← Book details Hatsabibiya Ramlat Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 25 OF 152

Sashe 25

Hatsabibiya Ramlat Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

Tasuwa tayi tazo ta rungumeta yi hakuri kinji to ya akayi ka gansu " lokacin ina parlour zaune saboda gida cikeda jama'a hankalina bai kwanta ba ina kalonsu ta CCtv camera suka shigo kuma security sun gansu ni nace su basu muga gun suka zo duk abinda sukayi ina kallinsu saida suka dauketa suka fita mukabi bayansu har kaduna Rumaisa ta yaudareni

Bazan taba yafe mataba wlh nasu kashe sai naga gwara tanje ta iske abinda ta shuka " yanzu Abdullahi ya zamuyi da jama'ar da aka tara agidanan gobe mik'ewa tayi tanufi bedroom din maigidanta ta kirawoshi yaga komai kansa ya dafe cikeda mamaki " to yanzu soja kanada wace zaka iya kawo mana agobe" Abbi nifa

wlh natsani mata ma baki daya wlh auran ya fita araina " aikuwa karya kake wlh bazaka tozartaniba yada natara Al'ummah daga kasashe Dana naka jama'ar sai my fito mucekafasa aure matarka yar shan jinice nayi hakuri kamin biyaya zan hadaka da yarinya mai hankali bazaa fasa duk abinda zaayi gobeba tashi Kaje

nayi alwala mutafi masalaci mik'ewa yayi ransa amutikar bace ya ficewarsa " jawa tashi maza kiyi sallah kizo zamutafi gidanku idota dako cikin Saudi ta kalli Abbi kai ya daga mata mik'ewa tayi ta nufi bedroom din shaffah " Alhaji wai dawa zaka gamashi " da jawa zani neman izini gun mahaifinta tin

man tana ta fito su shirya tarbarmu zuwa daurin aure, " to Allah Sanya alheri bedroom suka nufa domin yin Alwala, Ana gala sallah ya kira jawa suka nufi unguwar Asokoro suna zuwa yace ta kira masa dadynta bata jima da shigaba sai GA alhaji murtala suka gaisa cikin mutumci ya janyosa parlour suka zauna" to nazo dawani babban lamarine nazo

Nemawa Abdallah auran jawa " to masha Allah kena su biyu za ahada " ah ah wancan ansami matsalane to in a so anjima a daura da jawa saboda na yana hankalinta kuyi hakuri da yada nazo muku kai tsaye murmushi yayi" wlh ba komai zamu shirts komai kafin zuwa sallah azuhur insha allah ai kaima yar kace far kanwarka uwa daya uba daya" eh to amma kai kakeda

iko akanta bamuba nagode da amincewarka in kashiga ka gayamata ba sai tazo gidaba ta tsaya ta shirts yarinya " to shikenan Allah ya tabbatar da alheri har gun mota ya rakoshi yashiga yanufi gida lokacin har rana ta fara fitowa ya sanarwa da yinma yada sukayi dakansa ya nufi part din soja ya sanar dasji komai da gargadin karya kuskura ya Nuna ko afuska

Kuma duk abinda ya tsara tare da aboka nansa to yayi kar ya fasa ko daya amsawa yayi yana godiya danshi mutumne mai mutikar biyayya kwanci yayi ya dafe kansa da hannu biyu " haka tawa kaddara tazo Rumaisa allah ya isa tsakanina

dake, kafin kaceme mustapha ya hada meeting familys yamusu bayanin komai GA inda auran ya karkata kowa yaso ace yarsa akaba shiko dama gudun haka tasa ya zabi yar mace su Asiya sai tsinewa anty maimuna sukeyi saboda bakin ciki ba y'ayan su bane
--------------------------------------------------

Kafin kaceme labari ya kewaye familys usman Buzun bagayyah Dada sosai tayi Murna tinda tayi sallah take bacci bata tashiba sai karfe goma tayi wanka taxi kwaliya ta fito tayi breakfast mummy tafito cikin shiri " lah mummy yanzu a haka zaki gun jama'a baki zamanki har kije ki haihu a gun sabga " dan

kaniyarki bikin dannawa guda zan zauna bushewa tayi da dariya" to jeki abunki tsaki tayi ta fice daga parlour mik'ewa tayi ta fito tafi kyau har ta gaji part din Dada ta nufa ko ina gidan jama'a ne aparlour ta isko su jameela " ku Ana kuke" wlh kuwa munanan muna farin ciki allah yasa bamu hada jini da mugun iriba bushewa tayi da dariya " a yo dama ai sai mayyar we zai auri mai mugun

Hali kallonta suke hadeeza tace " wlh idan yajiki zaici uwarkine fitsarara kawai jikin Dada ta zauna " Dada ya jama'a ya kikaji da masu Jan kunne " shalelena ai kema buzuwarce tinda hamza ya kawoki duniya ko" a kwarai kuwa amma ai banyi irinsu oh oh da oh oh ba ko Dada Gide bakusha dariya ba allah jiya na dirkawa wani takalmi afuska alquraan bakiga

yada yaji wuyaba ido duk yan cikin parlour suka zaro harda bakin " ke shalelena waye to " hhhhh wani mugune kuma yana cikin gidanan mik'ewa tayi fada bari naje gunsu shaffah tin yanzu mushirya zuwa Dinner din marece danyau ba kama hannu yari biki na mayu Dole mu kwaso shoki💃🏼, duk saida
ta basu dariya dagudu ta fice

part din yinma tashiga duk bakine bata sansuba sosai ta wuce bedroom din shaffah ta shiryawa " yauwa sister dama gunki zani kizo mutafi gidansu jawa dagacan bayan daurin aure sai mudawo muyi shirin zuwa Dinner bata kawo komiba cikin farin ciki suka fito amotar Ramlat suka tafi ita take cikin kwarewa har suka iso gidan dam da jama'a parking tayi suka fito suka nufi ciki a parlour

suka GA momy " momy ina kwana" lfy yarana sannukun da zuwa kushiga ciki dama ita dayace na haka ta fadawa kawayanta saboda korewar lokaci parlour Jawa suka nufa Ana cancada mata kit so da konshi Tasha murjan lalle sai kyalli take zama sukayi shaffah tace " kai antyna haka daga asuba zauwa yanzu kikayi kyau

