← Book details Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 138

Sashe 27

Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Allah ba zai tab'a barin addah ba, domin daga duniya zata ga sakamakon abinda ta aikata. Wallahi nayi dasananin abin da na aikata, Zuzu akan idonku aka keta alfarmar Mahaifiyata, aka keta nawa maza sun fi shida akan Yakumbo, Zuzu Gaya min har zan ji wani d'a namiji ya burge ni? Gaya min anya akwai adalci a cikin wannan yanayin? Mahaifiyata fa suka lalatawa farinciki bayan sun kashe kannena da mahaifina da kowa nawa.

Zuzu me Addah take so nayi? Bayan na gama ganin masifa da idanuna zata bukaci na kara hada shimfida da wani d'a namiji, tsoro nake ji Zuzu ina tsoron Allah kada ya kona ni." Rungume juna suka yi. "Babu wanda zai kuma saka ki dole, koda bana nan kada ki gayawa Zahrah kome ki barta ta fahimci abinda ya faru da kanta, kada ki gaya mata don Allah."
"Wallahi ba zan iya ba, matukar na ganta cikin wani yanayi zan gaya mata. Amma zuzu me yasa kike gaya min haka?" Murmushi tayi tace mata. "Ba kome kawai dai na gaya miki ne kada ki gaya mata kome."
Suna zaune addah suka shigo da kayan ciye-ciye, itama Zuzu ledar da tazo da shi, ta bude suka ci abincin da Ummi. Sai da ta gama cin abincin, ta kalli Munaisah. "Ita baiwarki da kika bari a can Asibitin me kike nufi?" Kallon Addah tayi, tana son tayi magana amma ganin har lokacin Zuzu bata yi magana ba, yasa Addah kasa da kanta. "Zaki tashi ko sai naci Bu..... Ubanki." Inji Zuzu tana mikewa. "Doluwa jaka!" Mikewa Munaisah tayi kamar zata mutu, ta dauki kayanta. Itama zuzun ta mike tana bayan Munaisah, tana kare mata zagin kare dangi, har asibitin don masifa Zuzu ta kawo ta, ina zaune kamar wata mara galihu, sai ga su nan mikewa nayi ina kallon yadda Munaisah take share kwalla. Domin a duke zasu daku da Zuzu, amma kuma Zuzu irin mutanan ne masu matukar kwarjini domin yar bala'i ce.
"Meye na kuka?" "Rabu da shegiya ba zata zo ba, wai har tana kuka yar iska Uwarki ce, ba Uwarta ba."
Girgiza kai nayi na cewa Zuzu. "Tunda bata son zama ta koma, ke mu kwana dake." "Wallahi ba zata koma ba, idan ta koma ma wurin wani shegen zata kwana." Sake baki nayi ina kallonta, "wurin wani shegen zata kwana?" "Wallahi na rantse miki da Allah, kwana zata yi a wani wurin."
Mikewa nayi ina karkad'e jikina na ce mata. "Ok sai ki zauna. Ai kin san yadda ake kome ke muje!" Daga haka muka bar asibitin, raina yana b'aci. "Kin san Ummi da Addah sunyi faɗa?" "Ina zan sani, tunda ina asibiti."
Murmushi tayi tace min. "Hmmm! Allah abin tsoro rayuwa abin tsoro, yau wai Ummi ce take gaya min Addah ta sakata aiakata abubuwa masu kazanta, yanzu ta tuba ta bi Allah ba zata kuma bin maza ba, asalima tsoron mazan take "
"Alhamdulillahi Allah ya amshi addu'ata, akanta kenan, tunda gashi nan tana faɗin ta tuba."
Murmushin karfin hali tayi ta fara bani labarin yadda aka yi, ware idanu nayi ina mamakin yadda ta iya dauke kai kamar babu abinda ya faru. "Me yasa baki damu ba?" "Kawai ba zan tab'a damuwa ba, domin kare rayuwar Mahaifiyarta tayi, kuma ko kashe addah tayi bata da wani hukuncin." "Amma!" Rike hannuna tayi tana faɗin. "Addah tayi kurakurai, kada haka ya zama abin da zaki bi bayanta, barta da halinta bata ga kome ba." Ta fada tana sauke ajiyar zuciya.

