← Book details Hatsabibiya Ramlat Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 35 OF 152

Sashe 35

Hatsabibiya Ramlat Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

gun yinma ta tafi ta zauna, tea ya fara bata amma taki ta amsa sai hawaye take tana turo baki yayi yayi taki amsa kallonta yayi ya kamo hannuta " my angel mai na miki kuma ko yau Sam baki son abinci ne kallonsa tayi tana turo baki kuma sai ta fashe da kuka ta fada jikinsa tana kiran

Abbie rikiceawa yayi yada yaga duk hankalinta atashe yana bubbuga bayanta " my Ramlat ni bansan mai kike so ba ya zan miki please yi hakuri me kikeso,

Matsalata dake baki magana sai maimaici dago fuskarta yayi ya kuramata ido itama shi take kallo tana lumshe idanta tamkar tanajin bacci ahankali yayi mata magana " abar kaunata meya sameki duk kin birki cemin zaunar da ita yayi cikin dubara ya fara bata tea din abaki yana lalabata yatsareta da manyan idanunsa ta fara amsa tana sha ahankali har ta shanye, tana tuturo Baki alamun an tabata

ya yago gasasar kaza ya bata abaki ta faraci itama sai ta yago ta basa abaki baiyi musuba ya amsa yanaci ahaka har takoshi tashiga girgiza kai murmushi yayi ya mikar da ita tsaye yaja hannuta suka nufi kitchen ya wanke mata hannuta sai dariya take tana yarfa mishi ruwan hannuta a fuskarsa murmushi yayi ya kama yatsar hannu ya ciza kadan dariya tayi itama ta kamo

hannusa ta ciza da karfi tana dariya zungurata yayi akai " kina cikin cutar mantau ma sai kinyi mugunta ko janta yayi suka fito parlour yinma tace" taci agunka ko zama yayi kusa da yinma itama ta zauna kusansa ta Dora

kanta akafadarsa " eh taci amma nima da kyat na lalabata " Allah yabata lafiya ke shaffah tashi dauko maganin " har yanzu batasha maganiba ai sai ku kirani abar bari rana nayi,

Shaffah ta kawo maganin da ruwa ya ballo ya dagota ya saka mata abaki nan ma saida ta cijeza cikin wasarwa yayi ganin jawa na kallonsu ya bude gora ruwa ya Kafa mata abaki Tasha sosai ruwan yinma kallonsu take cikeda Shawa aranta tace dama burina ya ciki amma

nasan hakan ba mai samuwa bane jawa ko da taga abin zai tabamata zuciya sai ta tashi ta nufi part din Dada bata jimaba da shan magani tayi bacci, tana jingene akafadarsa

Ana parlour ya kwantar da ita saman 3 seater " yinma na tafi dan Allah in ta tashi akularmun da ita baiwar Allah" to sannu Allah yayi albarka ya kuma bata lfy" amin ina Abbie " bayanan sun fita shida mansour ficewa yayi ya nufi part din anty rahama da sallama ya shigo parlour tana zaune tana shayar da Rufaida ya zauna yana gaisheta" soja ya dai nakeganin kana cika kana batsewa,

" haba dan Allah anty mai baiwar Allah tayi daga zuwa dubiya dan taki cin Abinci sai ki daketa ai ba ahankalinta take a sai hakuri " au dama shine kake cika kana batsewa to Allah ya Baku hakuri wlh haushine ta bani hardasu Abbi da Papinta anyi anyi tayi breakfast taki sai kiran Abbie take shinefa na dan zungureta da Mari daya ido ya rumtse " haba anty Mari baiwar Allah wlh gun har ja yayi murmushi tayi tayi banza dashi

Ya gaji da mitarsa ya Mike ya fice part din Dada ya nufa a parlour ya sameta ita da jawa kusanta ya zauna " my Dada bakya nemana ma ko " kajini da ja'irin yaro kai ka nemeni ne ayau nida shalelena ta manta dani dazu ba yanda ban ba taki tazo guna murmushi yayi " to ai

Bazata yada dakeba sai ta dado daidai " to Allah bata lfy ai gobe ina jiran usman ya iso ya kwana biyu ya huta akirawo iyayan Ahmadu face ya hade ya Mike " jawa zo in baki sako kwanar parlour ya tsaya ta iskoshi hannuta ya rike " please

karkiyi fushi da my angel da abinda ta miki ba ahankalinta takeba ita yanzu bata San wani soba kawai shirmenta ne take

Saboda ayanzu batasan kowaba saini murmushi tayi " tana boye hawayen fuskarta " yaya wlh ba komai ai nasani murmushi yayi ya lakaci hancinta " yauwa jawa thanks rungumesa tayi tanajin sonsa har cikin jini da tsukarta na yawa janyeta yayi ya rankwafo ya mata kiss agoshi yaja hannuta suka shigo parlour

Dada tace" ikon Allah Abdullahi Manya dugowa yayi yama dada kiss a goshi yana murmushi " to dada na tafi sai dare zan leka Villa jawa na tafi kai ta daga masa tana murmushi ficewa yayi ya nufi

harabar gida gun da motor take ya nufa suka bude masa ya shige suka tafi, tinda Ramlat tayi bacci bata tashiba sai kusan karfe biyu shaffah ta jata taje tayi wanka tayi sallah amma fur taki cin abinci haka

tayi zamanta saida soja yazo ya bata taci Ana suka yini har dare ganin soja yana nan yasa Ramlat ta Saki jikinta tana wasanta tamakar wata yarinya sai da ya bata abincin dare Tasha magani tikon suka fara shirin tafiya tanaga ya tashi ta Mike ta fara kuka sanin

maganin na saurin sata bacci ya zauna Abbie yau abun nasu dariya ya bashi" wlh wahalar da kabata yau GA ranar fanshewa nan hannuta yaja ya nufi gun kwancinta ya zauna bakin gado itama zama tayi tana dariya

