← Book details Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 135 OF 138

Sashe 135

Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ina son Mamana, wallahi babu ruwanta kankaro min mutunci take ta ko wace fuskar, Bayan mun isa Kamaru naga likitan kunne an bani abin jin magana, sannan muka dawo, ina ganin ta hada dilke ta saka ni a gaba tana gyara min jiki. "Munafuka, kina nunawa babu ruwanki, nan kuwa nasan har kuka ke yi kina jin haushin na raba ki da mijinki. Ja'ira ya tafi tsawon shekaru uku, kina tsammanin baya son dadi ne, wurin za a kara gyarawa mutuncinki ya cika idanunshi. Ya gane ke daban ce a cikin mata, na lura har wani hura min hanci kike to na ga bakaloji."
Tana fadar tana zungure min goshi, ni dai ban ce mata cikanki ba, sai dariyar da nake mata, wato gyaran da tayi min wallahi har wani ji nake iska na shiga jikina, ko ina na jin shi nake zam-zam kamar bani ba, a sati biyu na yi kyau na ciko ta ko ina, a ranar da na cika sati Uku a ranar ya diro ranar juma'a, ina can gidan lalle, an gyara mana bangaren mu. Sai kamshi yake daga gidan lalle da suke har saloon aka min, ko ina na jikina Masha Allah jiki duk Madara.

Muna dawowa, na hango shi tsaye jikin motar Malam, yana waya ya saka wani farin yadi na maza har ina iya hango farin singlet din cikin. Dauke kai nayi na zo xan wuce ya ce min. "Fulani ba magana ne?" Murmushi nayi nace mishi. "Barka da hanya baban Alfah!" Na wuce abina, bina yayi da idanun yana fadin."ji mana." Tsayawa nayi ina kallon gabana, jikina rawa yake, kasa ƙasa yace "Kinyi kyau sosai." Ya durkusa a gabana, abu ya ciro a cikin aljuhun shi ya saka min kamar sarka. "Ina son ganin mace da sarkar kafa, kuma nasan yadda ƙafafuwan nan sukaji lalle zai yi kyau." Murmushi nayi mishi, sannan na wuce cikin ban ce uffan ba, lokacin da na shiga cikin gidan Mama kallona tayi yana biye dani. "Ya kake binta!"
"Amma Inna mata ta ce?"
"Allah ko?" Ta tambaye shi tana d'aga mishi gira. "Yaushe muka fara wannan wasan!" Yadda tayi maganar babu wasa yasa nima na kalleta.
"Ya za ayi wasu daga cikin yan uwanka basu son kurma bayan nasan ba haka na baka Zahrah ba, ya xa ayi domin nima ba zan yarda a kuntatta mata ba! Kamar yadda kaima danginka basu so a kuntatta maka, Ina son Zahrah kuma ba zan bari a mata wani abin ba, Tow ya zamu yi don naga wasu suna ganin kamar ta zame maka lalura zaka yi maneji da ita ne kawai."
(Ya kuke ganin abin da Mama Amina take shirin yi zai haifar da d'a me ido ko yayya?")
300₦
0016341139 unity bank zahra'u yahaya Ali
Katin MTN 400
#Mai_Dambu ce
[5/29, 07:48] Hlm: BHB278

Sakin baki nayi ina kallon baiwar Allahn nan, kafin na ce. "Mama!" A wani fusace ta juyo min, jikina ya dauki rawa kar-kar domin bata taɓa min ko kallon banza ba, "ki b'ace min da gani kafin na mugun saɓa miki!" Da sauri na bar falon, yadda naga fuskarta babu wani sassauci. Yadda take cika tana batsewa ya kara saka Majid rud'ani da tashin hankali. "Inna fisabilillahi." "Ungo nan kaniyarka" ta masa dakuwa da hannu bibbiyu. "Kaci kaniyarka." Ta fada da karfi, kafin ta gyara zama ta ce mishi. "na fasa baka Zahra, maza maza ba yau ba. Ba gobe ba don gobe ta Allah ce maza ka yanko min takardar ta, idan kanwa ce zan jika abata."
"
A kidime ya mike jikin shi yana rawa, "wallahi ba zan iya ba, gara a kashe ni akan na saki Zahra!"
"Tow kuwa sai dai ka mutu, wato har ana tuna maka ta kurmance akwai mata masu ji. Akan waye ta samu lalurar?" Kamar an saka mishi shocking, kamar zai yi hauka fir Mama ta ki kula shi ta ce mishi. "Na rantse da Allah ba zan baka Zahra ba, sai an hadu family idan kana ganin wasa ne Bismillah ina ku Yayan Idanu ne, Ya Sa'a bata iya tsawata.muku? Tow b'ace min da gani ka fita ka bar min gidan Ubana, kamar yadda Anisah ta ce gidan Mamman Ba'are gidan Ubanta ne fita kabar min gidan Ubana duk lokacin da kayi arzikin gidan kanka danginka suka san darajar Y'ata zan zauna da kai."

