Sashe 23
Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kallona yayi ya ce min."Idan muka karasa wurin zaki iya ganin maza suna wanka, zaki iya ganin su babu kaya?" Sunkuyar da kai nayi na juya bayana, ilahirin jikina rawa yake, "bana fatan kara ganin wani babu kaya" na juya kamar zan fashe da kuka. Abin da ya faru yana dawo min, a hankali naji kirjina yana min ciwo, ban san tafiyarshi ba, sai ga shi nan dauke da bokitin da jarkar ruwan, haka muka tawo, ina share hawayen da yake zuba min. "Idan zaki dauki shawarata, ki hakura da tarayya da yarinyar nan, sannan idan dare yayi ki kula da kanki da yan uwanki."
"Wani abu yana faruwa ne?" Murmushi yayi irin wanda yafi kuka ciwo, ya ce min."ki kula da kanki." Sai lokacin na hango Aina'u tana rungume da wani mutumin. Tana hango ni ta ture shi, ta iso wurina. "Balali meye haɗinka da Kawata?" Bai tanka mata ba, ya saka ni gaba muka wuce ta, shiru tayi har taga wucewar mu, sannan ta biyo mu, a bakin kofar tantin mu, muka hadu da Zuzu ta fito da wutar tana gani na, ta ce. "Zahra'u hala kin mai damu kazar turawa zaki saka mana wuta a daki?" Murmushi nayi nace mata. "matar Babban sakataren gwamnati yi hakuri bari na mai da shi waje, kada ki narke domin da kitse aka yi ki " na ajiye ruwan ina kallonshi. "Na gode Yayana " na fadi haka ina jin kwalla yana cika min idanu. "Ni ne da godiya, amma bana son yaya nan". Zuba ruwa a tunkuyar zuzu tayi, tana faɗin. "Love at first sight!" "Yes haka ne, yar uwa." Ita kan aikinta ta cigaba da yi, dakyar na sallame shi ya tafi. Yana tafiya Aina'u tana zuwa. "Zahrah kin ga mutumin nan dan iska ne, kada ki bashi fuska." Kallonta nayi na wasu dakikai, kafin na ce mata. "Na gode." Tow me zance mata? Ni dai nasan idan karuwanci bai zama abincina ba, ba zai tab'a zame min guba ba, tunda mutanen da suke zagaye da ni kusan ƙaddararsu ta haɗa da wannan sana'ar.
Ganin naki kulata, ta ja ta zauna domin na fahimci abincin take bukata, don haka Zuzu tayi uwa tayi makarbiya, ta tsaya kan abincin, ganin nima bani da katabus akan abincin ta koma tantinsu, domin yadda Zuzu ta haɗe rai ko ni a dakile take amsa min magana, don haka tana gama abincin, ta zuba kwanon asibiti sannan ta zuba mana a wani kwano, muka hadu har da Addah muka ci. Alhamdulillahi ba laifi mun tashi komad'a, sallah muka yi, sannan na shirya tare da kwanon abincin ni da Zuzu muka nufi Asibitin, ba a hana mu fita ba, amma sai da muka bi kofar uwar mugu, haka Balali ya gaya min ya ce na gaya mata zamu tafi asibiti. Lokacin da muka isa tantinta wanda yafi na kowa kyau, domin kamar gida yake, buga mata kofa muka yi, ta ce. "Waye?" "Zahra'u ce." "Shigo abinki!" Bude kofar nayi na tura kaina da sallama, dakin sai warin wiwi yake, durkusawa nayi na ce mata. "zamu tafi duba Mamana a asibiti ni sai gobe zan dawo, yayata zata dawo da yar Uwata."
"Ai naji labarin Yadikonki ce, mahaifiyarki yar kasar nan ce, baki son a nima miki ita ne?" Idanuna ne suka cika da kwalla muryata a sanyayye na ce mata. "ba a bukata, waɗanda suke wani hali nake son su samu lafiya tukun nan."
"Sai kin dawo, ga abinci ko zaki ci." Da sauri na ce mata. "A'a na gode!" Na mike na fito, Zuzu da Balali suna waje, ina fitowa ya kalle ni. " Me yasa kace mu gaya mata?" "Domin ina son ki samu kusanci da ita, yadda babu me iya tunkararki da mugun nufi, idan har kika iya kiyaye abin da bata so, cinnaka bai isa ya cijeki bata saka an ga bayanshi ba."
"Amma ya naji ɗakinta yana warin wiwi?" Murmushi yayi yana faɗin, "muje zaki fahimci wani abu nan gaba." Da muka fito mun haɗu da wasu zafafan motoci guda biyar, mutanen da suke jikin motar dauke suke da manyan bindigu. "Tambayarki ga amsarta." Shiru nayi ban san dame zan lissafa abinda nake son ganewa ba, haka muka isa bakin hanya ya saka mu a mota, ya dawo. "Zahrah bayan tafiyarki diban ruwa, matar nan dai Addah ta bata labarin mu, sannan ta amince zata shiga sana'arta."