Tunkudata yayi cikin wasa " oya yi bacci na tafi my Ramlat bacci nakeji matsuwa yayi yana shafa kanta ta dago Kanta tayi ta kallesa ya kashe mata ido murmushi tayi tana lumshe ido" Abbie I love u

murmushi yayi " my angel I love u too bakinsa ya matsu kusa da kunneta yana mata kalaman soyayya tamkar tasan abinda yake fada sai murmushi take ta

rike hannusa daya gam tasaka yatsarsa abaki tana cizawa tin karfi yanajin zafi amma ya daure har bacci ya dauketa yanaga tayi bacci ya janye hannusa daga com n bakinta da ta ciza yatsar har tayi ja murmushi yayi ya mata

Adu'a ya tofa mata yashafa mata afuska ya lulubeta da lallausan bargo ya Kara gudun Ac ya fito parlour yayi musu Abbie sallama jawa ta musu suka tafi suna zuwa gida

Kowa ya nufi bangaransa yayi wanka shiryawa yayi cikin kayan bacci ya fito dakin jawa ya shigo lokacin ta gama shirin bacci tana tsaye atsakiyar dakin " bakiyi bacci ba murmushi tayi " eh ban yiba baiyi mata magana ba ya kamo hannuta ya kaita har man gadonta ya kwantar da ita shima ya kwanta" naxo tayaki kwana

Murmushi tayi ta rungumesa tana shakar kamshinsa dago fuskarta yayi suna kallon juna kasa daure kallonsa tayi ta sada kanta hannu ya meka ya kashe wutar dakin" oya muyi bacci ya rungumeta narkemasa tayi baidai yi mata komaiba har bacci ya daukeso suna rungume da juna Asuba ta gari,

*********************************

Yau kwana hudu da farkawar Ramlat har yanzu idan ba soja ya bata abinci ba to bazata Ciba sosai yake kula da ita a man kwanakin nan ta murja tayi kyau sun shaku da soja shakuwa mai tsanani shi kansa baya cika awa biyu batare da yazo ya dubata ba yanzu tana magana kadan kadan sangarta iri iri take

masa idan yazo saida dabara yake tafiya dama dama yanzu idan taga anty rahama to guri daya take zama saboda dukan da ta mata tashiga tsoranta ta dan fara yada da yinma da shaffah kadan kadan

Tsoho mai ran karfe yau yace kowa da kowa da yanma ya hallara Ana hada meeting Family buzun Bagayyah akarfe biyar na yanma Abdallah gabansa saifaduwa yake dan yana tuna karfa aje a daurawa angel dinsa aure da Ahmed

Tin karfe uku soja ya zo amma yana part dinsa hankalinsa atashe yayi kwance yana tunani har akayi sallah la'asar ya Mike yaje masallaci Ana gama sallah gidan ya fara taro jama'a part din yinma ya shiga parlour sunkusa su goma cikeda kunya ya gaishesu ya juya ya fito

mik'ewa tayi zata bishi har ta fara kuka anty rahama ta daka mata tsawa ta koma ta zauna tana kuka anty" maimunatu tace " haba rahama wlh abinda kike ba daidai bane Akan mai zaki rika takurata sanin kankine Ramlat in lafiyata kalau zaiyi wuya ta takjrawa Abdallah ke jawa tashi ki rakata gunsa ku zauna idan an fara meeting zaaneme ku mik'ewa tayi

Ta kama hannu Ramlat fizgewa tayi tana turo baki saudat ta kalleta " hassana tashi kutafi gun Abbie zata kaiki mik'ewa tayi tana dariya jawa taja hannuta suka nufi part din soja yana parlour ya hada kai da guiwa yarasa abinda yake masa dadi daga kofar parlour ta tsaya ta. Nuna mata soja saboda bata son abinda zaisa tank tsanar

Ramlat fita tayi ta zauna a harabar gidan Ramlat ko daga bakin kofar parlour take kiransa tana murmushi " Abbie I love u cikin Sauri ya Mike yana murmushi ya ware mata hannuwansa da gudu ta taho tana dariya ta fada girninsa ya rungumeta hawaye na fita a idonsa " my angel ina tsananin kaunarki dan Allah kar ki yada arabamu janyeta yayi daga jikinsa ya kamo hannuta suka zauna amma taki zama saida ta

Dora kanta akafadarsa tana dariya kana ganinta kasan afarin ciki take Tv ta kurawa ido tamkar tasan mainene ake sai kuwa aka sako waka indiya tana kallo tana dariya tana Kada kai azaune tin tanayi azaune har ta Mike sak yanda

suke rawar itama sai ta fara tanayi tin karfinta kallonta ya tsaya yi har baisan lokacin da ya fara dariya ba saboda sosai ta ita rawa mik'ewa yayi ya janyota ta zauna " my angel huta haka kinyi rawa sosai

dariya tayi ta Dora kanta akafadarsa ta kamo yatsasa guda tasa abaki ta ciza da karfi yaji zafi amma ya basar Abu kamar wasa saida gun yayi jawur amma ya kasa hanata murmushi tayi tana kallon yatsar " Abbie kalli kallonta yayi ya lakaci hancinta " nagani idan baki gajiba to cigaba da cizawa

Sakin yatsar tayi ta kamo fuskarsa tana hawaye tana girgiza kai " to ni me nace miki my Ramlat kodan ki hadamin zafi biyu naface kici gaba da ciwa ko na hanakine,
Chapter 35 · 0% Book details