Har ta wuce ta juya a fusace ta ce mishi. "na fasa zaman family wallahi kada na kara ganinka a wurin Y'ata ka saketa domin na mata mijin da zai zauna da ita da kurmanta maza nan da 48hrs ka kawo min sakinta."
Kaf gidan babu wanda ya goyi Bayan Majid domin duk abinda ya faru, Barakatu ta gayawa Mama ashe ni ban sani ba, Cidi aka hada ni da ita, ni ina zaune da ita tsakanina da Allah ashe ita aikin Mama take, ban sani ba. Dakyar na danne fushin da yake raina, amma Mama ta bani mamaki koda yake Zaytoonah munafuka ta ce min ganinta nake haka, ko Hajiya bata tab'a marin Majid ba amma Mama ta watsa mishi mari. Ina zaune har dare sannan ta shigo inda nake matar nan bata kalla ba. Tayi uzurinta ita da Jikarta suka kwanta suna hira tana bata labari da tatsuniya da hirar duniya kafin naji yarinyar tayi shiru, ina jin tana mata addu'a ta tofa mata. Ina zaune kan Sallaaya ta ce min. "Na b'ata miki rai ko? Na batawa mijinki rai ko?" Gyara zama nayi tare da cusa kaina tsakanin cinyoyina. Hmmm na zata rarrashina zata yi tare da bani hakuri, a'a bata yi haka ba, bata kuma ji a ranta tayi hakan ba sai ce min tayi. "Don Uban mutum idan ya fasa jin haushina na karci hancin uwar Mutum;" ta faɗa tana tsare gida saboda yadda na d'ago da sauri ta kuma sake hada rai. "Eh na fada din, kuma wallahi ko da wasa naji an ganki da Majid sai na ci ubanki don uwarki, mara zuciya da rashin sanin ciwon kai idan ba rashin sanin ciwon kai ba, ina ke ina jin haushina. Ke ki mutu akan kowa ke ba zaki samu me sumewa akanki ba, kuma kika min kuka na tashi na ci Uwarki."
Wani irin tsoro ne ya kama ni, na ja bargo na gyara wurin kwanciya na kwanta, ina ajiyar zuciya. Har barci ya dauke ni.
Kafin tayi wannan borin, sai da ta samu iyayensu da Yayunta manya uku ta gaya musu halin da ake ciki, ta ce musu idan bata tsayawa Zahra ba, abubuwan zasu yi yawa ga rashin kunne ga cin zarafi a gaban kowa kuma Sa'adatu bata ce kome ba shi ma Majid bai yi magana ba, ta ce ba zata iya ba, ba zata kashe musu aure ba. Amma don Allah a kyaleta ta taya Zahra, da Uban Zahra yana raye ba zai barta haka ba. Wannan yasa kowa ya goyi bayan Mama.

Kuma ba karya babu b'ata lokaci, ta hana ni ganin Majid ko tsakar gida bana fita, abinci ma daki ake kawo min, wani lokaci ina jin Muryar shi da Yarshi amma babu yadda na iya nasan yayi kewata domin kuwa a yadda yake bawa Yafendo da Goggo Sume hakuri suna yab'a mishi magana zai baka tausayi, idan Mama bata nan.zama nake naci kuka na wanke idanuna.

Wasa wasa tun yana bin kakanninmu har ya fara sarewa, Malamijo da ya samu da maganar murmushi yayi ya ce mishi. "Kasan Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya tsayawa Yarshi Nana Fadimah da mijinta Sayyiduna Ali zai auro yar wurin Abujahal ? Yace bai yarda ba, kamar yadda Nana Fadimah bata yarda ba shima.bai yarda a yiwa Yarshi kishiya ba, kasan sayyadi Ali bai kara wata matar ba sai bayan mutuwar Nana Fadimah Allah ya kara mata yarda. Don haka ina bayan Aminatu tayi duk yadda take so, Yarta ce mu tayata zamu yi."

Haka ya tafi gidan Kawu Gidado, shima kiri-kiri ya ce "ai Aminatu tana kan Daidai shima uwarsa ta tsaya mishi balle marainiya da bata da uba bata da kowa don bata da arziki ba yana nufin bata da me tsaya mata bane, Ummi, Kai babu wadanda basu zo ba har zuzu da Mijinta. Family ya hadu bakiɗaya. Ranar Alhamis muka fara amsar baki har ranar asabar, ranar Lahadi aka fara meeting. Kafin a fara meeting din sai da aka so raba raini tsakanin Munaisah da Anisah da Zuzu. Suka nime dukarta saboda habaicin da take yada min. Na cewa. "An samu wuri ana zuba iskanci, dadin abu dan uwana aure zai kara mace me ji da magana a hankali."
Shine suka mike tare da rufe ta da duka, na shiga tsakaninsu, ture ni tayi na hada kai da cabinet na kitchen, hayaniyarsu ya janyo hankulan mutanen gidan aka shigo da sauri ana tambayarta.
"Waɗan nan yan iskan karuwan ne zasu shiga tsakani na da Zahra don kawai ina..."
Kifa mata mari Mama tayi sai da ta gigice, bata kuma dawowa hayyacinta ba, ta ƙara kifa mata wani tana fadin. "Yaran nawa zaki jifa da kalmar karuwanci?" Matar Kawu Gidado ta riƙeta. "Haba Amina fadar yara ne."
"Bu... Ubanta, don ubanta ni zata kawowa rashin mutunci. Shegiya ta kasa zaman gidan mijinta zata saka yara a gaba, naji karuwai ne baki ga zaman gidan Aurensu suke ba jaka jahila."

"Amina wani irin magana ce haka, zaki zauna kina cin mutuncin Anisah akan Yara...." Fusace Mama ta juya tana kallon Hajiya da ta kasa karasa maganar bakinta. Wai idan kasan na fada baka san na maidawa ba, wani irin tashin hankalin da ba a tab'a yin shi ba, domin Ni kan daki na wuce na rufe kaina, Majid rike kanshi yayi kamar ya fasa ihu.
Chapter 135 · 0% Book details