"Yanzu don Allah ita Addah meye abin burgewa a wannan sana'ar? Gaskiya gara na mutu da nayi wannan sana'ar." Murmushin takaici tayi ta ce mata. "gara ke, kina da taurin kai, ni Addah tana cewa zata tsine min nake amincewa. Ki godewa Allah babu wani mai mugun nufi a rayuwarki." Ta fada tana kuka, rike hannunta nayi ina faɗin. "Ya isa haka!" Itama rike hannuna tayi tana wani irin kuka, wanda na fahimci ba kukan abin da yake faruwa damu ba ne, akwai wani abu a ranta. "Zahra'u Alfarma nake nima daya tal?" Rike hannunta nayi, hannuna ta ja cikin rigarta, ta daura a saman cikinta. A razane na cire hannun ina toshe baki. "Idan ya rayu, zan so ki rike a matsayin naki don Allah bana son ya bata min gobe na. Idan na mutu ki rike shi har abada." Wani irin rawa jikina ya dauka, ban taɓa kawowa a raina haka zai faru da Zuzu ba, "Me yasa kika bukaci haka?" "Babu wanda ya sani sai ke, don Allah." A daidai isar mu asibitin, sauka nayi na bashi canjin da Balali ya bamu. Koda muka isa asibitin Munaisah tayi kuka har ta godewa Allah. Tana ganinmu ta faɗa jikina, tana kuka tana faɗin. "tun tafiyarku sai tashi abin yake ana ta niman wanda zai nimo ki, tana son ganinki." Bubbuga bayanta nayi, na ce mata. "Ya isa!" Dakyar ta daina kuka na ajiye mata abinci, ta fara ci zata cire hannu na cigaba da bata, tana ci tana kallona. "Kiyi hakuri.!" Ta ce min, ni na saba da wannan kalmar bata wani hana ni sakat, haka ta ci abincin sosai, sannan na tafi inda zan sauya kayana, na nufi dakin da Yadikko take, an zuba mata na'ura kanta da kirjinta. Ina zuwa na rike hannunta. Kafin na shafa kanta bude idanu tayi tana kallona. Hawaye ne yake zuba mata, ta rike hannuna da babu kome. Ina murmushin karfin hali nace mata. "In sha Allah zaki tashi kin ji Nenne na, zaki tashi da kafarki da karfinki."
Kallona kawai take har na wani lokaci, kafin Munaisah da Zuzu suka shigo. Kallonmu tayi tana kallonmu bakidaya, "bari na rakasu," na janye rikon da tayi min, na tafi na rakasu. "Balali yana jiranku zai kai ku har har tantin in sha Allah."
"Tow shi kenan!" Haka suka hau mota na dawo dakin Nenne, ina rike da hannunta, tunda ta bude idanu ta ganni, ta lumshe idanunta, wato ko? Wannan yanayin Allah kadai yake da ikon jarabtarka a zauna lafiya. Nenne tana cikin wani irin yanayi, domin kuwa tasan kai ne akanta amma babu bakin magana. Can kuma zuzu ta fado min a rai. *Yaushe tayi cikin?* Wannan shi ne tambayar da nayiwa kaina, kuma nasan bani da me bani amsar sai ita, haka yasa nayi shiru, ina nazarin wannan al'amarin da tashin hankali yaƙe. Kwana nayi a zaune ban rintsa ba, ina sakawa da kwancewa, sannan Zuzu ta bani abin cikinta. Ashe Uwa tana kyauta da d'anta tun kafin ya shaki iskar Yanci? Amma me yasa Zuzu tayi haka? Me yasa tayi shiru bata fada ba? Ko tana tsoron kada Addah ta ce ta zubar ne?¹ tunda haka ya tab'a faruwa da Shamsiyah tasa dole sai da ta zubar da cikin hankalinta ya kwanta. Ajiyar zuciya na sauke idan har Addah zata iya sakawa a zubda na bare tabbas zama bai kama ni ba, dole mu bawa cikin kariya. Ajiyar zuciya na sauke ina jin kamar na sauke rabin damuwar da yake damuna. Kiran sallah ya fahimtar dani ashe kwana zaune nayi.
Haka na fito zuwa Masallaci, acan nayi sallar asuba, sannan na koma ciki.
Karfe tara da rabi, sai ga likitocin da suke dubata. Suka gama dubata sannan suka fito babu wanda ya ce min kome, bayan tafiyarsu ne Zuzu ta kawo mana abincin,"Ina Munaisah? Kina fama da kanki zaki zo nan?" Murmushi tayi tace min. "Kuma sai na zauna kowa yasan ina da Yaron ciki?" Gyara zama nayi na fara cin abincin da kunun da ta kawo min. Ina sha ina kallonta, "Zahrah don Allah bar kallona haka." Sai na dauke kai kamar ban ji me ta ce ba, na cigaba da cin abincin na. "me yasa baki gaya min kina da ciki ba?" "Saboda kin koya min kome ya same ni, na adana shi sirrina ne ba na kowa da kowa ba, har kwanan gobe baki gaya min yadda aka yi kika samu yankar cikin ba, amma na tayaki boye mutumin da kuka kwanta gado daya a asibiti. Addah tasan da wannan zancen ai sunanki." Murmushi nayi ina kallonta. "Zuzu kenan, kina tsammanin wani hujja ce don na ki gaya miki yadda aka yi na yanke a cikina? Ban sanshi ba, ban san yadda aka yi ya taimaka min ba, ban kuma San me yasa ya yanke ni ba, abu daya na sani Allah ya kubutar da ni daga hannun Azzalumi ne ya wurga ni rayuwarshi. Haka ya ishe ki ko kina buƙatar wani karin bayanin?"