← Book details Hatsabibiya Ramlat Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 114 OF 152

Sashe 114

Hatsabibiya Ramlat Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

kamar jira yake ta fita ya fashe da kuka abinda ko me za'amasa baya yinsa da garaje kuka " yanzu Ramlat abinda zakimun kenan kin kyauta meyasa tun farko kika nuna kina sona dama kinyi hakan dan ki kullamun bakin ciki azuciyata kika zubarmun da ciki kinsa irin son da nakewa cikin jikinki kinsa irin Alherin da nayi akan cikin ki aboyé Ashe duk sona da nake gani a kwayar idanuki na karyane cikin wata irin kururuwa da tsawa yace me!!!!yasa Ramlat.. Me!!!yasa kika yaudareni kika kashemun gudan jinina hannusa ya nausa abango saida hannu ya kawo jini jikinsa na karkarwa ya kasa ko zauwa kusanta kallon daya zaka masa kasan yana cikin baccin rai jijiyoyin kansa sunyi rado rado idanusa sunyi jajur ko ina najikinsa rawa yakeyi jiyake kamar yaje ya shaketa yakeji yau kam Allura Sojoji ta motsa fuskarshi babu rahma ko gudu dolene a wanan lokacin idan Ka kalli soja kallo daya kayi kokarin dauke kanka daga kallonsa yakai awa daya zaune ya kasa tashi mikewa yayi ya shiga toilet yayi Alwalla ya tafi masallaci yana dawowa ya zauna gun da ya tashi

babu irin tunanin da bai zomasaba sai yanzu ya kara tabbatarwa da son da jawa take masa na hakikane tunda ta iya jurewa ta haifo masa da gudan jininsa mikewa yayi yana tangadi ya nufi gadon da Ramlat take kwance ya zauna har yanzu bata farfadoba idanu ya tsara mata babu wani dugo da yarage asonta azuciyarsa shine abunda ya damesa yanzu dan yanaso yaji tsanarta aransa yada zaiji dadin hukun tata yamata horo mai tsanani yada ko wata taji zata zubar da ciki hankalunta sai yatashi rankwafawa yayi ya dora kansa ak'irjinta ya tura hannusa cikin gashinta yana shafawa hawaye na zuba idanusa ya fara magana" my Ramlat nagode da butulciki gareni nagode da zubarmun da gudan jinina da kikayi bansan baki kaunataba wlh da dau son da nake miki bazan taba yada namiki cikiba lokacin kafin ki samu ciki Allah kade yasan damuwar da nake ciki burina naga cikina ajikinki Ashe dama can bakiso shiyasa baki taba mun zanceba ina jin yaunin Auntyna bazan iya sakinki ba ga mugun sonki na damuna bazan iya sakinki ba asalima bazan iya fadawa kowaba banaso wasu su zagarmun ke ko kuma atsaneki na tabbatar Auntyna taji wanan mugun abun dakikayi abunda zata miki sai yaba kowa mamaki so bana so zafi ya miki yawa azabar da zan gana miki kade ta isheki wlh sai nasaki kukan da yafi wanda kika sani zan baki mamaki dan in kuntata miki zan auri kawarki Nusaiba duk babu digon sonta araina kai asalima banida burin da yafi na zauna da mace daya araina to Allah bai kaddara ba amma kinsa ni zan kara auran huce haushi duk danasan zansha wuya kafin na samu hadin kanta amma nasan zata soni wanan abun kawai zan miki na huce wlh sai na auri kawarki nasan zaki fi jin tsanar abun fiyeda komai aduniya ki dandana kiji azabar da naji don yanzu sam bazan iya dukanki ko horo na wahalaba

Wanan kade ya isa da na bata miki suna a Family gwara hakan janye jikinsa yayi ya koma can nesa da ita ya zauna ko 4mnt baiba ta fara motsa alamar ta farfado da sauri ya Mike ya fice ya kirawo Dr tare suka shigo da sauri ta shiga bata temako numfashinta ya dawo nurmal ta cire mata Karin jinin da ya kare da idanu take bin Dr Ameera da kallo a cikin sanyin murya tace" Dr ina yayana da su yinma " sannu Mrs Abdallah ya karfin jiki gashina bayanki zaune bari naje na kawo maganin da zakisha yanzu Soja dan Allah kayi kokari taci abunci sai tasha magani mikewa yayi yana kallon Dr " muje waje inason magana dake yayi gaba tabi bayansa akofa suka tsaya " abinda nakeso dake wlh karki kuskura koda wasa watarana kice zaki fadawa wani daga cikin Family dinmu laifi de ni tayiwa nikuma na yafe mata dan haka ki tsira da mutumciki da na aikinki dan bazan tana bar in Wanda zai wulakanta mun Ramlat ba ni nasan irin hukuncin da zamata " wlh insha Allah babu Wanda zan fadawa " OK nagode ya koma ciki ya murza kofar key da kallo Ramlat take binsa yada ko kallonta yaki gabanta ya fadi tuna lokacin da take kwance cikin jini cikin sanyin murya tace" yayana bai amsaba ya kalleta fuska a hade ya mata nuni da hannu lafiya " dan Allah yayana zo ka rungumeni sanyi nakeji hararata yayi amma bai cemata komaiba yama kara matsawa daga kusanta ya fito da wayarsa yayi dailing wata number bugo daya aka daga

