← Book details Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 99 OF 138

Sashe 99

Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Har barci yayi gaba dani, da safe ina tashi na nufi banɗaki nayi wanka da alola da sallah, na samu an kawo min abin karyawa, naci kadan domin Yazid ya gaya min yau zamu karya tare. A dakin na bar mishi kome nayi tafiya ta bayan na ajiye mishi yar ƙaramar note, don na san sai sha biyu zamu shiga seminar. Don haka na tafi muka karya da Yazid a wurin cin abinci na alfarma. Lokacin da Majid ya je duba ta ya samu ta ajiye mishi yar note. *zan dawo kafin mu shiga mun fita da Sultan*
Bai ce kome ba amma abin yana kona mishi rai, bai wani nuna a fuskarshi ba juyawa yayi ya fita, karyawan da bai yi ba kenan. A daddafe aka gama seminar ni da Yazid kamar kada mu rabu, tunda muka bar Delhi yake dan jana da hira na ga ni ba fahimta nake ba, barci nayi na bar shi. Sai dare muka isa Abu Dhabi, ko awa bamu yi ba muka wuce Nijar, a gajiye suka.kai ni gida, tunda nayi salolin kaina barci yayi gaba da ni.

Tunda ya lura da bana ta, ta shi, aikina da Yazid ne a gabana yasa shi shafa min lafiya. Na kuma kara mai da hankali kan abinda nake yi, wasa wasa wata irin shakuwa ta kullu a tsakanina Yazid, wanda haka kawai zai zo nijar, duk lokacin da yazo sai naga sauyi daga Chairman. Don da wuri nake tashi, kafin shekaru daya kamfanin ya farfaɗo tare da kara bude rassa haka yasa na zama busy, ga yawan baƙin da muke yi a kai akai. Sanadin Amirah SK Lamido ya saka hannun jari a kamfanin Ba'are, sama sama suke mutunci da Chairman don ma yana da kirki shima yasa Chairman yake kula shi. A hankali na fahimci duk namijin da yake tare da ni, Chairman haushinsa yake ji haka ya faru ne sakamakon wata tafiyar da muka yi Nigeria, aka yi taron tattalin arzikin kasa ta nahiyar Afirka, inda aka gayyaci har yan kasuwa da attajiran African.
A lokacin da muka hadu da wani saurayi, ya rako Babanshi gayen nan yayi ta rawar kafa akaina. Bayan an yi taron na kwana uku, gayen nan sai da ya kashe min kudi a ranar da zamu rabu kiri -kiri Chairman ya gaya masa akan idanuna. "Ka daina wahalar da kanka matata ce."
"Ke Matarshi ce?" Bakina sake nake kallon shi. Kafin na samu damar cewa wani abu, Har mun shiga jirgi ya ce. "Ya ishe ki tara samari haka, SK Lamido, Yazid yake ko Ziyad ne oho, ga Amaan maza nawa zaki aura?" Tura baki nayi ina faɗin. "Tow kai meye matsalar ka, ni burina na tara maza ashirin kowa kuma yana sona "
"Hm, haukar banza dai."
Ya faɗa yana kallona, haka muka dawo Niamey, sai mita nake har gida suka ajiye ni na shige ko.sai da safe bance ba.
***
Camp
"Allah ya gani na gama gajiya zan koma Nijeriya idan kin so kada ki tafi ki zauna anan, amma ni zan koma gida wurin Yayana." Inji Ummi tana faɗa dai-dai lokacin da take haɗa kayanta, domin karshen wata zasu bar camp amma Addah take niman su kara rasa damarsu na barin kasar.
Ita kan Ummi ta rantse ba zata kara zama a Nijar ba, idan ita zata zauna ba laifi amma ita zata koma wurin ahalinta.
"Ina haka ne don ke!"
"Karya kike Addah ba don ni kike ba, don kanki kike." Daga haka ta bar dakin. Zuwa yanzu ya dace ace ta san yadda kome yake tafiya, musamman Zulaihah da ita ta dace yanzu ta dauki alhakin kula da ita amma ba hali ko ta koma Nijeriya, babu me kula da ita sama da Zulaihah da Zahrah.

