← Book details Hatsabibiya Ramlat Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 75 OF 152

Sashe 75

Hatsabibiya Ramlat Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

Kusanta ya zauna ya amshe tea dinta yana sha shagwabewa tayi ta kwanta kafadarsa " my sojana karka shanyemin fa bata yayi ta kurba " ki hada wani ni bazanci komai wani ta hada ta gama da sauran nata tana bashi abaki saida ya shanye tass ta sake hada wani ya amsa ya tallabota jikinsa yana bata tanasha har ta shanye " my babyna baza kici komaiba kai ta daga tana tashi daga jikinsa " my sojana tashi muje muyi hira ko fita zakayi" yauwa Ashe kin gane mikewa yayi zanje gida dagacan zan leka office Dina na Villa daga can sai mambila bansan ranar dawowaba maybe sai dare rau rau tayi da ido ta fada jikinsa " Dan Allah Dan uwana karka Dade nayi hakuri da dawo nan da awa biyu matesta yayi yana shafa lalausan gashinta" to naji amma karkiyimin kuka zan dawo my zumatyna zan kiraki musha hiramu kinji Mrs Abdallah kai ta dago tana murmushi

" Allah kai ka lafiya my jinin jikina "Amin my bungon zuciyata dariya tayi suka fito ta zauna kusan jawa " my jawa taso na ganki mana murmushi tayi ta tashi hanyar fita suka tsaya ya janyota jikinsa yana shafa cikinta " ya babyna " yana missing dina dadynsa " to kicemasa dadynsa ma yayi missing dinsa har mamasa dariya tayi " ni nafita sai dare shiru abinki idan yar gima tafara jaje kicemata ai ina tafe yanzu har ta manta " hhh sai na fadi gaskiya Dan kasa ta kafamun rigima irin na ranar harda kuka yayanta yaki dawowa bata bar in a na huta wlh rigima takemun ko tayi ta kwanci jikina tana hawaye wai nakiraka ka dawo gida dariya yayi " jawa ai kinsan bama haka dake fa please kiyita mata wayo har dare fuskarshi ta shafa " to naji zan lalabata har lokaci yaja" yauwa uwar gida ran gida my jawana amshi nan kiss ya bata mai zafi ya saketa bye hannu ta daga masa tana dariya har ya bace ta

koma parlo Ramlat na Danna wayarta jawa ta zauna kusan Ramlat suna hirasu cikin wasa da dariya Abdallah suna fita gidansu ya fara zuwa direct part din yinma ya Shiga tana zaune a parlour. tana waya ya zauna har ta idar ya gaisheta " ina yarana " suna lafiya " kiji hukuncin fa iyayanku suka yanke Alan Aminu fa safina ko" eh Abbie ya fadamun da zara n ta haihu zaa daura musu aure hakan yayi sunane sun rigada sun bata mana sai hakuri kawai Allah ya shiya yinma yafa kamata sadeeq yayi aure fa Naseer ne ya shigo da sallama " ah kaga mijin mace biyu yaya da kanwarta masha Allah haka kazama yaro hankalinka kwance nima fa inaga tabiyu zanyi kusan yinma ya zauna " wai Naseer meyasa ka dauki Abdallah abokin wasa kayi huduma mana

dariya yayi " oh yinma daga yabo shine laifi ke agida ba damar atafa Abdallah da Ramlat soja kallonsa yayi " to my brother kai da kanka ya kace Abdallah da Ramlat ai kayi karshen magana mudin a Family na dabane dariya yinma tayi " dakyau mazan fama mik'ewa yayi " yinma na koma amma zan biya gun Abbie nagansa Naseer yafa kamata sadeeq yayi aure zanga Abbi yanzu idan na fita " eh wlh nima nayi masa magana idan ya biya kasunwacin dayasa agaba to fa bazai yiba salllama sukama yia suka fice a tare anty Rahma ce ta shigo da sallama yinma ta amsa suka gaisa cikin mutumci ta zauna " yinma ina gafa kamar ya kamata my taimakawa Asiya ta dawo Rayuwa irin ya mutane ko ya kikace?

" Rahma ni kuwa me zance dibar albarka fa tamun ranar saida na mata wankin babban bargo " eh baa biya ta mutum ma gyaleta tana rayuwa kamar wata dabba ni yanzu haka wlh Nusaiba da take hannu Saude Dan banida yada zanyi da amso diyata nake saboda yarinya yanzu kiri kiri takemaka so kinsan halin Hamza bazai taba yada ya amshetaba saide kawai nayi ta Addu'a

" hakuri zakiyi kawai Asiya kuwa kibari zamuga ta inda zan fara insha Allah idan tanada rabon shiriya zata shiryu tinda yanzu ta fasa bin bokayan " Allah yasa mudace hirasu ta duniya sukaci gaba dayi,, hajara tana zaune tana kallon Tv Asiya ta shigo parlon tana Jan tsaki taje ta kashe tv " ke malama mufa kunna tv lokaci gareshi Ana gidan koda yake ba sabonba

acan gida babu Dole anshigo gidan arziki akalla " gaskiya kika fada a can gida babu kayan kallo saide akwai mutumci da tarbiyya da tsoron Allah ba Dan haka ni bana rigima iyayena basumun bakiba Alhmdllh tinda mijina na sona ba zaman yara nakeba ta fada ta shigewa dakinta " ke fan ubanki ni waye cemiki baya sona Munniru bashida abin so kamar ni yar matsiyata da kitsaya na kuya miki hankali safna ce ta fito " haba mamah Dan Allah kiyi hakuri matarnan tana miki biyayya fa " kunji uwarku ke da ita shegiya da baki kishin mahaifiyarki ficewa tayi ta barmata gidan tagama haukanta ita daya,,

