Sashe 5
Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ganin na mike a hankali har na tsaya da kafaffuna, matar ta ce min. "Amma baki da hankali?" Murmushin wahala nayi domin ciwon kamar yanzu aka ji min, zafi da azaba sun ishe ni. "Eh ni mahaukaciya ce akan dangina!" Eh sune raunina, "ina zaki yanzu?" Matar ta tambaye ni, "zan tafi gida wani abu yana faruwa, idan naje in sha Allah zan dawo don Allah ki bar ni na fita."
"Zai shafi aikina ne!"ta faɗa tana kallon yadda damuwa ta bayyana ƙarara akan fuskata. Amsar wayar tayi ta koma gefe tayo kira, maganar da bai wuce second talatin ba, ta dawo ta mika min wayar tana faɗin. "Jira Doctor tazo."
"Ok" na fada ina kallon agogon ward din, wato wani ikon Allah jiran Doctor da nayi ji nake kamar rayuwata nake jiran yadda xa ayi da ita, domin ban san iya adadin bugun zuciyar da nake ji ba, can har na hakura zan mike, sai ga wata kyakkyawar matashiya ta d'andasa wanka kamar wata fure.
"Sannu yan mata ya jikin naki?" Ta tambaye ni,tana kai hannun ta saman rigata ta d'aga. "Pretty good!" Ta faɗa, "Sisi ta kira ni ta ce min,kina son zuwa gida."
"Eh!" Na faɗa ina kallon ƙasa, "ok wacce unguwa kenan?" Domin bata yi tsammanin ina jin Hausa ba, balle a kai ga wani yare. A'a tunaninta ai daga irin cotonou ko Togo, ko Mali,na fito ko irin yan ciranin Ethiopia nan, Yes haka skin dina yake kasancewar ni ba fara ba ce, amma ina da wani irin dogon fuska da siririn hanci, idanuna manya ne dara-dara.
Ni ba wata dogowa ba ce, domin yar siririya nake, sai dai fa ina da cikar halitta musamman kirji da kugu, a yanzu da nake shekaru sha shida a duniya, ina ji kamar na kama duk abinda ake bukata, sai dai halin irin na rayuwa yasa na faɗa ƙaddarar rayuwa.
"Wacce unguwa kike? Sannan me yasa zaki tafi yanzu bayan baki warke ba?" Kallonta nayi na ce mata. "Ina unguwar hausawa!" Na bata amsa cikin tararadin yadda zata dauki unguwar da na fito. "Ke Bahaushiya ce?" Hadiya yawu nayi,tare da girgixa kai. Kallona tayi kafin ta ce min. "Fulani?" Da idanu na amsa mata, ina lumshe su, gyada kai tayi tana faɗin. "Jiya an kawo ki cikin mawuyacin hali, bamu jima da miki aiki ba, kice zaki tafi?"
"Dangina suna cikin wani yanayi!" Na fada kamar zan yi kuka nace mata. "Ni dai zan dawo kuma haka na gaya mata, don Allah ku bar ni naje naga halin da suke ciki."
Kallona tayi kafin ta ce da harshen Hausa, "kina son ciwonki kada ya warke ne?" Murmushi nayi kafin na ce mata. "Babu abin da xai samu ciwo na, kawai dai ina son ki kai ni na gansu, don Allah." Na fada mata da hausa. "shi kenan muje!" Ta fita zuwa waje can sai gata da kaya, ta mika min, haka na saka kayan na shiga bin bayanta a hankali, har na isa inda motarta take, wani soja ne ya bude min kofar ita kuma ta shiga baya, suka rufe min motar muka bar asibitin. "Amma me had'aki dashi?" "Wa kenan?" Juyawa tayi tana kallona. "Wanda ya kawo ki?" Hadiye yawu nayi, kafin na ce mata "babu" domin ban san yadda zan mata bayani ta fahimta ba. Har muka fita daga barrack din, ita kanta tunani take a ranta.
Yaushe Captain ya fara bin mata? Tasan a iya rayuwarta bata tab'a kama shi da mugun abu ba, kuma har yau babu wanda zai zo ya ce maka mace tana gabanshi.
A hankali ta maida kanta nazarin yadda ya ji mata ciwo, gabakidaya kanta ya daure ciwon yana bukatar nazari. Har muka bar barrack, hankalina baya jikina sai da naga mun dauki hanyar unguwar da muke zama, na ji kamar an kuma cilla ni cikin wata sabuwar bala'i "ya zanyi da addah idan ta san na dawo babu kudi sai ciwo."
Juyawa tayi tana kallona, ni a tunani na a zuciyata nayi maganar sai na fahimci ashe ba da zuciyata nayi ba, a zahiri nayi. "Zata dake ki ne?" Idanuna ne suka cika da kwalla na ce mata. "Idan duka ne da sauki, mahaifiyata ita ce zata sha zagi." Cikin yanayin dan son ta sha cikina ta ce. "Dama ba mahaifiyarki ba ce?"
_Fatimah na hore ki, ki zama me takatsantsan ɗa abin da zai fito daga bakinki. Addah yar Uwata ce kada kuskurenta yasa ki saka duniya ta zargeta._
Hadiye maganar nayi kamar ban tab'a furta koda kalma daya ne ba, kaina a sunkuye muka isa kofar gidan da an yi bala'in cika. Kafin muyi parking motar sojoji ta bar unguwar tana kara da ihun a bata hanya, sai da suka wuce muka samu damar parking, a hankali mutanen suka ragu kowa ya kama gabanshi.