Ban san me yasa haka yake faruwa ba, amma nasan Addah tana da kaso mafi girma na lalacewar rayuwar Ummi, lokacin da muka isa da Balali muka haɗu tunda ya ganni yake murna, sama sama na gaishe su, muka wuce koda muka isa kallona Ummi tayi ta ce mana."me yasa kuka bar ta a can Asibitin?." "Mahaifiyarta ce duk abinda ta gadama tayi, rayuwar Nenne yana hannunta, ta ce ko ta samu damar kawar da ita, zata yi ga damar nan na bata na dauko Zahrah da ta tare mata damar." Inji Zuzu tana dafa kafadana. "Ban gane ba?" "Ba zaki gane ba." Hadiye yawu nayi wato idan na fahimta akwai abin da ake boye min, kura musu idanu nayi da na fahimci basu son na fahimci kome, sai na zauna ina faɗin . "Yau baku mana abinci ba ne?"
"Tun tafiyarki jiya babu wanda ya kara abinci sai Zuzu." Inji Ummi, mikewa nayi na dauki sauran kayan abincin, na fara kokarin daurawa, sai ga Uwar Mugu da wasu matasa uku, kallonta nayi kafin na mike ina son nayi magana. "Ina Munaisah?" Tana asibiti wurin Mamarta. "Me yasa bata zo ta gaya min ba?" Daga ciki zuzu ta leko tana faɗin. "Bata zo ba, domin can ya dace da ita ba nan ba." "Ke waye ya saka ki?" Daya saurayin zai shiga cikin tantin na tare shi, "wai meye haka ne?" Na tambaye ta. "Kyale su ku tawo da Aina'u " haka suka wuce ina kallonsu, juyowa Uwar mugu tayi tana kallona, fuskarta a sake. Ta bar wurin a can kuwa tana shiga dakinta, ta ce . "Yallabai yarinyar tana asibiti wurin jinyar Mamarta, amma na saka a kawo min Aina'u."
Gyad'a kai yayi yana kallon wayar hannunshi. "Me yasa bata gaya min Uwarta bata da lafiya ba?" "Afwa Yallabai."
Haka aka tawo da Aina'u da ta cab'a kwalliya kamar zata wurin gasar kyau.
★★★
Niamey. Niger republic
*Familyn BA'ARE*
Alhaji Muhammad Dan Ba'are, su ɗin dangi suke da Ibrahim Khalil Dan Ba'are (na cikin Bororoji) kakansu daya, kasancewar sun jima da barin agadaz, haka yasa su sai suke amfani da Ba'are zalla, yayin da Khalil yake amfani da Dan Ba'are.(zaku iya bincikar Bororoji duk da ban fito da nasabarsu ba, amma labarin BAƘIN HAURE da Bororoji yana da nasaba da juna)
Alhaji Muhammad Dan Ba'are, ya baro gida agadaz domin karatun addinin Muslunci, ba don kome ba sai don yadda Mahaifinsu yake fifita wasu ɓangaren na gidan da su, shine d'a na farko a gidan, sai Alhaji Ibrahim Dan Ba'are d'a na biyu, sai Hajiya Latifa, Mahaifiyar Mohan.

Kasancewar su dakinsu Ibrahim sun maida hankalinsu akan karatun boko, yayinda Mamman Ba'are yaki boko ko kadan, haka yasa shi ganin ai ana fifita yaran dakinsu Ibrahim, mahaifiyasu an maida ta kamar saniyar ware. Dalilin haka ya bar gida, ya tafi karatu a can ya hadu da wani abokanshi. Suka wuce kasar mali.

