← Book details Hatsabibiya Ramlat Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 127 OF 152

Sashe 127

Hatsabibiya Ramlat Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

da misalin karfe shida na yamma Ramlat na zaune a parlo tana kallon Tv taji shawar indomie ta kwalawa Ancim kira taji shiru mikewa tayi ta nufi kitchen ta isko suna cikin aiki suna hira inna talatu na yada abunci " oh ni Ramlat Ancim ina ta kira shiru ba amsa " lah Aunti yi hakuri hira kayan dariya muke banjiba me kikeso " indomie nakeso bari na dafa inna talatu tace" bari adafa miki Ramlatu yarinya kirki dariya tayi " to nagode innata Allah barmu tare " amin inna ta fice ta dawo parlo ta zauna jawa ce ta fito little Ramlat a hannuta ta karaso gun Ramlat ta zauna Ramlat ta dauki little Ramlat ta rungume " babyna kinga dadynki yayi nisa tun safe ya tafi Kaduna har yanzu bai isoba ni gaskiya na damu dariya jawa tayi Ramlat ta kalleta dan kwana biyu da Ramlat batada lfy sun dan shirya sama sama shagwab'ewa Ramlat " to meye na dariya dan nayi missing d'in yayana " to ai Dole inyi dariya saikace idan yazo tare zaku kwana " wlh ke wanan yake gabanki baniba ni akullum naganshi cikin kwanciyar hankali da koshin lfy yafimun komai" to ya isa ni wasa nakemuki banza tayi da ita taci gaba da ma babynta wasa har Ancim ta kawo mata indomie ta jawa taba little Ramlat ta fara cin abinta afakai ce jawa take hararanta Ashe Ramlat na lure da ita murmushi tayi tace" Allah kuwa saide hararar ehe tsaki jawa tayi" wlh kefa my love kin cika neman jaraba to wa ya harareki yanzu banza ta mata aranta tace jaraba akasa taci indomienta tayi Ket ana Kiran sallah magrib aka fara Mik'ewa Ramlat tayi ta amshi little Ramlat ta Haye sama jawa ta Mike ta shige d'aka tasha had'e hadenta tashige bathroom tayi wanka ta dauro Alwalla Soja lokacin da ake Kiran sallah ya shigo gidan ya tsaya magana awayane ana harabar gidan yayi Alwalla ya tafi masallaci

Ramlat ma tana zuwa wanka tayi ta dauro Alwalla tayi sallah little Ramlat ta fara kuka tana gamawa ta dauketa tayi shiru tana zaune bata fito tana zizigata tayi bacci lokacin an kira isha ta kwantar da ita tayi sallah

ta danyi kwalliya tasaka Riga doguwa mai bin jiki batada hannuwa ta dauki little Ramlat ta sabko kasa a parlo tayi zamanta rungume da ita tasan yanzu jawa ta fito Ashe Soja yana cikin d'kinsa yazo Ramlat sai baza hanci takeyi dan taji kamshin turaresa kofar d'akin ta kalla arufe bazata iya ganewaba sanin ba itace ke dashiba yasa bata tashiba shiko yana ciki wanka yayi saka gajeran wando agadauce dan rabinsa da abinci tun safe shi yanzu coffee ne yake marmari jiyama bai shaba ya dauki wayarsa zai fita aka kirasa ganin Sadeeq ne yasa ya daga ya kara akunne ya koma ya zauna suna magana dede saitin CC TV Camera ya zauna yana kallon Ramlat sai kallon kofar d'akinsa take tana turo baki murmushi yayi sukaci gaba da hira da Sadeeq sun jima sosai kafin suyi slm cigaba yayi da kallonta duk ta damu sai turo baki takeyi ita daya mik'ewa yayi yazo saitin camera yaji yana shawar kallo yaga yada tayi lokacin da bayanan

sosai ya maido komai baya tsaki yaja ganin ya wuce daya yanayin gabane yaga jawa ita da kausar zaune cikin d'akinsa kamar ma ranar sunah murmushi ya saka magana yanaji tiryan tiryan abinda take

fadawa kausar muguwar tsanar da tawa Ramlat saboda shi zuface ke keto masa ta ko ina dayaji tana cewa sai ta rabashi da Ramlat ko ta wani hali cikin rawar jiki ya Mike yana tunani da karfi yace" Kenan Ramlat wanan abunne taji ranar sunah har zazzabi ya kusa kashemun ita harya fita ya nufa ya bude kofar da karfi ya fito parlo ransa amutikar bace Ramlat tana ganinsa ta Mike ai ganin yanayinsa yasa taja da baya gunta ya nufo " ke zo zan tambayeki wlh idan baki gayamun gaskiya sai nayi mugun saba miki jikinta na rawa tazo gabansa ta tsaya " yayana gani yi hakuri" ranar sunah little Ramlat a dakina me kikaji jawa na fadi akanki kai ta girgiza tsawa ya daka mata ta fashe da kuka " dan Allah yayana kayi hakuri batace mun komaiba " ni sa'an kiné zakimun karya damkota yayi ya nufi dakinsa da ita ya kunna mata komai ta gani little Ramlat ta shimfide ta rungumeshi ta baya tana kuka baice mata komaiba komai ya tuna naga yanata bincike