************************************

Misalin karfe uku jawa na dakinta ta bacci Ramlat ma tinda tayi sallah bata sabkoba tacika tayi fam Abadallah bai dawoba su daya ya kirata yanzuma kwance take tana Miranda bata dauka tashi tayi ta sabko kasa bataga jawaba dakinta tashiga bata parlo tashiga bedroom tana sharara barcinta baki ta turo " damar bacci kika samu miji baya nan bakin gadon ta matso ta zauna ashagwabe tace" my dear kitashi dayake jawa batada yaunin bacci idanuta ta bude

ta kalli Ramlat da idanuta suka cika tab da hawaye da Sauri ta tashi zaune aranta tace" anzo gun rigima zata kafamun my love minene waye yatabamin ke jikinta ta fada ta fashe da kuka " my dear bake kikace yayamu agida zaiyi sallah azuhur ba amma gashi Ana kiran sallah la'asar bai dawoba " to kiyi hakuri nima na damufa amma ai zaizo yana fa office dinsa akwai abubuwa masu mahimmaci dayake idan ya gama zai dawo ki kirashi mana " baya dauka " to tadani muyi sallah zai dawo yanafa gari

daga tayi ta tashi tashiga bathroom ta dauro alwalla Ramlat tashi tayi tashiga ta dauro alawlla ta bude wardrobe din jawa ta dauko katon hijab tasa ta tayar da sallah suna gamawa jawa tace suje parlor fitowa sukayi suka zauna jawa ta kirasa amma bai dagaba bawan Allah wlh Abu mai mahimmaci yake zai kiramu murmushi Ramlat tayi " ba komai my dear mikewa Ramlat tayi ta iskesu inna talatu ta kama musu suka fara kirki amma hankalinta duk atashe har suka gama dab da magrib ta fito daga kitchen jawa, nazaune tana waya kusanta ta zauna ta dora kanta cinyar jawa. amma bata magana jawa ta kalleta tana murmushi ta dora hannuta saman kan Ramlat tana shafawa " to my love ai kaidin ne kasa hankalunmu tashi ai dariya tayi wlh munyi missing dinka sosai kadawo gida, idan kanaso hankalinmu ya kwanta ina lafiya miji ya fice tin safe gashi ana Kiran magrib gata, jikina my love amshi saita kanta tayi ta kakaro murmushi tace" my dear kice nayi fushi bana amsa

" ama my love afuwa amsa tayi tana dariya ta kara akunne " yayana ina yini ya aiki " my zumaty ykk akimun hakuri wlh tunaninki ya dameni naga kiranku abubuwa sunyi yawa nakiraki har so biyar baki dagaba "Ayya yayamu Afuwa phone DINA tana dakin my dear na manceta yanzu de lokacin sallah yayi sai ka shigo amshi my dear kuyi sallama ni nafi nayi wanka da sallah lokaci yayi taba jawa wayar ta tashi ta hayewarta sama " my love sai kashigo gaskiya ka dawo munyi missing dinka " OK sai nazo Ramlat gudu tayi koeh lokacin sallah yayi nima tashi zanyi " OK bye sai nazo kitt ya katse Kiran jawa tashi tayi ta shiga dakinta saman bed dinta taga phone din Ramlat ana kiranta taga sunan *my jinin* *jikina* yana yawa saman screen wayar ajiyewa tayi ta shiga bathroom ta dauro alwalla Ramlat bangaran Abdallah tashiga bedroom d'insa tashige ta fada saman bed dinsa kayansa da yacire da safe ta rumgumesu tana shakar kamshinsa ta lumshe idanuta tana sabke ajiyar zuciya hawaye na gangarowa daga idanuta ba tare da tasan daliliba tajima kafin ta Mike tashiga bathroom dinsa tayi wanka ta dauro towel

ta fito wardrobe dinsa ta bude taciro jallabiya fara tasaka ta tayar da sallah tana gamawa tayi kwanciyata saman bed d'insa tana juyi da Jan tsaki Jawa tana gama sallah ta fito da wayar Ramlat ahannuta tana zama phone din Ramlat ta fara ringing taga tana dubawa taga *my bugon* *zuciyata* bata dagaba ta Mike ta haura sama amma ta duba Ko ina a shashanta batana " to ina taje Ko tana kitchen ne har zata sabko taga kofar soja abude ta shiga tana Kiran " my love shiru ba kowa a parlon fitowa tayi dan batayi tunanin KO tana cikin bedroom din saba ta sabko taje kitchen batanan to ina Ramlat tashiga ne tana zaune aka kira sallah isha, ta tasji taje tayi sallah Soja ya shigo parlon da sallama shiru ba kowa yaransa biyu suka aje kayan hannusu suka fice sama ya haura yana zuwa yaga kofar parlour a bude shiga yayi ya rufo kofar ya nufi bedroom ya cire kayan jikinsa ya d'aura towel zai shiga bathroom yzji motsi kallon gadon yayi yaga ta tsareshi da idanu
Chapter 75 · 0% Book details