Ban san yadda kome yake zuwa min ba, amma Alhamdulilahi zan iya cewa Yazid tsaye yake a kaina, kasancewar Chairman yau yake kara shekarun haihuwar shi, a gidansu.

Duk da ban wani damu na je ba, amma haka Amaan ya takura min, na dauki Siyamah da Baraka, d Amirah muka saya mishi abin da zamu bashi kyauta raka ni suka yi suma na saya musu. Muna dawowa gidan na ajiye su, "Mami zan bi ki." Shiru nayi kafin Nace musu. "Mujenku dukkan ku." Ai kuwa da sauri suka shiga, Ajiyar zuciya Siyamah tayi. "Wani abu ne?" "A'a!"
"Ma ki taka motar kamar ana bibiyar mu ne!" Kan uban can, da gudu na fisgi motar. Kamar xan tashi sama.

Sai da muka gama gudu, har mun isa gidansu, suka sha kaina tare da harbin tayar motar mu, "Ma! Ki tsaya." Ta fada tana kallon yadda na rud'e. Tura kujerar motar tayi naga ta ciro bindiga, tsoro ta bani."ku kwanta" ta fada da karfi ta sauke gilashin motar nan, ta fara sakar masu harbi kan me uwa da wa bi, ban tab'a ganin tashin hankali ba irin na yau. Rike hannunta nayi . "Bar harbin, ni suka zo dauka shi yasa basu harbe ki ba." Na fada ina kallonta, don tun fara harbin tartsatsi wutar motar na hango fuskar........
300₦
0016341139 unity bank zahra'u yahaya Ali
Katin MTN 400
#Mai_Dambu ce
[5/29, 07:47] Hlm: BHB253
Tabbas ko a cikin dubu Nawwas ba zan tab'a mance fuskar shi ba, haka yasa na dakatar da ita domin kuwa idan ta fusata shi ba zai tab'a kyale mu ba, duk sai ya hallaka mu. Anyi Y'a kwance uwa kwance kenan. Bude motar yayi ya fito yana zukar tab'a. Ya iso har gefen driver ya kwankwasa min glass, yana murmushi sauke glass din nayi ina me tausayin kaina. "Fatimah nan kika dawo?" Hawaye ne ya zubo min. "Nan Yazid ya kawo ki, sai gashi bai iya boye min ke ba, kin samu rayuwa me kyau kin manta da danginki."
Ni dai ban iya magana ba, sai dai shiru murmushi yayi sannan ya cigaba da cewa. "Haka ma yayi ai,fito muje Gimbiyata."
Ba musu na saka hannu zan fita Siyamah ta rike ni. "Sultan zai yi fushi idan ya ga ina raye ke kuma bakya nan." Murmusa mata nayi na ce mata. "Ki gaya mishi nasan zai zo ba zai miki kome ba." Haka na fito daga motar ya rike sigari da daya hannu me lafiyar. Shi kuma dungulmin ya saka a bayana ya nufi cikin motar da ni."Maminah ku kai ni Mamina." Inji Amirah. "Wow Yar wurin Zuzu kenan? A dauko min ita."
Cikin tsananin tsoro na ce mishi, "kayi hakuri kada ka cutar da ita bata da laifi ni ce mai laifi." "Har yau kina nan da son naki, koda yake ba laifi ba ne, kaso naka." Haka ya saka ni a motar, tunda muka isa na kifa kaina, ina wani irin kuka, kafin Yazid yazo daga Algers na mutu murus, shi wancan sikagon ba wani abu zai iya min ba, haka yasa nake ganin Allah yasa wannan tafiyar ta zama ajalina na gaji da abubuwan da suke faruwa da ni.
"Ya isa ba kuka zaki yi ba." Ya fada min, ban iya kula shi ba, kuka na cigaba da yi.
... Siyamah a daren ta kira Yazid, ta gaya mishi abin da ya faru ta dauka har da number motar da suka dauki Zahrah. Kiran Office din Embassy na Algers da yake nan nijar yayi ya shaida musu.
Chapter 99 · 0% Book details