ana barinsu suna shiga inda take sumata Adu'a su fito bangaran soja ba,acewa komai yazama kamar

zautace saida Abbi ya zare masa tikon ya koma man aiki amma zuciyasa na ga, Ramlat Ada'a tana shanta ba dare ba rana,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,

waiwaye bangaran Rumaisa sosai hauka yayi karfi har Tutu takeci tana sako zata cinyeshi tana cewa min sojana ne jini zansha an saka mata sarka dan ance ba abarin irinsu suna yawo annoba ce aduniya gwara ta karasa rayuwata adaure mahaifinta dan takaici gidan baki daya ya bark ya nemi wani

ya says a unguwar nasarawa yasa ayo masa cigiyar mata mai hankali amma abinciki zuriyarsu kar akuma yar gidan jiya con n sa,a yasamu ta gari ya aura ancewa yabari akwan biyu yace mutanan kirki akewa Kara ba lalatatuba con n ikon Allah yayansu Rumaisa bashida wanan masifa ta msita shiyasa mahaifinsa ya rikeshi hannu biyu sukaci gaba da rayuwarsu

*******

Yau takama weekend Abdallah na gida yana parlour zaune yana tunanin angel dinsa jawa ce tafito tazo ta zauna kusansa " yayana yau bakaje gun angel din kaba kallinta yayi ya mata nuni ta matsu gunsa cikin jin kunya ta karasa jikinsa rungumete yayi yana shafa bayanta" jawa nagode dayada

kike, nuna zallar kaunarki ga Ramlat shiyasa na baki matsayi murmushi tayi " bakomai yayana ai my duka yar uwarmuce tana maga dafda kunnensa wanda hakan yasa ya fara jin yanayinsa na sauyawa,

Yana kikarin janyeta ta Kara shigewa jikinsa ta fara kuka " wlh na damu ta warke ko kaima ka kasance acikin farin ciki tsusayi ta bashi ya rasa mai zai mata taji sanyi dan tadamu da Ramlat sosai fusakarta ya kamo bai bata lokaciba ya hade bakinsu ya shiga bata hot kiss wanda ya Kara rura wutar sonsa aranta nantake takusa zaucewa dede, lokacin wayarsa

tayi Ringing bakinsa yaje zarewa anata amma taki dan wani masifar dadin kissing din takeji kuma shima abinka da ba Sabon shiga sai ya biye mata har yakai ga ya zura hannushi cikin rigarta yana murza na shanunta nanfa suka

haukacewa juna dan jiyake tamkar Ramlat ce gabansa shiyasa ya fara nuna mata zazafan love mai tsayawa arai wayar ta kuma daukan Ringing idansa ya bude ya kalli screen din wayar din sunan dayaga nayawa saman screen din ya sashi saurin dawowa haiyacin sa cikin Sauri ya janye jawa daga jikinsa ya dauki wayar jikunsa har rawa yake yayi picking.....✍🏼

✍🏼✍🏼✍🏼Rahma ummu Fareesa ce😘
*‍♀HATSABIBIYA🤷🏻‍♀*
*💖💖RAMLAT💖💖*

*_?KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION_*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

Story & Written by
✍🏼
Ladin'go ikon Allah
yar mutam Niger🇳🇪

*👉🏻Duk daga Alkalamin✍🏼*
*Ladingo*
*MIJIN YAYA MUNEERA*
*HATSABIBIYA RAMLAT*
*MIJIN TEEMAH SABON SALO*

*Bismillahir Rahamanir Raheem*

🅿👉🏻4⃣9⃣&5⃣0⃣

....." Abbie doctor Abbie Doctor kallonta yake cikeda mamaki saboda ta maimai kusan so coma kuma taki sakinsa " my angel ki sakeni na bude kofar ai Abbie ne zai shigo da sauran family mu kin sakinsa tayi taci gaba da kiran Abbie da doctor,

Zama yayi ya cikin dubara ya cire hannuta daga rikon da tamasa " yau kuma dan na nunamiki so shine ko cikin Sauri ya Mike ya nufi kofar ya bado Abbie ne da Papi kusan su goma suka. Shigo cikeda farin ciki,

dede lokacin Dr fahad ya iso Abbie ya nufi gunta" my daughter kintashi Alhmdllh kallonsa take cikeda tsoro tana ganin ya nufota fashewa tayi da kuka tana begawa soja ahannu tana" Abbie doctor da gudu ya Kara ya riketa " my Ramlat Abbie ne fa kinga Papi rike soja

