← Book details Hatsabibiya Ramlat Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 106 OF 152

Sashe 106

Hatsabibiya Ramlat Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 7 min read

suna zuwa yana fitowa daga mota ya rika taku cikeda kuzari gaisheshi aka fara yarika gaisawa da jama'a ana masa sannu da zuwa da barka da kama Garba tanko bata gari da kuma barikin sojoji amunafurce da ya samu nasarar yi yana amsawa kai tsaye Office dinsa ya bude ya shiga kamshi kamar yananan ashare agoge Tass gilashin idanusa ya cire ya kunna Ac ya zauna saman lumtsumemiyar kujera ya kunna Laptop ya kunna sigari yana zuka yana fitar da hayaki baki da hanci yana danna waya ya kira aka hado masa coffee yanasha yana aiki a Laptop yakai awa daya yana aiki yasha sigari takai hudu kashe Laptop din yayi ya janyo wasu takardu yana rubutu yaji ana k'iran sallah hadadiyar agogon

hannusa ya kalla yaga karfe daya da rabi mik'ewa yayi ya kashe Ac yana daukar wayarsa tana daukan ringing yanaga jawace ya daga"my jawa zan kiraki zan shiga masallaci ki shafamun kan little Ramlat ya tsinke K'iran Kenan akayi knonking tsaki yaja " ya nufi kofar ya bude Sara masa yayi yallabai dama yar gidan Géneral Garba ta matsa sai ta ganka face ya hade " me na gaya muku yau ai ba ranar aiki bace ban gama hutawaba tsareshi tayi da idanu kamar ta cinyeshi ta marerece shi baima san tanayiba dan bai kalli ko bangaran da takeba duk da ya mata mugun kwarjini haka na daure nakirasa" Captain Abdallah Bagaiyyah dan Allah ka temakeni ka saurareni 5mnt ya isa bai kalletaba yace" OK zaki iya jira naje nayi ibada na dawo saboda darajar kin hadani da Allah kofar ya murzawa key yaje yayi Alwalla ya tafi masallaci

murmushi tayi " agaskiya Guy Dinan ya hadu ba karya wlh najima ina sonsa amma wanan bazai hana na dauki fansar abunda yama mahaifina ba ina cikin tunani har ya dawo bai kalletaba yace" zaki iya shigowa ya bude kofar ya shiga yaje ya zauna yaji dame tazo da sallama na shigo ya amsa bata banjira ya min tayin abin zama ba na zauna tana turo kirji wani shegen dinki ne ajikina kallonta yayi fuskarsa babu walwala yaga ta tsareshi da idanu tsaki yaja dan shi kyanta baya gabansa tunda ko kafar Matansa bata kamoba " malama kiyi magana inada abunyi. Numfasawa nayi duk da kwarjininsa na daure nace " Wlh sonka nake kuma na amince kayi duk yada kaso kayi dani murmushi gefen baki yayi takaici fall zuciyasa itako ganin kamar ya aminta ta Mike tanufo gunsa tana kukan karya tayi kansa nufinta ta fado jikinsa har tayi nasara dora hannuta kafadarsa yasa kafa ya tabeta ta fadi wanwar kasa ya Mike tsaye yasa

Hannusa ya dagota ya kifa mata mari yana shake da wuyanta ya fisge mayafinta sai ga gontuwar camara ta fado ya ingijeta ta fadi ya dauki camara yasa aljihu kuka take wiwi " dan ubanki ni lusarin namiji da zaki sameni da sauki kinsan irin matan da na baro gidana to ko yar wanke wankesu bazan daukekiba bare ki hada jiki dani yawu ya zubar wato kun hada baki da mahaifinki ku kullamun shairi ko tashi kibani guri mikewa tayi tana rusa kuka ta fice da gudu don tsoransa ya kamata dan ita har ga Allah sonsa take da zuciya daya tsaki yaja ransa abace ya kwashe wayoyinsa ya fito

Kana kallonsa kasan ransa abace yake ana masa magana hannu kawai yake dagawa ya shige mota driver yaje suka tafi kai tsaye inda aka kai Garba aka rufe yace akai,shi suna zuwa ya dinfari gunsa yana murmushi yana tafa hannu yacire camara ya nuna masa idanu ya zaro " wlh taku ba ta Allah kuma da naso zanyi yada naso da ita wlh ko da ta dauka da kanta zata goge to wanan harakar bata gabana kayi duk abinda zakayi Allah na tare dani kajira nan da kwana biyu na hada duk wasu manya manyan laifukanka za'a shigar dakai kotu ayankema hukunci dede da kai ya cilla masa caméra kasa akanka Abdallah zuciyarsa daya yana aiki da gaskiya bazaka iya cinmasaba Inde kana nufinsa da shairi ya fice ya barsa da cizon yatsa " wlh sai naga bayanka ya fada yana dafe kansa, direct Soja gidansa ya Nufa, Ramlat bata tashiba sai karfe biyu tayi wanka tayi sallah taci abinci Soja ya kirata sukasha hira tana zuba masa shagwaba har karfe uku kafin ya tsinke Kiran jawa na masa mita kanta na ciwo ya shiga lallabata yana shafa mata kanta, Ramlat suna