Fari tayi da ido " ke kuwa ba dole ba tsintsu daga sama gashashe dariya sukayi suka tafa " kai karku rainamin hankali ya naganki Ana mini shiri irin na Amare " au baki saniba shaffah bata hasken abin " kinfa Santa da musu ko na fada mata ba yada zatayi ba ki barta yar gwade ta gwada mata tsaki tana" ku kuka sani yan rainin hankali wayar tace tayi ringing

Screen din ta kalla tayi picking " my Ahmed ya kake " lfy my babyna ya y kk " lau nake Kafa kasance cikin shirin zuwa Dinner da matarka dan ni bazan bi yaraba da mijina zani" ok baby zan shirya kiyimin kwaliya mai kyau fa " ai karka damu sai nazamanto tamkar sarauniya agun my Ahmed Dina " ok sai na kiraki anjima bye" ok bye

Kallonta sukayi atare sukace "mune yaran banza ta musu ta shige bedroom tayi kwanciyata

Bangara. Abdallah ma shiye shirynsa yake saboda cika umarnin mahaifinsa zaune suke da babban Abokinsa Habeeb da sauran bakin Ana hira sai dariya suke suna masa tsiya murmushi yayi yana ciza lips dinsa habeeb yace" ai yau kam zanga wanan Amarya da taciri tota gun Abokina nabeel yace " haka nefa idansa ya lumshe ya

musu banza yana murmushi ta yada bazasu gano damuwar saba, misalin karfe biyu suka gama shirin zuwa gun daurin Aure inda ango yahade cikin dakekiyar shadda getzner fara tass waca aka mata zubin bakin zare gaskiya ya hadu iya haduwa dagashi har abokanansa su naseer ma anci kwaliya da sulaiman Abubakar

anwar Abdullateef nuradeen da sauran mazan gidan gwalin shawa dasu karfe uku daidai suka Kara Asokoro naman jama'a ce dam suna zuwa akafara shiye shiryan daurin aure fitowa sukayi cikeda kasaita ta isa sun maza kowa ya kalli Abdallah sai ya Kara kallonsa saboda yayi wani irin

kyau na musamman motoci burjik agun tamkar kanfanin motoci motocin sojawa ma sunfi guda ashirin sanarwa aka fara badawa daganan sai kabada shadar an daura aure Abdullahi mustapha usman Mani da Jawaheer murtalah maaruf Akan sadaki nera dubu dari biyu lakadan ba ajanaba kafe uku da rabi dadai aka daura auransu

Ihuu gurin ya dauka ko ina sai karan bindigogi ke tashi mutane sai gudu suke Ana ta dariya daurin aurene da ya sami halarta mutane daban daban duk wani mai fada aji tofa yazo daurin auran Abdallah da jawahir bayan sun gaji da harbe harbansu suka kama gabansu dan karfe shida za,atafi Dinner wanda sai dare zaatashi

Su jawa sunacan Ana shiryata bata masan an dauraba sai shaffah ce take fada mata iya Ramlat ko tanacan ta karta bacci jawa harda kukan dadi

Shaffah ce ta shigo bedroom din ta tashi Ramlat " ki tashi muje mu fara shiri kinfasan mune manya kawayanta tashi muje mushirya kar likaci ya kore mik'ewa tayi ta nufi bathroom ta wanko fuskarta " wlh nafa yi bacci sosai " aikuwa dan har an daura aure an watsa " har sunje sun dawo to muyi Sauri mutafi

mushirya fitowa sukayi " kannena sai gida to ai nan zaku dawo fa shaffah tace " itafa tace da Ahmed zata kibarta kawai acan ta maye gurbin babbar kawa " ok ina jiranku banda African tym please hararata Ramlat tayi " kefa kin fiya azarbabi " ai Dole miji a wasa kefa aduhu kike nicefa matar soja " dalla can mai zakiyi dashi " da allah zo muje yar gwade ta gwada fitowa sukayi Ramlat sai masifa take

" to ke ina ruwanki bataji ta iyaba sukarata. Dashi tukinta take hankali kwance har suka iso gida bangaran su Rumaisa hauka take jajir tukuru lokacin da labari yazowa Alhaji lawali haukane baiyiba dan bai taba sanin mugun abun da suke kitsawaba aduniya kusan kashe illham yayi da bugo saida jama'a tan buki suka amsheta

ya mata korakare duk wani dangi na wanan mom kora kare ya masa tafito ko takalmi babu akafarta tana kuka tazo tsalaka titi wata babbar mota tabi ta kanta ko tsayawa baiyiba mutane sun fara taru cikin fitar rai take cewa mutum talatin kadai naci ba yawa malamimu

ma ni na kashashi mutane sunajin haka kowa ya tafi ya barta daket akasami wanda suka dauke gawarta Ana cigiyar masu ita mahaifinta ya gani sarai yaki zuwa sai wasu fan kwarorin motane suka binneta kamar yada akama uwarta Allah kasa mucika da imani

Amma har yanzu bincike ake sai an tabbatar ko ba hannu mahaifinsu haka taron gidan yawatsa Ana ta fadin mugun abunda suke uwa da diyanta

********************************
Chapter 25 · 0% Book details