Tayi gam tana kuka Abin yabasu mamaki Dr ya karaso yana kallonta jikin gadon ya karasa dan tuni ya fahimci ta tashi awani hali Abbie ya Kalli Dr " likita me nake shirin gani yarinyana fa ta nuna batan kowaba sai Abdallah me hakan

Yake nufi " wlh Abbie ban saniba bari nima ina zargin hakan amma bari nayi bincike daket tayada Dr fahad ya nufi wani daki da ita domin bincike wanda hankin yan gidansu ba karamin tashi yayiba ba kamar papi da anty Rahama wada har zufa ke keto mata akalla ya kwashe awa daya cur, Kafin ya gano gaskiya Alamari suna fitowa suka fara tambayar sa

Meke faruwa yinma ce zata riko da gudu ta yi wanan Abdallah ta fada jikinsa tana Abbie doctor gaba daya ilahirin jikinsa karkarwa yake saboda ya gama gano komai Ramlat ta manta kowa shima dan shi tafara gani daga tashinta Dr fahad yace " muje office namuku bayani hannuta soja,

Ya kama yabi bayansu cikin rawar jiki Abbie ke tambaya " doctor mai ya fari da hassana nagafa kamar bata sanmuba " eh to haka dan wlh ban taba tunanin zata tashi ahakaba dan nayi bincike lokacin zata iya tashi cikin koshin lafiya amma sai Allah yayi ikon wanda shi kadai yasan dalilin hakan,

Agaskiya saidai kuyi hakuri Ramlat hamza tayi losing momery dinta ayanzu ita da jariri mai sham nono duk daya suke bazata tana yada dakowa idan ba soja ba saboda shikadai ta bude ido ta gani komai sai an koya mata sai kun rinka hakuri da ita dan gabaki dayanku ta manta daku ba

abinda Suke fadi sai innalillahi wainnah ilahirrajuun Abbie yace " to dr yanzu yaya zaayi zaafitarbda ita wajane " ai basai an kaita ko inaba insha Allah tunaninta zai dawo fama dayace yanzu yada zaku rabata da soja dan yanzu haka kallon abin tsoro take mana agunta shi kadaine mutum dan haka,

Sai kuyi kokari kuya mata abubuwa kamar su sallah wanka hata da cin abinci sai an koyamata zan kawo magunguna da zaarinka bata insha Allah zai dorata Alan turbar samun lafiya dede lokacin Ahmed yashigo cikeda farin ciki yayi gunta " my baby ina farin con n tashin Allah nagodema tanaga yana matsowa kusansu ta fasa kuka ta shige jikin soja tana boye kanta tana " Abbie doctor

Cikie da tsoro ya kallesu " dan Allah mi yake faruwa Abbie yayi masa bayanin komai kuka ya fara " Abbie ku taimakeni ku daura mana aure zata warke agidana" haba Ahmed ai in hankali ya bata hankali yake maidosa yarinya da koda uwayanta taking ta yada zamu daura maka aure da ita Dada tace " yanzu Dr zata ci gaba da zamane ko zamu tafi da ita,

" kutafi da ita ai gu dayane zan rika shiga ina dubata tinda ciwukan sun warke sai magani da zata rikasha godiya suka masa suka fito baki dayansu sai boyewa take abayan Abdallah duk tsoraon mutanan take anty rahama tin tana dakewa ta fashe da kuka yinma na bata hakuri a parlour yinma suka taru baki dayansu tana nannage jikin soja taking ta zauna kasa

Yinma tace" to munadi tayi wanka ya kenan mik'ewa yayi ai kuwa ta Mike it am a tana kiran Abbie doctor kowa saida ya mata hawaye saboda tausayi anty rahama tace " dolafa sai ka zare mata ido tanajin tsoranka zatayi wani abun, ke shaffah tashi kuje ki gwada mata yada ake wanka Abdallah ka zare mata ido ko zata yada
Chapter 33 · 0% Book details