← Book details Hatsabibiya Ramlat Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 115 OF 152

Sashe 115

Hatsabibiya Ramlat Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

awani hadadan madedecin gida mai masifar kyau ya tsaya parking yayi yana tunanin yada zai fara shiga nemanta cikin ikon Allah sai gata ta fito tana waya alamar kwatance ne takewa wani ko wata cikeda mamaki take kallon dirkekiyar motar da take kofar gidansu fitowa yayi fuskarsa dauke da murmushi idanu ta zuba mishi cike da mamaki take kallon Soja yada yayi kyau haibarsa da kwarjinisa sun fito ya hade cikin wata arniyar shadda kalarta ruwan Zuma gashin kansa kwance luf sai sheki yakeyi sajansa ya kawat fuskarsa gunta ya karaso kasa tayi da kanta dan wanan shegen lumsasun idanu nasa mace bata iya jurar kallonsa dan har ga Allah ta Mance waya takeyi da kawarta ta gun aikisu da takewa kwantacan gidansu nutsuwarta ta tataro ta saki murmushi

" yayamu barka da zuwa daga ina haka ina kawata dazu ina ta kiranta bata dauka ko tare kuke murmushi yayi " my Nusaiba irin wanan tambayoyi haka wacce zan amsa yada ya kirata sai taji barbakwai ta maimaita sunan aranta " inason magana dake kibani yan mitina " OK yayamu mushiga daga ciki bayanta yabi suka shiga ciki parlon baki ta kaishi ya zauna ta shiga ciki ta kawo masa ruwa da lemo ta aje masa wata kujera daban ta zauna yace ta dawo inda yake bata musaba dan kwarjini yakemata sosai cikin tattausar murya ya fara mata magana ya zano mata abunda ya kawoshi gunta kuma yace bayaso komai yajima kuma karta damu saida ya fara neman sadeeq saurayinta na da kafin yazo gurinta zuface take keto mata ta ko ina jikinta rawa yakeyi tsoro ya kamata sanin wacece Ramlat hada miji da itama bala'i ne bare kawarta tun ta primary har yau basu rabubu saida ta tafi karatu ne suka rabu tana dawowo suka koma kamar da duk wani yawansu tare suke abunsu itace ta kaita dakin mijinta shine mijinta zaizo yace yana sonta dan Allah ta aureshi mikewa tayi tana kuka harda bubbuga kafa " wlh soja nide ba daniba Allah bana sonka bazan aureka ransa ya soso dan yasan duk macan da tace bata sonsa karyane yana ganowa daga kwayar idanuta mikewa yayi yana murmushi ya nufo gunta " karya kike Nusaiba kicede kina tsoran Ramlat kawai ganin yada yake nufota yasa ta zuba da gudu saboda ita masifafiyace bata barin aci zalinta shiyasa ai tun suna yara tasu tazo daya da Ramlat akofar d'aki ta tsaya tana maida numfashi tana murguda masa baki ta hararesa " eh ba'a sonka sai nacuci kaina yo mezanyi dakai Allah kiyaye nayi auran cin Amana mezanyi da mijn mace biyu ina yarinya karama ko ka manta ni sa'ar matarka ce Ramlat ai itama naga kokarinta da tashiga gidan me mace ai abinda ya hadani da captain kenan nufota yayi ya damkota ta murguda baki wlh nide bana Sonka ta zuba da gudun bala'i tana ihu kansa ya dafe " Anya zan iya kuwa dan naga alamar yarinya itama fitina zatayi karfa najawa kaina hawan jini ina zan iya da mata ukku aikuwa idan banyiba to wlh bazan huceba akan bakin cikin da ta kumsamun gwara na auri wacce Takeda kusanci da ita wayarta da ta bari ta dauki ringing ya dauka har Kiran ya katse number ya saka sa yayi Kiran kansa yaga numberta ya aje mata wayarta ya fice

babu alamunta awaje murmushi yayi motarsa ya shige ya nufi maitama itako Nusaiba da gudu ta fada parlinsu dan ta tsorata yada soja ya nufota tanajin labarin muguntar da yakeba Ramlat saman cinyar umma ta fada tana zazaro idanu irin na marasa gaskiya " ke kekuma kedawa was kika tabo keda Mubarak ko ba kawarki kika fita ki taroba baki ta turo ta Mike batayi magana, ta shige bedroom,

lokacin da ya iso ana Kiran sallah magrib yayi alwalla ya tafi masallaci bai dawo saida akayi isha'i part d'in yinma ya shiga tana parlo da tasbaha ahannuta tana ja zama yayi ya dora kansa akafadarta "yinmata barka da dare kansa ta shafa " Abdallah ya gida ya dota da jiki"da sauki suna gaisheku ina Abbie ko basu isoba daga kadunar " basu zuba tashi kaci abunci kalli yada idanuka suka fada wai mema ya sameka haka ga damuwa karara a idanuka " yinma babu komai amma zuwa gobe zan fadamuki wani Abu dan Allah karku hanani banayin Abu saida dalili dan Allah karki bari Abbie ya hanani " to ikon Allah meye shi abun Allah ya kaimu tashi kaci abunci mikewa yayi yaje ya danci ba lafi yayi mata slm ya tafi part Auntynsa ya nufa itama de ta gane akwai damu atare dashi tayi ta lallabashi yada ya fadawa yinma haka ya gaya mata dan baya iya boye mata komai tun yana yaro tabashi hadinkai tace Allah ya kaimu koma menene zai samu insha Allah daganan ya biya part Dada suma abinda yace musu kenen ita da mai ran karfe yaso ya gayama Dada abinda Ramlat tayi masa dan yasan tana sonta sosai

