← Book details Hatsabibiya Ramlat Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 138 OF 152

Sashe 138

Hatsabibiya Ramlat Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

ta rarafo tazo tana Jan rigar Ramlat sakin jawa tayi ta dauketa " oh baby kinga k'ananki ya hanani kula dake dariya jawa tayi " aikuwa kwa karata uwa da yarta hira sukaci gaba dayi Ramlat ta kira Ancim tace akara abunci anasu ba na sojoji ba ayi kirki mai dadi sunada baki jawa tace bari taje ta kama musu,aiki ta Mike ta tafi kitchen Ramlat tana zaune suna kallo ita da baby, Soja suna fita gidansu yace a kaishi suna isa ya shiga part d'in yinma tana zaune a parlo ya shigo ya gaisheta " Abdallah ya masu jiki kusanta ya zauna " yinma da sauki ina kwana " lfy kalau ya dotana " tana lfy sai rigima " ai Dole baiwar Allah wayarsa ce ta dauki rururi ya ya cirota yana duba yaga habeeb ne yayi picking ya Kara kunnesa " hello habeeb ykk " Alhmdllh yanzu Soja rashin mutumcinka ya kai nayi rasjin lafiya ba ko dubiya " Ya Salaam kayi hakuri wlh kaina achaje yake sai hakuri yanzu kana ina "ban saniba d'an rainin hankali " please Abokina fadaman yanzu zan fits gun aiki zan biya " OK ina gida " ok ganinan ya kashe kiran ya kalli yinma " Yinma zan wuce kiss ya mata agoshi ya Mike " kai dawa kuke waya " yinma habeeb ne abokina bayada lfy " ayya Allah ya nashi lfy ai muma baka kyauta manaba akayi auransa ko ka gaiyacemu dariya Soja yayi " yinma ayi hakuri wlh rashin wadataccen zama agarine yake hanani sakewa da kowa yinmata natafi " Allah ya kiyayeka da kiyayewasa Abdullahi " Ameen uwata ya fada yana ficewa daga parlon

yana fita kai tsaye gidan habeeb ya nufa suna zuwa yakirasa yana kofar. gida ya giyo yamasa iso har cikin parlonsa da sallama ya shigo Jiddah ta amsa zaman sukayi suka gaisa " Amarya ayimun afuwa wlh banida isashan lokaci murmushi tayi " wlh babu komai Allah ya taimaka ina su Ramlat " suna lfy to kai kace bakada lfy kasa na biyo amma na ganga ras murmushi yayi " Abdallah ceton rai zakayi wlh yarinya ta kamu da ciwon sonka dayawa kusan so ukku Ana kwantar da ita asibiti kasan fah kawar jiddah ce wlh tun da safe tazo ta tisamu gaba tana kuka wlh idan ka ganta sai ka tausaya mata kallonsa Abdallah yake cike da rashin fahimta " wai habeeb wa kake magana ban fahimcekaba dallah malam kayimun magana yada zan gane mana murmushi yayi " lateefa bismillah kallon habeeb yayi dan shi baisan wata lateefa ba da sallama tashigo kallo daya yamata ya ganota mik'ewa yayi ransa a mutikar b'ace ya nufi hanyar fita ta fashe da kuka ta rike masa kafa harbata yayi ya fice habeeb na masa magana bai saurare saba ya fito ya shiga mota driver yaja sukabar gurin ciki ya koma " kinsan Allah lateefa kiwa kanki fada ki dauki hakuri koda baduyi haka da ma haifinkiba ba lallai bane ya kulaki mata biyu gareshi dama nayi hakane dan ki tabatar ko muma kin barmu musarara mikewa tayi
tana kuka ta fice daga parlon jiddah tace" kaima sai kayi biko dan nasan fushi zaimaka mikewa yayi" ni nafita rakoshi tayi

***********

Karfe daya su shafa suka zo gidan soja akofa soja gamu yazo ganin Ramlat zai koma suka gaishesa ya amsa ya shiga mota ya koma gun aiki da sallama suka shigo parlon Ramlat ta miki daket ta tarbosu sai dariya suke mata tacika tayi fam yar gidan shaffah ta amsa jawa ta amsha yar gida Safna Nabeela tace" au kuna nufin no d'ana bashida uwa kenan jawa tace" aje hankalinki ni'imatu mai wayoce ta ajeta tana rarafenta ko ina ta amshi Nuradeeni suka zazauna jawa ta kira Ancim ta kawo masu ruwa da lemo da kayan motsa baki Nabeela tace"aunty Ramlat ya karfin jiki tab Allah yasa kafin mutafi ki haihu " Ameen amma da saura zanci sati biyu fah shaffah tace" Allah ba ruwansa da fadar Dr fada sace gaskiya Safna tace" nima fah haka sukace amma nacinye lokacin harda Kari wani kuma kiga baikai wa adinba Nabeela tace" Shaffah kin mata akace tsakanina dake sati uku amma ina ruwan Allah sai gashi kwana daya tsakani ai cikin budurwa haihuwar farko bata cikin wata Tara wlh Aunty Ramlat kin kusa haihuwa baki ciki sati biyu duk komai na Allah ne jikinta yayi sanyi binsu takeyi da idanu tausayi duk tabasu dan sunsa akwai yaki gabanta kam cikin sanyin murya tace" kusha ruwa mana jawa ta zuba masu kamar daga sama sai ga Nusaiba ihu Ramlat tayi da Sauri Nusaiba ta karaso ta rungume Ramlat " wlh kullum kina raina hidimar bikina ce ta badani sanin bakida lfy shiyasa ban takuraba yanzuma cewa nayi bari nazo na dubaki kar aje kin haihu" banason iskanci ya zan haihu bakida labari biki yau sauran kwana sha biyar fah " ai nagani gashi duk kin sauya dariya tayi ta gaishe da su jawa dariya sukayi suka amsa jawa tace" aikuwa lokacin kawarki ta haihu tana jego " wlh bari kedai idan na tuna har kuka nakeyi ni nakawota d'akinta gashi ni bata kainiba Allah ya sabkeki lafiya wlh ko washe garin aurena sunanki ya kama Allah sai na fito lemo Ramlat ta tsiyaya mata ta bata ta amsa tana sha " my nusaiba karkiyi haka kiyi hakuri kuci amarcinki suna cikin hirasu wasa da dariya sukaji sallama dagowar da jawa zatayi taga anty kausar wani uban zagi ta lailayo ta kurma mata ta wawuri plate ta nufi gunta cikin zafin nama nusaiba ta riketa " haba jawa lfy wanan ba antynki bace wada naga ranar sunan little Ramlat duk inda kikayi tana biye dake " eh nice wlh yanzuma neman gafara nazo naga sakaiya ido da ido mik'ewa Ramlat tayi tazo gun kausar ta kama hannuta " please karki fadi komai jeki kawai banaso ki falasata cikin jama'a kije idan taje gidan momy sai kuyafi juna kowa yaji abinda ya faru da dan uwansa har kofar parlo Ramlat ta fitar da ita ta dawo ta zauna nusaiba ta Saki jawa ta zauna ranta duk babu dadi su shaffah watsar abun sukayi suci gaba da hirasu da su nusaiba tunda bzsu san kan digin zancenba