Hango Munaisah sun rufe Addah da mutane suke daukarta a waya, da sauri na fara kokarin bude motar, Doctor ta ce min. "Baki da lafiya fa, ki kula da lafiyarki mana."
Sauka nayi daga motar a hankali, bayan itama ta fito, ban tsaya jin abinda zata ce min ba, wallahi na zura da gudu."Addah" cikin wani irin yanayi me dauke da kallon kiyayya, tsana, takaici, bakinciki, Addah ke kallona."Zahra'u na gode da abinda kika saka aka min. Zahra'u saboda nace mu mori juna ki bada gishiri a baki manda shine zaki wulakanta ni? Zahra'u duk wani abinda nake bawa Ubanku da mishi kome nan nake sayarwa a bani kudi na tura mishi abinci, na bi maza a Saudiya don na ciyar da Ubanku. Duk yan uwanki suna kyautata min Zahrah kece kawai kika zaɓi kuntatta min. In sha Allah ki rubuta ki ajiye kamar yadda kika saka aka tozarta ni, wallahi sai na d'and'ana miki."
"Hajiya kafin ki fara shan alwashi yana da kyau, ki san me ya samu Zahran domin daga asibiti muke; taurin kai da tunda ta kira taji ihun ku, taki kwanciya a ka'idar aikin sai nan da gobe xata fara sauka a gado,amma ta tawo ganin halin da kuke ci!" Ta d'aga mata cikina, inda mutumin duhu ya caka min wuka. Takaici yasa Doctor ta koma motar ta ciro kudi a jakarta,ta kalle ni. "Gashi wannan kudinki ne,wannan kuma ƙatin shiga asibitin ne. Ina fatan zaki dawo a duba lafiyarki"
"Zan dawo"na fada mata, ina sunkuyar da kaina. Har ta juya zata tafi nace mata. "Baki gaya min sunanki ba" "Doctor Umaima Amin Minjibir." Daga haka ta juya zuwa motarsu, suka bar ni a tsaye. "Ke Zulaihah kamo hannunta ku shiga daga ciki, kafin matar nan ta dawo ta maida mata kudin,kin san halin zahararriyar kawarki "
Gabakidaya Addah ta manta da shegen dukar da aka mata, kun san wacece Addah? Addah ta musamman ce a duniyar kaunar kudi, Ya Allah ka mana tsari da irin soyayyar kudin Addah. A haka kuma duk duniya babu me moranta sama da Baffansu Ummi,baffan mu yana dai rike da dabbobinta ne domin babu yadda ya iya da jarabar Addah.
Idan nace zan fara baku labarin kauna da soyayyar da Allah ya daurama Addah kan kudi, sai ku ce karya nake domin haka ba zai faru ba. Addah saboda son kudi. Ta tafi har Saudiya tayi aikin tuwo tuwo.Addah ta zauna a garin lagos tayi harkar tuwo tuwo, kuma kada ku ce iya tuwo tuwon ne fa, A'a har da d'aga buje ana yi babu laifi. Jan hannuna yasa na dawo duniyar tunanin halin Addah, Matar nan kamar Ba ita aka daka ba. Haka muka shiga cikin gidan, Ummi tana gyara gidan.
"Shegiya kin zame mana bala'i da masifa, ban san wacce irin ƙaddara ce tasa adda."
"Ke kyaleta! Sannu Zahrah sannu yar nan, ke Zulaihah saka min ruwa na gasa jikina."
Ta zube kan taburma tana matsar kwalla, kafin na koma can gefe rike da bunch na yan dubu dubu har biyu. Hadiya yawu tayi ganin yadda nake rike dashi. Zulaihah har zata wuce, ta dawo ta amshi kudin ta mika mata ɗaya. "ai kowa yasan g**ndi kika sayar kika ciyar da Kawu shad'ari, duk cikin mu babu yarinyar da fita daya ta dawo miki da dubu dari biyu, sai yar baiwa me kafar sa'a don haka ga dubu dari nan ki warware gajiya, daga yau Kawu shad'ari kudin yar baiwa zai ci, muje Zahrah kici abinci mu koma asibiti. Ina rokon Allah kada yasa ki yi karkon kifi daga ruwa zuwa wuta. Duk me hankali ya ga ciwon nan yasan kin tsallake siraɗin rayuwa da mutuwa "
Da sauri Adda ta wawuri dubu darinta,tana washe baki. "Kema dai Zahra hala taurin kai kika mishi,ya burm.. ke daya waye ya turo sojoji suka min shegen duka?"
Dariya Zulaihah tayi ta ce "Ai kuwa gajarabul din da ya dauke ta mana ko Zahra?" Bakina ya mutu murus Allah ya horewa Zulaihah baiwar predict duk abinda tayi hasashenshi sai ya tabbata haka.
Tsakin Munaisah muka ji, ta juya tana me faɗin. "A gama boye-boye sabo da kaza bai hana a yankata." Ta faɗa tana nufar dakin mu, haka muka bita muka bar Ummi a wurin Addah. Lokacin da muka shiga dakin. Zulaihah ta haɗa min tea, "Zahrah kin gudu a hannun gayen nan ko?"
"Eh zuzu!" Na fadi haka, ina kiranta da Zuzu saboda jin dadin sunan, Zulaihah ta girme ni, don kusan sa'ar Munaisah ce, a ƙalla zasu kai shekaru ashirin a duniya.