← Book details Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 138

Sashe 33

Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Sannan a gefe guda ta mallake Nana sai yadda tayi da ita, kuma bata da katabus sai Abinda Tani ta ce, ana haka ta saka Alhaji Mamman a gaba ya saka mata danta Sajjid a makaranta tare da gaya mishi duk abinda yake so Sajjid zai mishi, ba sai ya damu da Abdul ba, fatanta kawai ya saka Sajjid a cikin Yaranshi. Amma mutumin nan yaki kula zancen. Idan ta dauko zancen zai ce mata yaji kawai don ta rabu dashi amma a ranshi baya jin zai yarda ya amshi Sajjid domin ba jininshi ba ne.
Haka tayi ta kokarin lallai sai yaron, ya zama wani abu kai babu wanda ya isa yayi mishi fada balle tsawa. Ga rashin kunya da fitsara.
****
Tunda suka dawo ta fara laulayin cikin Jamilah don ma babu wani wahala, amma kuma tana yawan kwanciya. Saidai da sauki,haka taci gaba da rayuwa har Allah ya sauketa lafiya, ta samu yarta mace, Kyakyawa da ita, haka yasa ta saka sunan Yafendo Jamilah.

A lokacin ba laifi abinci da sakon yana samunta, haka tayi ta renon Jamila, amma ta turawa Alhaji Abubakar Abzin sakon ta haihu, shi kuma ya turawa Alhaji Mamman Ba'are, bai bi ta kanta ba, sai bayan shekaru biyu, rabon Anisah ya kaishi Kano, a lokacin Abdul Majid ya kusan gama primary, a wannan zuwan da yayi ne. Ya kama yaron ya mishi mugun dukar da ya suma saboda kawai an kawo kararshi wai ya dauki kudin wani me shago, ya mishi wannan dukar, ya tura shi gidan horar da kangararun Yara,. Wani abin tashin hankali ya dauke Hajiya da sauran Yaran suka koma Niamey. Suka bar Abdul Majid, da yayi fama da jinya ga cutarwar yan gidan, duk wanda ya fika ƙarfi zai zalunce ka, sannan yara ne masu banbancin hali, har da marasa jin magana masu luwadi, sai dai tunda suka barshi Hajiya ta bar amanarshi a hannun Maman Luba. Tana can amma addu'arta bai daina sauka a kanshi ba,

Sai da ya kwashe shekaru goma har ya zama kaman dan gida, anan ya gama primary school da secondry school, yayi jarabawar shiga jami'a, ƙoƙarinshi yasa shi samu tallafin karatu a wurin gwamnatin Kano, anan ya tsaya ya karanci bangaren likitanci, tsawon wannan lokacin, Hajiya tana marad'i, tunda Alhaji Mamman ya zubasu yayi tafiyarshi, Alhaji Abubakar Abzin shine kome nasu, har ta haihu.

Dukkan Yaran sun san Majid amma Anisah bata san shi ba, sai labarinshi. Zamanshi a gidan horan Yara, ya kara maida shi wani irin mutum mai murdadden hali, sannan baya hmm baya Humm. Dole yasa yake zama a cikin aji, amma baya son hayaniyar mutane ko kaɗan. Idan dare yayi kuwa baya barci domin idan ya fara barci zai ta mafarkin Babansu yana dukar Hajiya. Haka xai bude idanu, sau biyu yana faduwa a aji, a duk ranar da yayi mafarkin tow zai fadi ya suma sai washe gari don bai samun isasshen barci.

Ganin haka zai shafi karatunsa, yasa shi fara ganin likitan kwakwalwa, aka fara duba shi, domin har dawanau aka tura shi. Lokacin da suka samu hutu, ya shirya ya tafi marad'i da tambaya da kwatance yaje gidan Alhaji Abubakar Abzin, Aryan yana kofar gidansu na maradin ya hango Abdul ba zai manta da shi ba, da gudu ya tafi ya rungume shi." Hammayo;" murmushi yayi ya kara rike shi suka nufi cikin gidan, ya kawo musu tsarabar Kano. Hajiya da ta ganshi, juya baya tayi tana kuka. Murmushi yayi bai ce mata kome ba. Ya zauna kanshi a sunkuye. Haka ta shiga daki Jamilah ta fito ta ce. "Hammayo kai ne" ta zauna a kusa dashi tana washe baki . "Yafendo kin zama yan mata " "sai buhun rashin mutunci." "Hammayo kaga Hamma Aryan ko?" Tashi yayi ya shiga dakin Hajiya, ya same ta a can kuryar dakin tana kuka. Zama yayi gabanta. "Hajiya ko daidai da rana daya ban manta daku ba."
"Amma ai na manta da kai!" "Hajiya nasha mafarkin kina sallah kina min addu'a da wannan na yarda a zuciyarki ina tare dake."
"Alhaji baka yi fushi ba?" Girgiza kai yayi yana murmushi. "Hajiya kina karkashin mijinki, a kaina ba zaki kashe auren da na bude idanu na gani ba." Hawaye ne ya zubo mata danta dan kimanin shekaru goma sha takwas. "Gobe zamu je Niamey."
"Hmm! Allah ya kai mu!" Ya fada.
Haka ya fita ta kawo mishi abinci, kannen suka zagaye shi, suna bashi labari can sai ga Anisah ta shigo tana kuka."Hajiya!" "Na'am Auta."
"Hajiya Hamma Amaan ya kwace sauran canjin."
"Allah ya shirya min ku baki daya." Ta amshi sakon, ta ajiye a kitchen. "Hajiya Ina hamma Aryan?" "Suna cikin daki Hammayonku ya dawo." Da sauri ta shiga Dakin, ta d'aga labule. Kura mishi idanu tayi idanunta cike da kwalla. "Hammayo!' bude mata hannu yayi, da sauri ta isa gareshi tana kuka. "Hammayo ban sanka ba, amma Hamma Aryan kullum sai ya bani labarinka." Murmushi yayi yana kallon Aryan. "Ya ce miki ina sat.." rufe mishi baki Aryan yayi. "Alkhairi nake gaya mata, yarinya ce bata san sharri ba please."
"Hamma Amaan yake gaya min wai sat..." Rufe mata baki Jamilah tayi. "Ke dai akwai bakin allatsine, idan kika bi na wancan sakaran sai an daure ki igiya tayi saura."

