← Book details Hatsabibiya Ramlat Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 136 OF 152

Sashe 136

Hatsabibiya Ramlat Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

kana kuwa maida hankali kana karatu kamar Nusaiba " Aunty inayi wlh " OK yayi kyau suna zaune sai karfe goma su mummy suka dawo har ta fara gyangyadi mummy tace" tashi kije ki kwanta yinma tazo " papina sannu " yauwa Ramlatuna Allah ua sabkeki lafiya mikewa tayi tanajin kunya " mummy na tafi hannuta mummy ta kama suka fito saida ta kawota har get d'in su yinma ta koma itako ta shiga suna zaune a parlo ta shigo" dota da yanzu zani kawoki mikewa tayi muje mu kwanta Abbie murmushi yayi" hassana uwar yan rigima Allah ya sabkeki lafiya yinma tace " Ameen ta kam hannuta suka shiga bedroom d'in yinma bathroom tashiga tayi wanka ta maida rigar jikinta tunda batada nauyi dama hijabine kato ta hau gado ta kwanta kusan yinma suna hirasu har bacci ya dauketa saida baccinta yayi nisa Sosai yinma ta sidade ta tafi gun Abbie amma bata wuce awani biyu ba ta dawo ta rungume Ramlat har bacci ya dauketa bangaran Soja tunda ya dawo kowa ya kama gabansa ya bata yarta ta shayar da ita yaje yayi wanka yayi shirin kwanciya yaba jawa magani tasha ya taba jikinta babu wani zafi " bakijin ciwon komai ko " eh banaji " gud sai ki kawanta gadon da yake kusa da na jawa ya nufa ya kara gudun Ac ya kwanta itako suna kwance ita da little Ramlat sai kallonsa take batasan yana Lure da itaba " malama lfy kika tsareni da idanu ko so kike nazo na rungumeki idanuta ta janye daga kallonsa tanaji dama tace masa eh yazo ya rungumeta idanuta ta lumshe ta rungume yarta ranta fari kal har tayi bacci ya dauketa Wanda sama da wata biyu batayi irinsaba baki ya tab'e ya lumshe idanusa yana tunanin Ramlat ko tayi bacci bayaso ya kirata tayi masa rigima baya kusanta bare ya lallasheta yanajin wayarsa daya na kara yaki bude idanusa ma bare yasan ko waye dan ya tabbata ba Ramlat bace yana tunani ahaka har bacci ya daukesa

************
Washe gari bayan Soja ya dawo daga masallaci ya tashi jawa ko tana iya yin sallah tace A,A kawai jini jikinta taje tayi wanka ta canza kayan da Soja ya kawo mata daga gida ta shirya kanta ta koma ta kwanta tana shayar da baby Soja yana kwance yana kallonsu har barawon bacci ya kwashesa itama baccin tayi Ramlat tunda tayi sallah Asubah take ta tunanin Soja tana lumshe idanuta har bacci ya dauketa, karfe takwas nasafe Soja ya farka yayi wanka ya shirya cikin wani danyan boyal bleu ya kalki bangaran jawa tana bacci hankali kwance kusanta ya matso ya gyarama little Ramlat kwancita itama jawar ya gyata mata kanta ya bude kofar ya nufi cikin gida parlon shiru bakowa bedroom d'in shaffah ya nufa ba kowa murmushi yayi ya tuna ita da yinma suka kwana kan dining ya nufa anjera komai cup mai girma ya dauka ya hada tea ya zubi soyayen dankalin turawa da kwai sai farfesun kayan ciki

ya zubi komai yasa cikin dan kwando ya fice har ya dawo jawa bata farkaba aje kwandon ya zauna bakin gadon pillow da take sama ya dan bubbuga " jawahir tashi idanu ta bude bata yada ta kallesaba ta Mike kamata yayi ta sabko toilet ta shiga ta wanko bakinta da fuskarta ta fito ta zauna ta gaisheshi ba yabo ba fallasa ya amasa " maza kiyi breakfast kayan ta janyo da dan sauri taci dan karyaga laifinta tana gamawa yabata magani tasha tana gamawa likita ta buga musu kofa tashi yayi yaje ya bude ta shigo suka gaisa ta dubata tayi mamakin yada bugun zuciyarta ya dawo normal suka shiga wani dan daki ta duba babu wani sauran jinin d'a da yarage acikinta saboda Alluran da tayi mata jiya sosai likitar taji dadin ganin ta warke ras sai dan jini dayake zuba tace zai tsaya insha Allah

amma tace sallama sai yamma zasu saka mata Karin ruwa yanzu da kuma yamma idan ya gama zata sallamesu tayi mata kashedin tarika shan magani akan lokaci kuma ta rage cin Abu mai maiko dan harda fara masassarata ta dan motsa dalilin cikin godiya Soja yayi mata ta tafi kayan da yakawo ya kwashe ya fice ya nufi gida yana zuwa ya iske su Ramlat saman dining kusan Abbie ya zauna ya gaishesu " ya me jiki " Abbie tayi sauki amma sai yamma za'a sakemu " Yayana ina kwana ya mai jiki " Alhmdllh tea ya hada mai kauri yasha yinma tace" to ai sai ka kaimata Karin kumallo " ai nazo na kaimata lokacin baku fitoba yana gama shan tea ya kalli Ramlat " tashi kije gun jawa ni aiki zan tafi zan dawo da marece yinma tace " tashi kuje anjima ganinan mik'ewa tayi dama da hijab ajikinta tayima su sallama suka fito sai cika take tana batsewa

