← Book details Hatsabibiya Ramlat Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 149 OF 152

Sashe 149

Hatsabibiya Ramlat Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

...."haba Soja kuyi hakuri kai kana kuka ya za'ayi kanwarka ta samu nutsuwa tunda kaine mai lallashinta to kaima kuka kakeyi zama tayi ta janyo Ramlat jikinta ta rungumeta mai ran karfe ya zauna ya rungume Soja suna lallashinsu da kalamai masu dadi da ratsa zuciya da jadadda musu ba'a fushi fah da ikon Allah sun jima sunayi musu nasiyya har sukayi shiru suna samun nutsuwa Dr ne ya shigo da sallama yana gaishesu Dada ta janye Ramlat daga jikinta Dr ya dubata" Alhmdllh bata da wata Matsala yanzu amma tabar yawan damuwa dan jiya jininta ya hau amma yanzu da dan dama godiya su Abbie sukayi masa ya basu sallama Soja ya Saki mai ran karfe ya shiga toilet ya wanko fuskarshi ya fito Ramlat taje ta wanke fuskarta tazo Dada tace" to sai mutafi gida ko hijab Soja ya ba Ramlat ta saka tana kallonsa kai ya girgiza mata gun yinma ta tafi ta rungumeta " dotana sannu kinji Allah ya bamu hakuri mu duka kai ta daga ta Saki yinma ta rungume Maimuna muryata na rawa tace" momyna Allah ya bamu hakuri " Ameen dota hakuri yazama Dole Abbie yace" sai su tafi

Soja ya matso kusan yinma little Ramlat ta sunto abayanta tabashi dan ta gane nufinsa ya amsheta ya rungumeta Abubakar ya matso kusansa ya rike hannusa daya " my brother ayi ta hakuri kansa ya daga Ramlat taje ta rike hannu mummy suka fito gaba dayansu suka dunguma harabar hospital Din motoci biyune suka shiga sai gidan Suka tafi jama'a ba laifi rumfonan harabar gidan duk da yan zama tunda ba'ayi sadakar sati ba sojojinsu duk suna zaune ya nufi gunsu ya dan Saki fuska suka gagaisa su Abbie zama sukayi Su yinma suka shige ciki parlon cike yake da jama'a anata musu sannu da zuwa yinma ta kama hannu Ramlat ta zaunar da ita itama ta zauna ta jinginata jikinta tana shaffah kanta tana mata kwantar mata da hankali su jameela ne dasu shaffah kusan su biyar suka dawo kusan Ramlat suka zauna suna mata gaisu ta amsa tana jikin yinma kwance yinma ta kalli Shaffah " kawo jawahir abata nono tashi tayi ta daukota takawota

Yinma ta amsheta" dota tashi ki shayar da yaranki kinji tashi zaune tayi" yinma kawo babyna na fara shayar da ita" dota ya zaki iya shayar da rai hudu kiyi hakuri yau kwana hudu har ta manta nono tanacin abunci tanashan madara bata rigima maimunatu zata amsheta da zaran tayi dan wayo yaranki sun warware suna tafiya za'a dawo miki da ita kinji kuka ta fara " wlh yinma baza'a rabani da yata ba nono bai ishetaba zan shayar dasu dukansu " to yi shiru little Ramlat ta bata ta amsheta ta rungumeta ta sakata hijabi tana shayar da ita baiwar Allah sosai takeshan nono saida ta koshi tana cizonta ta cireta tana gefenta ta mashi jawahir tana shayar da ita Ramlat ko wasanta takeyi saida mutane dayawa ta sasu kuka Ramlat daurewa kawai takeyi har tagama shayar da yaranta dukan su ta rungume gam little Ramlat ce gaba har tayi bacci Ramlat ta kalli hadeeza " Anty rikemun su mushiga cikin biyu ta dauka Nabeela ta dauki daya Ramlat na rungume da little Ramlat suka shiga cikin d'aki saman