saime jawace a kijin tana dubé dubé ta fito ta nufi dining ta sinto wasu kwayoyin magani ta zuba cikin abunci da ruwan zafin tea ta mayar da magani jikinta tana murmushi tana cewa yau cikin sai ya fita wlh gaba yayi yaga inda sukayi breakfast shida Ramlat da fitarsa da komawa da Ramlat tayi sama gashinan bata sabkoba sai zauwarsa da jawa takece masa ta sabko tasha magani duk babu gurin sai fitowarsa da Ramlat babu rai da inda jawa ta taresa tana gaya masa karya yana fita tahau murna duk ilahirin jikin soja rawa yake idanusa sunyi jawur zuciyasa tayi bakinkirin Ramlat ta sakeshi cikeda tsoron abunda ta gani ita kanta karkarwa take jikinta na tsuma ta fashe da kuka ta dawo gaban soja ta fada saman faffadan k'irjinsa ta rungumeshi gam tana wani irin kuka " wayyo yayana Abdallah bazamu rabuba insha Allah sai na haifoma danka idan narabu dakai wallahi mutuwa zanyi sonka yakai matakin a rasaka rasa rainane kara rungumeshi tayi gam gam tana kuka kamar ranta zai fita janyeta yayi jikinsa yana kallonta hannuta ya kamo ya

kaita bakin gado ya zaunar da ita " Ashe ni inacan ina yawon ceton rayukan Al'ummah musulmai da sayar da nawan ran da nemo muku abinda zakuci ko kunsa yada natsallake rijiya da baibai awanan fitar da nayi cikin tsawa yace mata satinku nawa kuna kirana baku samuna cikin rawar murya duk ta tsorata da Soja tace " sati..! Ukku..? " gud amma shine ban saniba Ashe gidana ya kama da wuta yanaci balbal banida lbr saboda tsananin yarda da nayi daku wlh ban tab'a tsayawa na duba CC TV Camerorin gidana ba sanin yan uwane masu hadin kai da kaunar juna Ashe kishi ya wuce tunanin mai tunani gashi saboda sake har za'a mun kisankai agidana amma saboda tsabar munafurci ba'a nunawa agabana yada zan gane wlh dani kuke zancan duk maganar dayake cikin fushi yake maganar idanusa yayi jajur kamar gauta ya nufi kofar fita cikin kuka ta Mike dagudu tana kiransa Yayana Abdallah kafin ta Iso gunsa" tsawa ya daka mata ya bugi bango saida hannu ya gwalje kirjinsa sai sama da kasa yake cikin sauri cike da tsoro ta kamo ta hau gadonsa tayi kwance ta rungume little Ramlat tana kallonsa tana shashekar kuka zabga mata harara yayi" ke wlh Ramlat kiyimun shiru ki hadiye kukanki ki zauna inda na ajeki ina zuwa ban yada ki fitoba ko kofar parlo kijirani wlh idan kika kuskura kika fito Hamm yaciza lips d'insa yana hararata yace ilove you Ramlat ya fada ya fice daga bedroom d'in fuskarsa idan kakallesa akacema ya taba dariya aduniya zakayi musu ya rufo kofar parlo babba ya fito jawa batanan hamdala yayi dama bayaso yan aiki su Gansu ko su jisu ko aga wasan da zai buga yanzu cikin wani

irin taku na karfafan maza ya dunfari hanyar inda jawa take saboda yanayin bacin rai har tangadi yakeyi dama ya dan boye damuwar sane saboda yada yaga hankalin Ramlat atashe kar cikinta ya samu matsala d'akin jawa ya banka kofar ya shiga bata parlo ya nufi bedroom d'inta tayi dare dare saman gado tana magana " wlh sai na tarwatsa musu zama natsaneta bana ko son ganinta kuma cikin sai na salwantar dashi ai bata kai karshen maganarba taji wata Irin shaka anma wuyanta cikin wata razanar nan tsawa yace" cikin nawa zaki salwantar mun bayan kinyi kokarin kashemun mata da diyan da suke cikinta Allah baibaki sa'aba shine yanzu kike shirya yada zaki kasheta ita da abun cikinta wlh jawa kinci Amanar yan uwantaka kinci amanar kaunar da take tsakanina dake nasoki tsakanina da Allah nabaki wani matsayi cikin zuciyata mai girman gaske ashe kinacan kina hadamun gobara agida wlh daga kanki nashiga tsoron mace mai shiru shiru ladabinki Ashe na banzane kin bata rawarki da tsalle natsaneki jawa bani bake dama can ba sona ba kike natsani mutum mai fuska biyu baki ta bude zatayi magana wasu mahaukatan tagwayan mari dama da hagun yarika zuba mata bakinta tuni ya fashe jini na fita hardaga hanci ga shakar da ya mata ko numfashin kirki batayi da wata irin murya mai cike da tsantsar bacin rai taji Soja na kalmar da ta firgitata cikinta ya wuntsula kallo daya tamasa Wanda bata fatan koda ta rayu ta sake ganinsa da irin wanna kamanin atake cikinta ya sake murda kawai sai taji zawo da fitsari anan take suna zubowa daga kasanta babu kakautawa... ✍🏻

😭🤲🏻Ya Allah kasa mufi karfin zuciyarmu Allah karabamu da aikin da nasani Allah kasa mufi karfin shedan la'anane Allah kishi masifane idan ka biyema kishi wlh zai kaika ya baroka Allah karabu da zafin kishi Ameen

Rahma ce ummu Fareesa😘

✍🏻✍🏻✍🏻

*🤷🏻‍♀HATSABIBIYA🤷🏻‍♀*
*💖💖RAMLAT💖💖*

*_🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION_*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

Story & Written by
✍🏻
Real Ladingo😉
yar mutan Niger🇳🇪

*👏🏻👏🏻👏🏻DON GIRMAN ALLAH KARKUMANTA DA GIRMAN ALKAWARI DA AMANA KARKU FITARMUN DA BOOK WAJE KUKARANTA KYAUTA RUWAN ALLAH AMMA ARIKE AMANA👏🏻👏🏻👏🏻*

*Bismillahir Rahamanir Raheem*

*Book 2* 🅿👉🏻3⃣9⃣&4⃣0⃣
Chapter 127 · 0% Book details