kome ya fada oho baide jimaba ya katse K'iran knocking kofar akayi ya Mike yaje ya bude Dr tace ta shigo da maguguna aleda ta gwargwada masa yada zatasha su harda na Karin jini godiya ya mata ta karawa Ramlat sannu da jiki tambayata yayi za'a sallamesu yau tace A,A sai ta kwana sai anyi mata Karin ruwa yanzuma da ta gama cin abuci tasha magani ya mata magana zata turo asamata ruwa ta fice Ramlat hawaye yacika mata idanu tanaso ta Mike ta zauna jikinta babu kwari " yayana zoka temaka mun na zauna kaji! baiyi magnaba yazo ya dagota ta zauna zai juya ta rike masa hannu ta fashe da kuka don Allah yayana me na maka kasan bana jure rashin maganarka gareni please fadi laifin da nayi maka zama yayi bakin gadon yayi murmushi mai ciwo " Ramlat kenen mekuwa kikayi tunda har bakisan abunda kikayi har kina gadon asibiti ma so babu damuwa ai ranar ramako na tafe lokacin sai ki gane me kikayi OK ya cire hannusa da ta rike

Ya taba jikinta yaji babu zafi fuskarsa tam ahad'e yace " kinajin sanyi haryanzu jikinta duk yasaki hankalinta ya tashi bata iya magaba ta daga masa kai jikinsa ya janyota ya rungumeta gam ya janyo hijab d'inta ya rufesu lamo tayi jikinsa tana tura kanta k'irjinsa tana shakar kamshinsa shi kansa yasami nutsuwa da yajita jikinsa yanzu kara matseta yayi yana sabke ajiyar zuciya gam ta rikeshi " yayana idan nayimaka laifi kayafemun dan Allah karka gujeni bana iya jure rashinka ta fashe da kuka " wlh ki hadiya kukanki maza karki cazamun kai dayawa nine ya kamata nayi kuka kuma nayi na barwa Allah komai tunda bakison haihuwa dani bazan kuma miki cikiba ki kwantar da hankalinki kanta duk ya dauré bata gane maganar ba shiyasa ta janyo hannusa daya ta dora cikinta tana shafa " yayana shafa babynka wlh inason haihuwa da kai Allah kadai yasan yada nakeson wanan cikin zaiyi magana aka buga kofa ya janyeta jikinsa ya zaunar da ita yaje ya bude kofra jawa ce dauke da kwanonin abunci yada taga fuskarta yasa tashiga

hankalinta ya matsa mata ta shige ya rufo kofar suka kayan ta aje Soja ya sabko little Ramlat daga bayan jawa ya rungumeta tsam ya zuba mata idanu jawa gun Ramlat taje ta zaune tana hawaye " my love sannu ya jiki " da sauki
abunci ta zuba mata a plate " gyara na baki " na koshi wani kallo soja ya watsa mata babu shiri ta bude bakinta jawa tana bata tana ci har ta koshi ya nunawa jawa magani ta dauko ya fito dasu daya bayan daya yana bata har tashanye

" my love Allah yasa de babu abunda yasami babyna hararata yayi fuska a hade " ban saniba wlh hukuncin da zanyi kema sai ya shafeki meyasa baki fadamun tinjiya " Allah ya baka hakuri ai banzata abin zaikai hakaba amma dan Allah wani hukuncine zai shafeni Ramlat da idanu take binsu dan sam bata gano komaiba banzq tayi dasu ta juya musu baya tayi kwanciyata " kasha' da zan miki kuwa shine karki kuskura kigayawa wani kindai san hali tau haushi ya fara bata da halamu de bazaice Ramlat ta koma gidaba saide da alamu cikin ya zube mikewa tayi " bari nashiga gida " ba inda zaki banason kowa ya sani dan haka ki zauna zanje gida na dawo ke sai ki koma " to sai ka dawo baby ya bata ya ficewasa ya turo Dr ta saka mta drip jawa na zaune da ita idanuta biyu amma ko kallo jawa bata ishetaba tayi ta maganar har tagaji tayi shiru dan Ramlat jitake kamar jawa ta hadata da soja shiyasa takejin haushinta

Soja yana fita ya shiga mota yaja yayi gida yana zuwa yayi wanka yayi sallah la'asar dan lokacin da yazo angamata kenan ya cire kakin soja ya saka kaya saka ya shiga gyara dakinsa ya cire zanan gadon ya shmfida wani ya cire carpet din ya sakq wani masha Allah kamar mace saida ya tsaftace ko ina ya kunna turaruka masu kamshi ya Haye saman bed ya fada tunani ransa na masa kona Ramlat taci Amanar taci Amanar kauna Ashe duk karyace sonda take masa ta kasa rike masa gudan jinisa acikinta saboda tana fama da laulayi haushinta yakeji sosai auran Nusaiba shikadai zaisa ya rama abunda tayi masa mikewayayi idanusa jajur ya dauki makullu mota ya fito dakin Ramlat ya shiga ya dauki kaya kala ukku da hijab daya yadaka aleda ya fito kasa ya sabko harabar gidan ya fito yaransa na Mika masa gaisuwa yana daga musu hannu ya bude motar ya shiga ya hana kowa binsa ya shige yaja aka bude masa get ya fice gudu yake sosai kan titi cikin kwarewa yake murza kan motar gidan Sadeeeq ya fara zuwa bai jimaba sosai ya fito yana murmushi ya bude motar ya shige ya bata wuta naga ya nufi babban titin gwarumfa yana gudu sosai saboda bayaso yayi magrib acan
Chapter 114 · 0% Book details