gado suka shimfidesu ta kwantar da little Ramlat ta haye gadon ta rungume yaran tana kuka sunyi ta bata hakuri takiyin shiru Nabeela ta kirawo mummy tazo itama ta sigar lallashi tabi da ita har zuciyarta tayi sanyi kanta cinyar mummy har tayi bacci mummy ta janyeta cike da tausayin ace yarinya kamar Ramlat zata shayar da yara hudu gyara mata kwanciyar tayi ta dauki jawahir dan bata bacci sai tsotsar yatsa parlo ta fito ta zauna sukaci gaba da jimami Ana hira sama sama, to haka de aka wuni har dare Soja ya dan sake cikin jama'a saboda baqin da yake samu Dole tasa yake cin abunci cikin yan uwansa

Da dare kowa ya nemun ma,kwancinsa Soja shida Abubakar suka kwanta dan ya debe masa kewa su mummy sun tafi gida amma yinma tananan gin Ramlat da sauran jama'a yaran mata kuwa kowa ya tafi gidansa yinma na tare da Ramlat da Dada saboda kama mata yaran yinma kuwa dan ta kwantar mata da hankali sun samu taci abunci kafin su kwanta Soja yana cikin tunanin duniya Ashe ba matabbata baceba har bacci ya kwashesa Abubakar shi dama yajima da bacci

****************************************
*bayan sadakar bakwai*

Zuwa yanzu jama'a sun tsagaita tun jiya da akayi sadakar bakwai saboda yawan nasiyya da, kulawa da su Ramlat da Soja suke samu sun rage damuwa sun danyi hira da mutane misalin karfe 8:00pm na dare angama shirya kayan su Ramlat tafiya gida Soja ya cema yinma shima gida zai koma ta hana tana kwantar masa da hankali Ramlat tana kuka suka tafi dan tana tausayin Soja batason barinsa, Dole ce tasa, Rayuwa Kenan haka suka tafi yinma tace Abubakar ya zauna dashi kafin yabar gari, part dinsu yinma ta kaita dan tasan Dole mahaifiyarta na bukatarta harda Ancim akazo, washe gari tun Asubah mummy ta hadawa Ramlat ruwan wanka taje ta tado da kanta tayi mata dan tasan kwananan yarta

bata samun wankan ruwan zafi sosai ta wanketa da gasta sosai aikuwa tana kwanci sai bacci mai dadi duk ciwon jikin da takeji babu sosai take bacci har mummy tayiwa yaran wanka daya bayan daya ta shiryasu ta kawosu ta kwantar gaban Ramlat ta fice girkin breakfast sai kusan tara mummy ta shigo d'akin" ke Ramlat tashi tana bubbuga cinyarta idanu ta bude da Addu'a dauke bakinta ta kalli mummy " mummy ina kwana " lfy kalau ya karfin jiki.?" Alhmdllh" tashi maza kafin yaran su motsa kiyi breakfast mik'ewa tayi ta sabko ta shiga bathroom ta wanko bakinta da fuskarta ta fito ta kalli yaran suka bacci sukeyi parlo ta fito papi na zaune ya gama breakfast " papi ina kwana " hassana ya jiki? " Alhmdllh papi" to maza aje ayi breakfast kan dining ta nufa ta zauna bata wani ci abun kirkiba Ashe mummy na Lura da ita tazo ta tisata gaba saida ta cika cikinta ta barta parlo ta dawo ta zauna papi na kara mata nasiyya da Abbie da yinma suka shigo da sallama Ramlat ta Mike,

