Sashe 90
Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Sai da na idar sannan na dora da addu'a, kafin na mike na koma wurin Kujerar..
.... Yana zaune yana aiki da laptop ɗinshi, yaji kamar ana numfashi sama-sama, shi ya zata ma Amaan ne yasa shi leka dakin sai dai yana shiga ya ganta a kan kujera. Tana juya kanta. Fita yayi ya dauko goran ruwan da ya ajiye don aikinshi. Yana shiga ya samu ta farka. Cilla mata goran yayi ya fita. Haka kawai yake jin wani strang feel ganinta, a duk lokacin da yayi ido biyu da ita yana jin abin yana yawo a jininshi da jikinshi. Cigaba yayi da aikinshi.
Washe gari.
Da safe sai ga Amirah, rungume juna muka yi. "Mami ina kika je?" Ta tambaye ni da fulatanci. "Ba bai da lafiya ina wurin shi."
"Kina jin fulatanci dama?" Juya idanu nayi ina cewa. "Eh ni Fulanin Bauchi ce." Na tsinci kaina da fadar haka, "ikon Allah." "Ai kuwa gashi nan kin yi."
"Mami Ba bai tashi ba ne?"
"A'a Ba bai tashi ba, muje gida Uncle yana jiranki."
"Fatimah, baban Yarki ya rasu ne?" Inji Aryan, haɗiye yawu nayi zan bashi amsa Hajiya ta make kanshi tare da faɗin. "Kada ku tsannanta bincike." Ba iya ni ba, sai gashi kowa a wurin zuciyarshi tayi sanyi, gida Aryan ya ce zai kawo ni, muna fita muka hadu da Aseem, da gudu Amirah ta nufe shi ya cillata sama. "Yan matan Uncle muje a shirya ko." Ya kalle ni. " Amma kin yi kwanan zaune ne?" Murmushi nayi ina girgza kai. Tare da hamma. "Ni soyayya kike yi ne da mara lafiyar?" Yadda yayi min mganar yasa na kara kallonshi domin babu wasa a cikin maganarshi. "A'a"
"Amma ai ba danginki ba ne?" Kallon shi nayi a karo na biyu cike da mamaki. "Me ya kawo wannan tuhumar haka?"
"Saboda tsaron lafiyarki da rayuwarki na kai na ne."
"Hm!" Na faɗa, ai ba zan kuma cewa kome ba, kuma ban ga laifinshi ba. "Yazid yana raye?"
"Kice Sultan da girmamawa." Ya faɗa min had'e rai nayi ban kuma magana ba, domin nasan idan na kara magana masifa zan yi, amadadin ya kai ni gidan da na sani wata unguwa naga ya kai ni na daban, "tun jiya na tattara miki kayanki, suna nan na saka an gyara gidan ki shiga ki duba." Yar karamar unguwa ce da aka yi gidajen estate. Masu bala'in kyau da ɗaukar hankali.
A hankali na fito tare da nufar gidan, fitowa yayi ya bude min gidan, yana min bayani sam bana fahimtar shi, har sai da ya kira sunan siyamah. Na kalli kofar babbar mace ce. "Na'am." Ta amsa cikin girmamawa.
"Ga Amirah sugrah, a shirya ta na kaita makaranta. Amirah ga Nannynki." Haka ya mikawa matar, ni dai ban ce kome ba. "Idan kin shirya zan zo na kai ki kamfanin ko asibitin."
"Asibiti." Na fada ina kallonshi. "Wai don Allah duk wannan na meye ne?"
"Nima Umarni aka bani."
"Waye Yazid ko?"
"Ki ambaci sunanshi da girmamawa."
"Anki a ambata." Na fada a masifance. Daga haka na wuce dakin da ya nuna min, kayan haushi kome na dakin cream colour da coffee. Yayi kyau har wall ɗin. Wanka nayi na shimfida abin sallah, nayi sallar walaha. Ban tashi a wurin ba sai wurin karfe goma, kitchen na wuce na ga Siyamah, wake na zuba na fara aiki kamar yadda nake da can baya, na dafa wake da kifi, sai kwai da na dafa na zuba a waken. Dake ya kawo min kayan abinci na, na wancan gidan. Ina gamawa na bar Siyamah ta sauke min, ta juye min.
Wanka nayi na saka doguwar riga, na yane kaina da mayafi, mai kawai na shafa da hoda tare da kwalli. Hula na saka a cikin mayafin don gashina yaki bari mayafin ya zauna.
Ina gamawa ya kai ni har asibitin, sannan ya ce min. "Yaushe zan zo daukarki?"
"Karfe biyar tunda Siyamah tana tare da Amirah."