A can suka shiga harkar hako ma'adinai, har na tsawon shekaru biyu, ana haka wata rana, kasa ta rubta musu sai da suka kwashe wata goma sha huɗu, kafin aka fito dasu, a kasar nan shi daya ya rayu sun kai su goma sha takwas da suka shiga amma shi daya ya rayu, a lokacin da aka kai labarin Mutuwarshi, Nana sai da ta kwanta jinya da tsanar kishiyarta Hajiya Balaraba, da ganin kamar ita ta mata hanyar da d'anta ya mutu, gaba da kiyayya me zafi suka kara ruruwa a Familyn Dan Ba'are dalilin da yasa suka bar garin agadaz kenan.
Shi kuma a can ya rayu cikin amincin Allah, domin a tsawon watanni nan. A ramin nan da suke hako kuza, a nan yayi katarin haduwa da dutsen zinari, haka yayi ta hak'a, bai fasa ba Abinci sai beraye su yake kamawa ya buga gwal da kuza, wuta ta kama, ya gasa beran da ya kama. Ruwa yana samun shi ne ta wata jijiyar bishiya da ta ratsa karkashin kasa.
Haka yayi ta rayuwa, kwatsam sai ga shi ana tono, inda cikin hukuncin Allah aka tono da shi, ya tara dukiya me yawan gaske sannan aka fito dashi. Wannan abin ya bawa kowa mamaki, asibiti aka wuce da shi yayi sati biyu aka sallame shi, tare da kayanshi baki daya da ya hako a rami.
Aka dawo da shi Nijar, Aka karrama shi gwamnati ta bashi babban gida da fili anan Niamey. Sannan gwamnatin ƙasar ta nemi ya sayar mata da abinda ya zo da su, ya sayar da kadan domin ya gina dukiyarshi saboda kusan rayuwarshi ya saka a hatsari ya samo dukiyar nan.

Kad'an da ya sayar din nan, da ita ya cigaba da gina katafaren kamfanin zinari, har ya kuma haɗa gwiwa da kasar Mali ana shigo mishi da zinari, a lokacin bai wani karatun boko ba, amma kuma ya san kan lissafin kome, sai da ya samu shekaru uku da dawowarsa ya tafi ya nimo Danginshi. Ganinshi cikin wadata da nutsuwa yasa suka ta murna, har agadaz ya je domin an san ya mutu dole yaje ya nuna kanshi dan su san yana raye.
Yana zuwa Kanin mahaifiyar shi ya bashi auren Yarshi, Rabi duk da bai so ba amma haka ya amshi auren, domin yana niman macen da tayi karatun boko wacce zai ciccibeta ya dorata akan dukiyarsu, haka aka sha biki.

Tana shiga a burin shi tana fara haihuwar namiji, zai gina rayuwar yaron ta hanyar bashi ilimi me yawa da zai rike dukiyarsu. Sai dai kash tana fara haihuwa ta haifi mace, haka ya kara auro Fauziya itama tana shigowa mata ta fara haifa masa, haka ya hakura ya cigaba da kula da yaran da basu ilimi sai dai iyayen basu wani damu da ilimin ba, ana haka ya hadu da Harirah yar secondry haka yayi ta mata hidima, har ta gama itama dai ba wani abin kuzo ku gani ta yi ba,haka ya aureta.

Alhaji Mamman Ba'are, yana da wata dabi'a ita ce cacca, dake yana yawan shiga libya, a nan ya haɗu da Alhaji Nasiru Wodabbe shima rikakken dan cacca ne.

"Yau gidan nan yayi baki,ga Alhaji Nasiru Wodabbe gefe guda Alhaji Mamman Ba'are, yau wasan sai tafi koda yaushe armashi da karsashi" domin kowa yasan kowannensu gwani ne a harkar cacca.
"Idan nayi nasara akanka Ba'are me zaka bani?" Murmushi Mamman Ba'are yayi ya ce mishi. "Wodabbe idan kayi nasara a kaina, ka kwashe kome har da kayan jikina. Idan nayi nasara akanka kuwa zan bika har garin na dauke shanayenka!"
Chapter 27 · 0% Book details