Ta rungume yinma tana gaisheta" dotana ya karfin jikinki? " Alhmdllh hannuta taja suka zauna" Abbie ina kwana? " sai yanzu banyan kin gama gaisawa da mamarki shiru tayi kanta ak'asa " to ya jiki? Alhmdllh nasiyya sukayi ta mata mai ratsa zuciya suna lallashinta har tasaki jikinta suna hira saida sukaji kukan little Ramlat ta farka mik'ewa tayi da gudu tashiga d'akin" babyna kin tashi daukarta tayi ta zauna bakin gado ta janye rigarta tana shayar da ita tana hawaye harda shashekar kuka har ta koshi wayarta ta dauka ta kira Soja tanata ringing ba'a dagaba tana dabda tsinkewa aka daga sallama yayi mata" yayana ina kwana? "Baby kin tashi lfy ya jikinki.? "Alhmdllh yayana kaci abunci kuwa " eh naci baby ina yarana? " duk suna lfy bacci sukeyi sai babyna kade " ki gaisheta anjima zan shigo zuwa dare saboda ana zuwar mini gaisuwa kinji kici abunci " to naji bey" bey zan kiraki kinji baby" naji yayana na tsinke Kiran ina hawaye fuskata na goge na fito parlo kena yaran suka farka Ancim ta jidosu daya bayan daya na shayar dasu babyna na wasanta

***
Haka muka yini rai babu dadi danma mummy na qoqrinta har na saki jikina dadare bayan sallah isha Soja sukazo shi da Abubakar sun jima part din yinma suna tayi masa nasiyya yajita susa ya dan saki ransa tareda Abubakar din suka zo part d'inmu muna parlo suka shigo da sallama mummy ta amsa cikin sakin fuska suka gaishe" Abdallah ayi ta hakuri " babu komai Aunty babu maija da ikon Allah kallona kawai nakeyi cike da tausayinsa " Ya Abdallah ina yini " sannu ya karfin jikinki? " Alhmdllh " au ni bazaki gaisheni ba " yi hakuri brother ykk ina Lagos " Alhmdllh yaran ta kawo masa daya bayan daya ya musu Addu'a sun jima susai sukayi musu sallama mummy tace" tashiman ki rakasu Ramlat ta miki da hijab dama ajikinta ta biyosu Abubakar yayi gaba da gudu ta iso ta fada kirjin Soja ta saki kuka rungumeta yayi yana sabke ajiyar zuciya yana buga bayanta k'asa yayi da murya" my angel please kiyi hakuri kinji bari kukan muyi tayi mata Addu'a kinji baby kai ta daga ya kamo fuskarta ya goge mata hawayen ya lallasheta hannuta ya kamo ya maidota har kofar parlo " Yayana kaima karkayi kuka kaji murmushi ya k'akalo " baby bazanyi ba kinji kai ta daga kiss ya sakar mata agoshi ta shige cikin parlon ya juya
ya tafiyasa tana shiga parlo ta iske jawa na kuka ta zauna ta shayar da ita suna hira da mummy har papi yazo sukaci GABA duk dan susata nishadi sai wucin shadayan dare sukayi slm kowa ya nemi gun kwanciya Ramlat ta gama shirin kwanciya ta rungume yaranta hudu little Ramlat ce agabanta ta tofesu da Addu'a bata jimaba barci yayi awon GABA da ita Ancim nada ga k'asa saman katifarta akwance itama sai baccin suke shararawa

****************************************

*Agurguje bayan wata biyu*

har wannan lokacin Ramlat da Soja jawa na ransu sai de sun hakura da kuka sun fawalawa Allah komai Ramlat ta zubar da wanka yaranta sun warware sosai idan ka Gansu zaka zaci sunkai wata hudu da haihuwa sun samu kulawar mummy Ramlat ta murmure tayi jiki kadan fatarta na sheki saboda gyaran da mummy takeyi mata little Ramlat na samun kulawar Ramlat fiye da tunani me tunani yarinyar tayi mul mul da ita tana tafiarta ko ina tunda dama kafin mutuwar jawahir tana tsayuwa idan ta rike Abu Soja yanzu ya dan sake ya koma bakin aikinsa yanzu haka baya gari yau satinsa ukku Kenan yinma ta karo yan aiki biyu daya su gamu da Ancim surika ma Ramlat Reno daya ta hadu da inna talatu surika aiki tare
Chapter 149 · 0% Book details