gama waya da soja ta tashi ta tafi part din Safna tana bata labarin tunda aka kawota Aminu bai ko kalletaba bare ya kusanceta ita ta gaji gwara araba auran hakuri ta bata " hakan yayi daide haba safna kamar ba mace ki sauya ayau nakeso ki sauya yanzu kin jiga kirika shigar kananu kaya yada zakisha kasan kirika shiga wada bakida maraba da tsirara kuma duk irin kwanciyar da nabaki salonsa to ayau idan ya shigo hannu gobe ki kirani kimun bayani murmushi tayi" nagode el uwata Allah ya sabkeki lafiya mikewa tayi " ni natafi gun mummy yau ban gantaba har kofa ta rakota ta koma tayi hadin gujiya zalla da madara tasha
Ramlat saida ta biya part din dada sukasha hira da mai ran karfe da Dada saida aka kira sallah la'asar ta tafi part d'insu tayi sallah suna zaune ita da mummy tana saita yarta a hanya da mata nasiyya zaman duniya akan tama yar uwata uzuri shaidan ne keson hadasu wlh tasan Jawa yarinyar kirkice to kawa Ramlat tabita dashi tayi kwanciyata mummy na danna mata jikinta, affan na musu dariya yada Rufaida take turo. Ramlat daga jikin mummy " Allah ina ragama yarki darajar kamar da muke " karki raga mata to tasani na fasa tausar " yi hakuri mummy na murmushi tayi taci gaba da tausa mata jikinta,

****************************************

Da misalin karfe 8:00 pm na dare safna ta hade cikin wani shegen mitsi tsin wando ko rabin cinyata bai kaiba rigama guntuwace tana ba yarta nono ya shigo dama da ganga ta zaune kujera bakin kofa yada zai ganta aikuwa yana ganinta saida yawunsa ya tsinke dama haka take wucewa yayi baiyi minti biyuba ya fito ya kuma dawowa tashi tayi tsaye kamar tana jijiga yarta shiga yake yana fita yafi ya tsaya " ke nan ba gidan yawo tsirara wlh karna dawo naganki haka ya fice sau kusan goma yayi ko kallo bai ishetaba dariya yabata sosai amma ta danne ta shige bedroom dinta " yau zakazo hannu,

Karfe tara Soja yazo ya dauki Ramlat suka tafi gida suna shigowa parlo Jawa ta tare su da gudu ta rungume Ramlat " my love nayi missing dinki dariya Soja yayi ya barsu agun ya tafi yayi zamansa " nima Nayi missing dinki my jawa sakinta tayi ta kamo hannuta suka karasu gun soja " my love muje kuci abinci " ni nakoshi Antina ta cikamun cikina " to kefa " wlh nima na koshi ina babyna " tayi bacci zama Jawa tayi kusan Abdallah " my love wlh hajijiya nakeji " My love hajijiya kuma hannusa ya Dora kanta kanki babu zafi ganin yada jawa take son rabuwa jikinsa yasa Ramlat ta zauna gefansa ta kwanta jikinsa ta lumshe idanu cikin shagwaba tace" My Heart bacci nakeji " na kaiki ki kwanta kai ta daga OK tashi mutafi ya dagata jawa tace" wanan jaraba dame tayi kama mikewa yayi ya kama hannuta ta fisge ta saka masa kuka rikota yayi ta rungmeshi my baby " menene kuma yi shiru" ni ka goyani bazan iya tafiyaba yarasa ya zaiyi yauni jawa yakeji gashi baya jure kukan Ramlat hannuta ya kama suna karya kwana ya dauketa ya

goyata ya haye sama da ita bai tsaya ko inaba sai cikin bedroom dinsa ya wuce bathroom ya hada ruwa ya sabkota ya cire mata kayan jikinta yamata wanka ya nadota a towel ya fito da ita ya zauna bakin gado yana rungume da ita sai turo baki take " my baby laifin me nayi kanta ta tura kirjinsa jikinta ya goge mata ya zaunar da ita ya yashfeta da mai yazabo Riga bacci irin wada take bari dakinsa yasa mata ya kwantar da ita yarufe da blanket" Yayana" yi shiru bani minti biyar kasa ya koma yama jawa sallama da kuka suka rabu tana tamasa kuka zatayi kewarsa lallabata yayi da kalamai masu dadi ya dawo sama yashiga bathroom yayi wanka ya shirts cikin kayan bacci ya fesa turaren da Ramlat tafi so
Chapter 106 · 0% Book details