← Book details Hatsabibiya Ramlat Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 8 OF 152

Sashe 8

Hatsabibiya Ramlat Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

ya zage yaci sosai ya tafiyarsa part antysa suka gaisa can ma da jama'a " abdallah meyasa kasa ma Ramlat ido alhalin kasan kai kade ke iya mata batare da an sami matsalaba ka kyauta kenan yanzu ayau idan nacema na ganta a matsayina na mahaifiyarta nayi karya tayi ba daidai ba Dana mata fada cibi ya zama qari jiya haka irin barna da taminba saikace yarinya yar Karama, baki ya ciza" anty kiyi hakuri komai zaizo da sauki nasan maganinsu daga ita har saurayin ta an gamamin bincike akansa kuma mum gama magana da abbi da papi yanzu haka shima a gidansu ansaka masa matakan tsaro kuma basa haduwa wayarta na wajena kibani kwana biyu agama wanan bikin komai zaiyi daide gara amusu aure kowa ya huta farinciki kan fuskarta " amma Dana Abdallah allah yana albarka allah ya nuna min wanan ranar murmushi yayi " Ameen anty kuma kema kinyi suruka a kaduna " kai dan allah kace agida to allah tabatar da alkhairi amma akawo min ita " ai tana zowa gobe gun biki kuma gunki zata sauka " amma nani dadi allah yasa ayi biki a kusa murmushi yayi ya fice,

Part d'insa ya nufa yana Shiga parlour fara dudubata ya farayi can wani daki suka sata tana zaune yunwa takeji sosai, kitson kanta ya damko ya janyota har parlour ya ya wurgata saman carpet zaunawa yayi saman wata lumtsumemiyar kujera " tashi maza ki zauna tashi tayi ta zauna jikinta sai karkarwa yake dan yau bata ga sasauci ba, tsawa ya Daka mata

"matso nan kusansa ta matsu ta zauna " Ashe har Club kike zuwa mu muna famar rage karuwai agari Ashe agidanmu akwai ranta ya fara sosuwa sosai saide ba yada ta iya dashi ina so ki fadamin tin ranar da kika fara shigowa part Dina kina iya shege ko yanzu jikinki ya fada miki, shiru tayi,

Matsowa yayi ya damki wuyanta ya shaketa tin karfi " wlh idan baki fadiba zan kashe na rage mugun iri gani tayi dagaske yake zai kashetan ta fara magana muryata bata fita sakin wuyan ta yayi yana saurarata " kullum idan baka gari nake zauwa nayi rawa ko nayi bacci a part din yinma nake daukan makulai amma na tuba bazan karaba yi hakuri kifa mata Mari yayi " yar iska ni saanki ne kai ta girgiza tana hawaye " wlh soja bazan karaba natuba " to zuwa club fa tin yaushe kuma wayasa kika dauki motar da zan ba matar da zan aura kika Shiga zaki yawo" Club ban jimaba da fara zuwaba nade wlh bazan sake zuwa mota ko yau ne kadai na taba Shiga,, iska ya buso daga bakinsa sanin irin wanan baa kore musu guri ya mata shiru,

Cikinta ta rike tana hawaye " soja yunwa nakeji please taimakamin banza ya mata zuwa can yace, " ai yau baki Rama abinda na mikiba wayarta ya beka mata kai ta girgiza taki amsa bakinsa ya ciza" Ashe kinsan ga,bar

sonake ki sakamin kunama irin ta ranar kokuma ki rike min idona tinda, ke ba, a cin zalinki ai ni na sakasu ni yaka mata kima basuba, bindiga ya fito da ita ya aje wlh idan bakimin yada kika musuba to. Zan kasheki aide kinsa ba wanda yasan kinana, oya ina jira ki illata ni karma yada kikace ba acin zalinki