" babyna kina fushi dani " ni ai banceba ko murmushi yayi ya kama hannuta suka shiga hospital jawa na kwance dan maganin jiri kesata kusanta Ramlat ta zauna ta gaisheta da jiki Soja yayi musu sallama rungume Ramlat yayi ya shafi katon cikinta " sai nadawo " Allah bada sa'a ya kalli jawa " Allah kara Afuwa sai nadawo " Allah ya taimaka tafiya yayi gida ya shirya suna zaune Ramlat ta tashi ta koma gadon daya ytayi kwanciyarta suna dan taba hira har dr tazo tasama jawa drip Ramlat
ta dauko baby ta rike, ta

***
tunda soja ya tafi bai dawoba s'aide yayi ta kiransu awaya tare da su yinma suka yini yan gidan kowa bata shigowa d'adama ana tayi yini Aunty maimuna tazo ta dubata ta koma karfe shida aka gama samata drip Dr ta basu sallama suka shiga gida part d'in yinma babu laifi sosai jawa ta wartsake batajin komai yanzu ajikinta tanashan magani akan kari ana Kiran sallah magrib yazo gida Alwalla yayi ya tafi masallaci bai dawoba saida akayi sallah isha, a kan dining ya samesu suna dinner kusan yinma ya zauna Ramlat duk tayi sanyi karai da ita abuncin ma ba wani ci takeba sai jujuya spoon takeyi Soja tunda yazo ita yake kallo shima sama sama yaci abuncin duk tabashi tausayi yasani sarai rashinsa ne tun safe yinma tace " dota kici mana " yinma banajin yunwa na danci kadan mikewa yayi " yinma zamu tafi gida Abbie bai shihoba " bai zoba jawa ku tashi ku tafi gida kanta kasa ta amsa kama Ramlat tayi ta Mike " dota kutafi gida kuje ki kwanta ki huta kinji kai ta daga "to yinma little Ramlat ya dauka datake zaune saman kujera tana tsotsar yatsa ya kama hannu Ramlat suka fito kofa batace dashi komaiba Jawa na biye dasu rigarsa Ramlat ta rike " ikon Allah babyna

saikace makauniya " to ai ni haka nakeso tafiyar murmushi jawa tayi haka suka zo har gun mota ya bude Ramlat baya ta shiga " my love dan Allah ki koma gaba zan zauna abaya " banaso kiyi zamanki babu koma dole ta shiga gaban. Soja yayi kicin kicin da fuska tana Lure amma babu yada ta iya dama gudun hakan yasa taso ta zauna baya yana rungume da little Ramlat yake drinvig ta madubi suka hada idanu da Ramlat ya zabga mata harara kai ya kauda bata sake kallonsa ba har suka Iso honr yayi mai gadi ua bude kofar get ya danno hancin motar gidan parking' spece ya shiga da motar

yayi parking ya bude ya fice yana rungume da little Ramlat ransa duk abace yake jawa ta bude ta fito Ramlat ta fito tana biye dasu a parlo suka iskoshi a zaune ko kallonsa Ramlat batayi ba ta nufi hanyar bene " Ramlat zonan kin zuwa tayi ta karya kwana ta Haye warta jawa ma dakinta ta nufa dan yanzu tana mugun jin tsoransa mikewa yayi yana Rungume da little Ramlat ya Haye saman bene bangaran Ramlat ya nufa tun daga kofar bedroom yake jiyo kukanta da sauri ya karaso cikin dakin ya tardo ta durkushe tana risgar kuka " Ya Salam my babyna da sauri ya karasa ya aje little Ramlat saman gado ya nufi gunta...✍🏻

Rahma ce ummu Fareesa😘

✍🏻✍🏻✍🏻

*🤷🏻‍♀HATSABIBIYA🤷🏻‍♀*
*💖💖RAMLAT💖💖*

*_🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION_*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

Story & Written by
✍🏻
Real Ladingo😉
yar mutan Niger🇳🇪

*👏🏻👏🏻👏🏻DON GIRMAN ALLAH KARKUMANTA DA GIRMAN ALKAWARI DA AMANA KARKU FITARMUN DA BOOK WAJE KUKARANTA KYAUTA RUWAN ALLAH AMMA ARIKE AMANA👏🏻👏🏻👏🏻*

*Bismillahir Rahamanir Raheem*

*Book 2* 🅿👉🏻4⃣5⃣&4⃣6⃣

...batayi magana amma ta rage kukan" My Sweet heart kishine ke damunki saboda kina son mijinki shima yana sonki please kiyi hakuri my babyna kaface kika takura to kuma gashi kishi ya damarmun ke ya fada yana bubbuga bayanta bakinsa yakai saitin kunneta "My Heart beat ajiyar zuciya ta sabke ta Kara shiga jikinsa "Na'am yayana " yi hakuri bari kukan tashi muje nayi miki wanka mik'ewa yayi ya dagota ya cire mata hijab ya cire mata kayanta ya dauketa camak ya shiga bathroom da ita shower ya kunna sama sama yayi mata wanka sai sabke ajiyar zuciya takeyi ya daura mata towel ya daukota suka fito ya goge mata jikinta ya shafa mata mai ya bude wardrobe d'inta ya ciro mata rigar bacci yar karama mai dan fadi ya saka mata da idanu take binsa murmushi ya sakar maya ya jata gaban mirror ya rungumeta suna kallon juna " my angel kinyi kyau murmushi tayi ta shafi fuskarshi tana Sosa masa gashin sajansan fuskarsa" nagode my sojana daukarta yayi ya kwantar saman bed d'inta ya zauna yana tausa mata kafarta idanuta ta lumshe dan bacci takeji " my sojana bacci " my bugun zuciyata Oya yi baccinki Soja nakine har abadan
Chapter 136 · 0% Book details