"Shi kenan." Ya faɗa yana me barin Asibitin. A bakin kofar asibitin muka hadu da Chairman, kai jama'a mutumin nan ya iya tsare gida, kallo daya nayi mishi yana sanye da suit black colour, ana cewa dan adam bai cika goma ba, a idanuna Chairman ya kai 💯 percent, yana tafiya bindin shi yana biye da shi, sau daya na kalle su na kauda kaina. Har bakin kofar muka isa, dake suna gabana ban san me ya gayawa security din bakin kofar ba, naga suna kallona. Ina zuwa suka amshi basket ɗin, abincin suka buɗe. "Ki ci?" Kallonsu nayi su kan har sun shiga cikin dakin. "Ban gane ba?" "Ki ci umarni ne aka bamu." Cokalin da na zo da shi a cikin basket din na dauka tare da juya abincin na diba na ci, hawaye ne ya zubo min ban san me yasa yake min haka ba, sai da naci sau uku. Sannan na ajiye ina kallonsu. "Ok ki shiga amma ba da abincin ba."
"Ban gane ba!"
"Haka akace mana, kada kishiga da Abincin."
"Tow." Na fada ina shiga dakin babu kome, bakina da sallama. Ina shiga muka had'a idanu da shi, wani irin tsanarshi nake ji yana taso min, "ina wuni Hajiya." Na durkusa har kasa na gaishe ta."lafiya lau Fatimah, ya gajiyar kwanan zaune?"
"Alhamdulillahi, ya me jikin dai?"
"Jiki da sauki, yanzu yayi barci ma."
"Allah ya bashi lafiya." Sannan na juya na gaida sauran matan dakin, wanda nake ganin kamar kannen shi ne.
A dakile suka amsa min, ban kula su ba. "Zahrah!" Ya kira sunana."Na'am!" Na amsa ina isa inda yake. "Ina ta jiran abincinki ne fa" juyawa nayi na kalli Chairman da ya hana ni shigowa da Abincin. "Zaka ci ne?" "Eh Zahrah." Juyawa nayi na fita, na samu har lokacin abincin yana wurin, dauka.nayi zan shiga suka so hanawa, Aryan da ya biyo bayana ya ce musu. "Ku kyale ta."
"Tow!" Haka na shiga dakin da abincin na ajiye. "Dama kin zo da abinci ne?" "Eh security din kofar dakin nan suke dubawa ko an saka wani abu a ciki."
"Ayya ai bani da haufi zaki saka wani abu ..."
"Hajiya mutum mugun icce " d'ago kai nayi na kalle shi ya watsa min harara. Dauke kai nayi ina jin zafin haka ba yadda na iya, ina bude abincin kamshin ya cika ko ina. "Lallai ke yar Nigeria ce."
Murmushi nayi na zuba mishi abincin, sannan Chairman ya d'aga shi zaune yana mishi magna kasa kasa. Shi kuwa dariya yake yana faɗin. "sai kayi ƙoƙari." Hajiya na mikawa flat din ta fara zata bashi. "Ki bawa Zahra ta bani dai." Tsaki daya cikin matan dakin tayi, sannan ta mike zata fita."Anisah meye haka?"
"Waye ya sani ko a harkar banzan shi da ya saba ya kwaso kara da kiya shi."
Kallonta nayi sai bance kome ba, na cigaba da bashi abincin, turo kofar dakin aka yi wata budurwa ce, me sanyin murya ta shigo, d'ago kai nayi ina kallonta. Ban da akan idanuna Munaisah ta bar camp ba, da zan iya rantsuwa Munaisah ce a gabana. Jikina kamar an jona min wuta, haka nayi ta bashi har ya koshi.
"A ina kuka samo sadaka yalla?" Inji Yarinyar. "Wani irin magana ne haka?"
"Eh tow laifi ne don naso sanin a ina aka kwaso mana iri."
"Kanwata ce!"
"Au sai yanzu na gane ma'anar sunan Uba Teresa da Hamma Abdul yake faɗa, ashe kalandangi aka samu mana. Yarinya taga dan beauty an makalewa." "Matsalata dake baki iya tauna magana ba, daga dabi'arka ake fahimtar daga inda ka fito." Inji Hajiya. "Hajiya gaskiya ta faɗa, mata dubu nawa suke."
"Amma ai naga ita me maganar bata kai, Zahrah kamun kai ba, Zahrah tazo nan ne don ni na kirata. Sannan ita ba ballagaza ba ce, irin wasu matan da suke bin namiji suna so yana musu wulakanci. Zahrah first class ce bata bukatar sai tabi namiji ya sota, ita maza suke bi don taso su. Kun fahimci karatun ko na karo muku aya?"inji Amaan din, ganin zasu samu matsala akai na, na mike tare da cewa. "Ya Amaan Allah ya baka lafiya, zan tafi daukar Amirah a makaranta. Hajiya Allah ya bashi lafiya."
"Amin Zahrah." Na saka kai zan fita. "Karuwai ai basu da maraba da macizai, Hajiya idan." Idanuna ne suka cika da kwalla na ce mata. "Ke mace ce, kuma wata rana uwa, kada ki kara jifar wata da irin wannan kalaman....
300₦
0016341139 unity bank zahra'u yahaya Ali
Katin MTN 400
#Mai_Dambu ce
[5/29, 07:47] Hlm: BHB247