Sashe 79
Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
A ranar da kamfanin Ba'are suka zo, sun yi amfani da score din mu na kowace semester ne, haka yasa ina zaune aka kira sunana, kamar wacce aka tsikarawa allura haka na mike ina zare idanu, "Ni Zahra Abubakar?" "Eh ke." Mikewa nayi tare da bin bayan masinjan Den, a hankali nake tafiya ina tattare hijab dina, har Office ɗinta.
Lokacin da muka isa ni daya na shiga office din, manyan mutane ne a cikin office din idanuwansu ya dawo kaina,kunya kamar na nitse a kasa, "Shigo ki zauna!" Aka ce min, haka na samu wuri na zauna ina zare idanu. "Zahra Abubakar." Gyada kai nayi, kafin suka cigaba da tattaunawar su, "Za'a a tura ki kamfanin Ba'are, kuma dama muna neman kwararru akan kasuwanci da kuma tattalin arziki, shin wacce gudummawar zaki bawa kamfanonin mu."
Zufa ce ta karyo min muryata na rawa na ce musu, "Zan yi iya kokarina domin na bada iya gudummawar da zan iya, wannan shine kawai abin da zance."
"Bakya da wani fata ne ga cigaban Kamfanin?" Murmushi nayi sannan nace musu, "Fatana zai tsaya ne akan abinda ya kai ni, na gama lafiya na dawo makaranta lafiya"
Kallon juna suka yi kafin suka ce min. "Kafin yau kin tab'a aiki da wani kamfani?" "A'a ban tab'a ba, wannan shi ne karon farko da zan fara." Shiru suka yi sannan suka ce min. "Idan har muka ga kwarewarki zamu dauke ki aikin dindindin." "Ina me farincikin jin haka, ni kuma xan yi iya kokarina akan aikin."
"Allah ya bada sa'a."
"Amin na gode!" Na fada ina mikewa, bakiɗaya sai naji babu wani shakka a raina, domin kuwa wani irin nauyi ne da aka sauke min nake ji, haka yasa na wuce aji. Fitowa ta na hadu da Kashim daya daga cikin abokan Abdullahi, kamar maye duk da ya gama makarantar amma ya mai da makarantar gidan Ubanshi, "Kizo ga Sauban can mota ta buge shi." Amadadin na wuce aji sai na tsinci kaina da faɗin. "Innalillahi'wa'inna'ilaihirraji'un, garin yaya yanzu na fita na barshi a aji fa." "Eh " yayi gaba ina bin shi a baya, abin mamaki mu da zamu bi cikin mutane sai gashi ya kusa ta cikin lungun makaranta, ganin haka yasa na juya tare da cewa. "Ba zan bi ka ba, idan ma turo ka aka yi." Na juya tare da tattara hijab dina zan zuba gudu. Saka min kafa aka yi, ban san yaushe yazo wurin ba.
"Kin zata zaki shigo tarkona ki gudu ne? Bayan na gama tsara yadda zan kamaki, shine zaki gudu." Murmushin takaici nayi nace mishi. "Sam babu tsoron zaka min kome, domin ba zaka iya ba. Kana tsammanin kai har zaka razana ni na razana?" Mikewa nayi tare da cigaba da cewa. "Zan tafi kuma babu abinda zaka iya min, don ba xaka iya dakatar da ni ba. Abdullahi ba tsoronka yasa nake gudunka ba, ko daya ni bana gudun sharrinka. Tunda Allah ya kare ni daga ta'addancin da aka yi mana, bana jin akwai wanda ya isa ya min wani abu. Sannan izuwa yanzu na koyi tsayawa kaina." Takawa nayi gabanshi ina yar dariya na ce mishi. "Gata tayi maka yawa, jin dadi sun lullube ka. Bani amsar waɗannan tambayoyin nawa, ya zaka ji idan aka kashe mahaifinka akan idanunka? Ba ni amsar nan ya zuciyarka zata dauki ayiwa ahalinka fyade kana gani amma babu yadda ka iya?" Hawaye ne ya zubo min, na haɗiye kukana na ce mishi. "Ya zaka ji idan wad'anda ka yarda dasu, suka ci amanarka ya zaka yi? Duk wannan ciwon da aka jiwa zuciyata bai saka na juya da baya don tsoro ba, shine kai akan yar kudirin da bai wuce kayi minti ashirin kai minti biyar ma, kai ji mana gaya min a wannan lokacin da na dawo daga mutuwar ce zaka razana ni har na razana? Gaya min? ni da har mutuwa nayi na dawo don na cimma abin da nake bukata baka san yadda rayuwa take ba shi yasa idan kaci ka koshi, baka da burin da ya wuce ka wulakanta mata irina masu kima da daraja, bana faɗa kuma bana son faɗa,amma abinda kake so ka gani a idanuna har abada babu kuma ba zaka tab'a samu ba, domin gata da jin dadi sun saka kullum lissafinka na dabbobi ne, da kana lissafi irin na zakuna mace ba ta gabanka sai abin da kasa a gaba ,don haka b'ace min a gaba, duk ranar da ka samu amsar tambayoyina ka zo ni zan baka damar yin yadda kaso da ni.." daga haka na juya na barshi sake da baki, shi yasa aka ce ko wani mutum da fahimtar da yakewa kowa shi nashi fahimtar Mijinta ya watsar da ita, shi yasa zai maye gurbin shi duk yadda yaso ya b'ata mata lokaci da rayuwa, yanzu ya fahimci ashe bai san meye rayuwa karan kansa ba. Wauta da hauka yake domin da yasan darajar rayuwa ba zai tsaya bata lokaci haka ba,