bazata fadawa waniba amma sam ya kasa ya tafiyasa lokacin da yaje Ramlat na zaune jawa ta gama bata abunci taci sosai saboda kirkin yayi dadi sosai da slm ya shigo jawa ta amsa tayi masa sannu ya amsa " my jawa na jima ko murmushi tayi " ba komai " Ramlat ya jikin kallonsa tayi ta sada kanta " da sauki bai sake cewa komaiba ya zauna ya ajiye ledar kayan " tashi mutafi na kaiki gida dare ya fara kije ki kwanta ki huta baby ya amsa yana mata wasa mikewa tayi ta hada kayan tayima Ramlat sai da safe cikin sakin fuska ta amsa tayi mata godiya suka fice mikewa tayi ta sabko daga gadon ta duba ledar da ya ajiya taga kayantane harda su pant sai rigar baccinsa daya Riga doguwa ta dauka tafi toilet saboda sosai taji karfin jikinta sai de jini yana dan fita wanka tayi tsaf ta shirya jikinta ta fito ta sauya zanan gadon itama yanzu ta dau alwashi idan ya dawo banza zatayi dashi dan batada lfy zai wani mata shan kamshi kuma ta tambayi jawa ko cikintane ya zube tace A,A cikinta na nan juyin ma haiface kawai tsaki tayi ta janyo wayarta wada soja ya kawo mata tana dannawa taga Nusaiba tayi takiranta har so biyar " shegiya bazan kirakiba kina garin Abuja sai ki take wata biyu bakizo inda nakeba sai abkin kira ta waya taga K'iran soja har hudu tsaki taja ta aje wayar tayi kwanciyata Soja bai jimaba da ya maida jawa gida ya dawo ya kwasowa Ramlat drinks da kayan ciye ciye lokacin da yazo idanuta biyu amma tayi banza dashi taki juyowa kayansa ya cire yaje yayi wanka yafito da towel dauré ya goge jikinsa yasaka rigar baccinsa ya Haye gadon zatonsa tayi bacci ya janyota jikinsa ya burkito da fuskarta yaga idanuta biyu ido suka hada ta turo baki gaba face ya hade ya hada gira sama da ta kasa yaja tsaki janye idanuta tayi tana turo baki ta kara shiga jikinsa bai kulataba ya kara matseta jikinsa ya rufe idanusa don kansa mugun ciwo ya kema har wani jiri yakeji lamo tayi ajikinsa tanaso tace yamata tausa tana tsoronsa hannusa ta janyo guda tana dannawa jikinta ya gano nufinta yayi banza da ita yana jin gunjinta tanaso ta fara kuka yayi burus da ita daga karshe tayi fushi ta matsa daga kusansa fisgota yayi da karfi ta dawo jikinsa ya rumgumeta tsam tsam ciki masifa yace" karya kike ki bugeni ki hanani kuka maza kwanta jikina bama raba makwanci ko wuya ko dadi saide kiji launin azabata fuska ta kwakwabe ta bude baki zata fasa masa kuka ya buge bakin " wlh karki ma fara shiru hadiya kukanki ko na nuns miki kalata yanzu danne kukan tayi tanajin zafin labbanta da ya buge mata tacika tayi fam ta tura kanta da karfi cikin kirjinsa ta rumgumeshi gam kamar yada ya rungumeta tana sabke ajiyar zuciya da sauri sauri dan ranta ya baci sai cusa kanta kirjinsa takeyi yana jinta yayi banza da ita dan ciwon kansama ya shamishi kai hakade har bacci ya kwashesu suna manne da juna kar biyu na dare ya farka ya janyeta jikinsa ya shiga toilet ya dauro Alwalla yasaka kayansa ya shimfida sallaya ya tayar da sallah ya jima sosai dan bai dainaba saida akayi k'iran sallah ya bari ya shiga kwararo Adu'a Allah ya cire masa damuwar zubewar cikinna indan auransu da Nusaiba akwai alkairi Allah ya tabbatar dan yaji aransa haka kawai yanason auranta baisan daliliba tunda yaje gidansu da yanayin abubuwanta tamkar Ramlat takeyinsu shide yaji ana fada agidansu halaiyar kawar Ramlat komai yazo daya da Ramlat sai jiya ya tabbatar da hakan Adu'a ya sosai ya daga hannuwansa yakai kukansa gun Allah idan da Alkhairi Allah ya kawo komai cikin ruwan sanyi idan babu Allah ya ya ruguza Al'amarin cikin sauki yabar jin son abun aransa ya Mike yayi sallah raka'atanin fajri ya tashi ya tafi masallaci daga waje ya rufota ya tafi a can baya ya tsaya bayaso yan gidansu su ganshi har aka gama kuwa babu Wanda ya ganshi har ya dawo ya bude kofar ya shige ya murza key gadon ya Haye ya janyota jikinsa ya rumgume abarsa ya gyara mata gashinta ya daurémata bai wani jimaba bacci ya daukeshi har yanzu kansa na masa ciwo... ✍🏻

Rahma ce ummu Fareesa😘

✍🏻✍🏻✍🏻

*🤷🏻‍♀HATSABIBIYA🤷🏻‍♀*
*💖💖RAMLAT💖💖*

*_🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION_*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

Story & Written by
✍🏻
Real Ladingo😉
yar mutan Niger🇳🇪

*👏🏻👏🏻👏🏻DON GIRMAN ALLAH KARKUMANTA DA GIRMAN ALKAWARI DA AMANA KARKU FITARMUN DA BOOK WAJE KUKARANTA KYAUTA RUWAN ALLAH AMMA ARIKE AMANA👏🏻👏🏻👏🏻*

*Bismillahir Rahamanir Raheem*

*Book 2* 🅿👉🏻3⃣1⃣&3⃣2⃣
Chapter 115 · 0% Book details