suna hirasu ta mata duk kan haihuwa amma bawace ta yada tasako uwar wuyar da Tasha saboda kar Ramlat ta safe dayawa tako ji dadin yada sukace baby wata wahala shaffah dan ta Kara kwantar mata da hankali tace " nifa ina bacci ma saida naji yar ta fito da Sauri jawahir da safna suka kalleta tayi musu nuni da Ramlat shiru sukayi dariya Ramlat tayi " my sister shafffah kice nima una sharara bacci sai naji My Sojana na dadabani my Ramlat tashi ga danki ko yarki bushewa sukayi da dariya jawahir tace " aikuwa de hmmm Nusaiba ma dariya tayi fan ta gano Ramlat kawai suka kwantarwa hankali suna ta hira har akayi kiran sallah suka Mike gaba daya suka je suka sallah banda jawa har yanzu akwai jini jikinta ita ta rike yaran baki daya har suka gama sallah Ramlat ta kirawo Ancim ta dauki yaran daya bayan da tace sai sun gama cin abunci suka nufi kan dining abunci mai rai da lafiya jawa da su Ancim suka kirka jawa tayi sarving din kowa shnkafa ce fara da doya it am a fara sai jar miya da taji kaji manya Mayan da kwai aciki ga hadin salak da kwai sai danmbun nama da fruit yaji kankara kwasar kirki kawai suke ba magana nusaiba ma loda tayi son ranta Ramlat saida taji cikinta kamar zai fashe ta bari ta tsiyayi fruit Tasha ta Mike tana nishi sai dariya suke mata tana jinsu bayan sun gama suka dawo akaci gaba da hira

ta can uwantaka da shawara da zata karasu Ana suka yini tunkur sai kusan magrib suka tafi gida cike da kewar juna Ramlat harda kwalla tasan sa jima kafin su sake irin wanan haduwar saida jawa tayi ta lalabata badu dede da zamaba akayi kiran sallah magrib bedroom d'in Abdallah Ramlat ta shiga tayi wanka ta dauro Alwalla ta fito wardrobe d'insa ta bude ta ciro jallabiyarsa tasaka ta yafa mayafi tayi sallah azaune tayi ko da ta idar bata tashiba saida tayi sallah isha, tayi Addu'a Allah ya sabketa lafiya ta Mike haka ta fito dan ita haushin kwalliya takeji parlo tayi zamanta tana kallon Tv har jawa ta fito suna hira da sallama ya shigo parlon suka amsa dariyasa ya danne ya ware mata hannu tazo " Allah yayana kafata ta rike murmushi jawa tayi " bari na kamaki kije tashinta tayi ta nufi gunsa dariya yayi cikin siyasa yada bata masa kukaba rungumesa tayi " my sojana sannu kaga nasaka kayanka ko " my habibtyna kayana nakine kinyi kyaufa murmushi tayi hannuta ya kama suka isa kan kujera " zaunar da ita yayi jawa tayi masa sannu" yauwa ya jiki " Alhmdllh " gud Allah Kara lafiya bedroom d'insa ya shiga

Ta kalli jawa " d'an kamani na tashi please murmushi tayi ta kamata ta tashi jawa na gintse dariyata dan rigar tayi mata yawa sosai hanyar d'akin Soja tabi lokacin da tashiga yana wanka ta zauna bakin gado ta dauki wayarsa dayake tasan security d'in ta cire tana game har ya fito yana give jikinsa da towel karami " my habibtyna idan budurwata takirafa baki ta fara tayi jifa da wayar saman bed ta sabko ta nufesa jikinsa ta fada ta fashe da kuka tana dukan kirjinsa " Allah my Sojana da gaske kakeyi kanada budurwa awaje kamota yayi suka zauna bakin gado ya rungumeta yana shafa gashinta " my zumatyna please bari kuka matata wlh wasa nakeyi miki banida kowa kinji kai ta daga " Ya Abdallah karka sake min irin wanan wasan ni banaso fah murmushi yayi yana shafa cikinta " to Allah ya baki hakuri
Chapter 138 · 0% Book details