kai ta girgiza " au bazakiyi ba kenan, ki saka min irin ta ranar sai na kawo miki abinci, oya ina jira kanta akasa jitayi bazata iya masa mugunta ba yau tsawa ya Daka mata to zaki kwana haka fashewa tayi da kuka hannuta kunamune biyu amma jita yi ko zai kasheta baza saka masaba mikewa yayi ya fara tafiya " ok ki kwana Ana da gudu ta bisa " to gasu hannuta ta nuna masa " ok sakamin sai nakawo miki abincin a hankali ta karaso gareshi tayi kamar zata saka masa ta Kasa jikinsa ta fada tasaki kuka" wlh bazan iyaba ranar ma sharin shedan ne na hakura da abincin, shigewa, jikinsa tayi sosai tana Shakar kamshinsa soja bazan iyaba fara na kwana da yunwa abin yayi mutikar bashi mamaki,

amma hakan bai sa yaji tausayin taba ingizata yayi dag jikinsa " dan uwarki ni sa an,kine to kiyi ta zama da yunwar ina ruwana, Ashe ke karamar Mara kunyace, ki jira hukuncina na gobe wanda zaifi miki muni Akan, nayau ficewa yayi dan idan baiyi da gaskeba to bazata nutsuba

Kiran wani soja yayi naga yayi masa magana yanufi idan take yace ta tashi ta tafi cikin rawar jiki ta Mike ta fice tana kuka Kasa Kasa, kofar bata tabi inda ba wanda zai ganta ta shige part dinsu bata bi takan kowaba,

ta nufi room dinta tacire kayan tayi wanka sai da ta gasa jikinta sosai da ruwan zafi ta dauro alwala tayi salolin da ake binta kakaf ta fito neman abinci parlour saida taci ta koshi Nat, " anty Ramlat yau ina kika Shiga bata kalletaba tace" gidan ubanki na Shiga " ke nabeela kishiga sabgarki murmushi tayi ta Mike ta fice " ke kuma allah shiryeki baki ta turo ta tashi ta shige cikin bedroom dinta kasancewar ita da nabeela kowa dakinsa daban,

saman bed ta fada tasaki kuka tin karfinta " soja allah ya tsinema albarka mugun banza mai hana ruwa gudu wlh ban yafema zalina da kaciba, gashi yau bani ba zuwa club tana cikin mita har bacci ya kwasheta,

Sauran yan matan gidan kowa na hada hadasa har lokacin bacci,

kwance yake saman makeken gadon sa yana waya kasa Kasa yake magana" to kwana daya zakiyi ya isa allah ya kaimu goben mu kwana lfy dif ya kashe wayar ya gyra kwanciyarsa da Adu'a a bakinsa bai jimaba bacci ya daukesa,

**********
yau tin safe ta kama hanyar gun boka sani anjima gidansu ba hanyar fita yauma kamar jiya suka Kari masha,arsu ya jadada mata goba ne karshe tayi qokari tazo haka ta baro wajan boka makasheta zuciyarta fari tass,

Yau kam estate family bagaiyya cike take da tin safe sai shigi da fice ake mataye masu aure duk suna nan da iyalinsu , Ramlat tin safe ta rangada kwaliya anci make-up sai kace wace zata gasar kyau part din kawu ibraheem ta tafi,

ba kowa sai haleema itama ta gama shirinta tsaki tayi ta nufi part din kawu munnir su safna sun gama shiri " wow gaskiya sister kin yi kyau susai hararata tayi abdullateef ne ya shigo " my brother zaka fitane kallonta yayi " ina zakije " please ka fita dani wlh wancan mugu ya sakamin ta kunkumi ko naje bazu barni na fitaba sakone zan kai murmushi yayi