Domin daga Jamilah har Aryan basu shiri da Amaan,.kamar wuta da auduga. Mikewa yayi suka tafi masallaci, suna dawowa suka samu Hajiya tana kokarin tuka tuwo.. "Hajiya bani na miki?" "Yau.girkin maza zamu ci?" Ta tambaye shi, "zamana a gidan Horon kangararrun Yara, yasa na rike bangaren girki har gasar girki muke " ya faɗa a sanyayye, Duk da cikin raha yake maganar amma fuskarshi bata nuna haka ba, yanayinshi babu yabo babu fallasa, suna zaune ya tuke tuwon ya kwashe tas, yana gamawa wata mata ta shigo kawo kar'ar Amaan. "Maman Jamilah ina jin kunyarki, ki jawa danki kunne wallahi ya fita harkata da yarinya ta."
"Kiyi hakuri;" shine abinda Hajiya ta faɗa, sannan matar ta fita tana zage-zage. Can kafin magariba sai ga Amaan, ya shigo yana zage zage da rashin kunya. Kallon Abdul yayi ya ce mishi. "Barawo ka dawo ne?" "Hammayo muje masallaci!" Inji Aryan, domin a cike yake da Amaan babu ranar da zata waye ba a kawo ƙarar shi ba, "Kai dan shegiya da kai nayi?" Wani irin mari Abdul ya kifa mishi, a wurin ya zube yana nishi, "kayi yadda kake so, idan kaso ka fadi abinda yayi maka. Amma ka sake ka zagi wani cikinsu sai na cire ma hakori."
"Hajiya kina ganin barawon danki zai kashe ni." Alola yayi ta wuce daki, shima ya wuce dakin. A masallaci Aryan yake bashi labarin abinda yake faruwa, sannan wani abin tashin hankalin shine duk bayan wata biyu Hajiya xata kwashe su har Niamey, su je can ayi ta wulakanta su ana ganawa Hajiya azaba da masifa.

Lashe baki yayi yana jin daci a ranshi, haka sukayi sallah sai bayan Isha suka dawo, tun a kofar gidan suke jin muryar Jamilah, Hajiya tana gefe bata yi magana ba ta xuba musu idanu Amaan sai dukanta yake. A fusace Aryan ya nufi Amaan Majid ya rike shi, "sake ta!" "Idan naki fa?" "Aryan wuce da hajiya ɗakinta!" Ai dama ganin hajiya a wurin zai saka ya kyale shi, sai gashi cikin fushi ya kai mishi wani irin duka a kafa, dauke wuta yayi wato Majid zama gidan horon nan ya koyar da shi mugunta sala sala. Targad'a shi yayi ya ce mishi. "Kafin ka warke ka fara fita zaka fahimci muhimmancinsu, idan ma baka horu ba, akwai hanya dayawa da zaka nutsu."
Haka ya wuce da ita daki, yana faɗin. "Kin mishi rashin kunya ne?" "A'a Hammayo, kiranta yayi tana sallah shine tana idarwa ta fita ya kama dukanta da hajiya tai magana yace babu ruwanta."
Cizon fatar bakinshi yayi yana jin tafasa a ranshi, a daren Aryan ya gyara dakinsu, da Inda Hammayo zai kwana. Haka suka kwana suna hira, sai asuba suka yi barci.. wurin karfe goma motar kai su Niamey tazo, suka tafi sai cika Amaan yake yana batsewa. Har suka isa gidan, wanda daga kofar gidan zaka fahimci ana sha'ani ne.
Chapter 33 · 0% Book details