" wlh sister ba ruwana tsaki tayi tana turo baki safna ta kama hannuta suka fito " muje za amso dinkina wanda zan zaka bayan daurin aure suna fitowa babbar harabar gidan zasu Shiga mota Ramlat sai farin ciki ta ke yau zata wataya dan yau tayi niyar nemo khaleel dinta suci karansu babu babaka safna tashiga mazaunin driver ta wa motar key tana zuwa dede get motar Abdallah na shigowa har zaa bude mata get,

kuma sai aka rufe hantar cikin safna sai da ta Kada " sister kin jamin wlh sun gano kina motar duk akwai duhun Gilles tsawa wani soja ya Daka musu suka " fito cikeda tsoro sai matsar ido suke, Ramlat ta kai kallonta gun motar da Abdallah yake gani tayi wata zafgigiyar budurwa kyakyawa fara tass da ita ta fito fuskata dauke da murmushi da kuma wata mai kamarta saide wacan tafita kyau, " ku huce muje oga na kiranku Ramlat gabanta sai faduwa

yake har suka karaso inda suke safna ta gaisheshi bai amsaba" ke gidan ubanwa zaku kenan kece zaki karya dokata kifitar da wanan tantiriyar waje ko " dan allah brother kayi hakuri wlh ban saniba nace ta rakani amsar dinki Rumaisa kallansu take saboda taga tsantsar kamar sojanta da Ramlat murmushi tayi " my soja amusu afuwa " wuce maza ki maso dinki ke kuma ki guji haduwata dake anjima ban mance sauran hukuncin kiba maza huce ki kaisu wanan anty rahama ciki. Rawar jiki ta wuce suna binta Rumaisa tace" kanwarmu ba sannu da zuwama jitayi kamar ta kasheta saboda haushinta banza ta mata taki kaita part dinsu direct part din yinma ta kaisu daga kofa ta tsaya ta nuna musu da hannu tayi gaba abinta turiss sukayi kamar daga Sama sai ga Naseer ya kallesu " yadai bayin allah ku Shiga mana" nane part din anty rahma

" ba nan bane ko zo muje ya gaba suna biye dashi har parlour " anty kinyi baki da faraarta ta tarbesu dan ya kirata yanzu yace ta kaisu wanan yinma koda zuwa bayan daurin aurene " ku zauna zama sukayi suka gaisheta cikin girmamawa

Kayan motsa baki ta kawo masu " kuyi hakuri gidan yau cike yake da jama'a Ramlat ce ta shigo turiss tayi da ta gansu a parlour su amma sai tayi kamar bata gansuba zata wuce rahama ta maidota " ke kushiga cikin parlour ki inda ba hayaniya,

My dota kutashi kushiga ciki ku huta Kafin ajima mike'wa sukayi suna bite da ita suka shigo zama sukayi akujeru kallon Rumaisa tayi " ke kuma baiwar allah meye hadinki da wanan mugun sojan cikin Sauri Rumaisa ta kalli Ramlat " ban ganeba mugu " eh wlh da kinsa ko shi waye da kuma halinsa da ko darma miki shi akayi akafa bazaki jamaba kenan tanan ya bullo saboda kaf Abuja da kauyanta ya zagaye yarasa matar aure shine ya koma kaduna arashin sani kekuma kin fada tabkin sonsa ki hawaye ta fara wlh na tausaya miki, keda iyayanki mike'wa Rumaisa tayi jikinta na rawa ta nufo Ramlat ta riketa " ke kanwarsa ce nasan bazaki fadi abinda ba daide ba please gayamin menene matsalar Abdallah na fisgewa tayi tana hararata " ina so na ceceki kuma kina nema fadawa halaka" to naji gayamin tuni kuka ya kwacewa Rumaisa saboda rabuwa da soja a wanan lokacin zai mata wahala " to aabinda baki saniba shide wanan sojan da kike ganinsa to fa..... ✍🏼

Daga Al'kalamin
Rahma ummu fareesa😘

R luv ce😍🥰😘

✍🏼✍🏼✍🏼
‍♀HATSABIBIYAH🤷🏻‍♀
💖💖RAMLAT💖💖
Chapter 8 · 0% Book details