Sashe 68
Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Tsayawa tayi ta kalle ta kirashi da yatsu biyu, yana matsowa ta rike kunnenshi ta gaya mishi wata magana, murmushi ya sake. "Hajiya wacce irin Shaidaniyar tunani ne haka?" jan kunnen shi tayi tana faɗin. "Ba zan tab'a yarda wani ya san wacece ni sannan, ya dawo ya soke ni a baya ba, sun wanda ya sake ya ci amanata sai na mai da rayuwarshi abin kwatance yadda kowa sai yaso yaji me mutum yayi min haka."
"A'a sam haka ba zai taba faruwa ba, ai kowa ya kwana lafiya shi yaso."
Hajiya kam hankalinta yana kan Amaan, bakiɗayansu babu wanda yake zaune, azumin ma suna yi ne amma bakiɗaya hankalinsu yana can. A ranar da ya cika sati daya a asibitin aka sallame shi, domin ya d'aga musu hankali lallai a sallame shi. Hakan ya faru ne wani zuwan da Sajjid yayi mishi cikin daren rana na biyar ya, yana kwance ya shigo mishi don a sanin Amaan dai Majid yake zaune da shi amma bai san ya aka yi Sajjd ya shigo dakin ba. "Kana ta barci, ina can ina kewarka." Cikin tsananin tsoro Amaan ya ce mishi. "Sajjid wai ni daya ne kawai da ba zaka kyale ni ba? Ka kyale rayuwata kayi naka rayuwar."
Dariya ya saka mishi yana faɗin. "Amaan ba zan kyale ba, idan ka kuskura ka haura kwana goma a cikin asibitin nan, tabbas ward din mata nan zai zama wurin kwanciyar tsohuwarka. Domin ina ƙishirwanka, sannan ka duba wayarka zaka ga kayatattun hotunan da videon debe kewa"
Haka Sajjid ya saka kai ya bar dakin, sanadin haka yasa Amaan d'aga musu hankali sai an sallame shi. Sannan wani abin da ya kara tashin hankalinshi, yadda Sajjid ya tabbatar mishi matukar bai koma ruwa ba, sai kowa yasan abinda yake faruwa a tsakaninsu.
Asalin rashin lafiyan Amaan yana da nasaba da Sajjid, domin kuwa lokacin da aka mishi aiki tsakani da Allah ya daina wanna shashancin, ya mugun kame kanshi. Sai dai kuma gefe guda Sajjid ya haɗe kai da matar Amaan, inda suke sharholiyansu. Ranar da aka kai na farko ya dawo gida, ya ga motar Sajjid cikin azama ya shiga cikin gidan. Koda ya shiga bai same kowa a falo ba, haka.yasa ya wuce dakin shi, abin takaici da bakinciki. Zuwa yayi ya samu Matarshi da Sajjid suna tsulla tsiyarsu. Kuma abin bakinciki babu tsoro ko dar a tare da ita. Shi idan yana son hakkinshi sai ya biya asalima sai tayi ta jan shi a kasa, ya zuba mata kudi .
Gashi a karon iska akan Idanunshi, Sajjid yana more ta. "Na zata duk abin da kace nayi zan yi ba zaka wuce gona da iri ba, ashe har matar aurena kake hakewa." Basu fasa ba, karshe da bakinciki ya fita a dakin yana tari, tare da ciwon ciki tunda ya koma ruwa baya ganewa kanshi, gashi kullum idan suka yi akwai wani ruwa da Sajjid yake bashi ko yana so baya so sai ya sha ruwan tun daga wannan lokacin fatarshi ta fara duhu. Dalilin da yasa ya bar mata gidan kenan ya koma gidan Hajiya har ya fara rashin lafiya, tayi tayi ta same shi ya koma gida amma fir yaki da zata dame shi ya tura mata sakinta, haka yasa bakiɗaya Sajjid ta shiga takaici, na farko yana amfani da Amaan yasan motsi Aryan. Na biyu yana da abin da yake son sani daga bakin Amaan.
Sai akayi dace ranar da ya nemi ya ji dalilin sake, Matarshi. Suna haduwa ya saka mishi kwaya a ruwa ya bugar da shi, anan ya ji labarin abinda ya faru a lokacin suna Kano, kofa ya farka abin da ya faru akan shi ya dawo mishi kai, rokon Sajjid yake amma ina Sajjd tsalleke shi yayi yana faɗin. "Kada na kuma ganinka, idan na ganka sai na gayawa duniya wacece Uwarka, anya kuwa kai dan halak? Idan har kai dan halak ne ba zan kuma ganin kazamar fuskarka ba."
Daga haka suka rabu wannan abin ya saka Amaan tsoro da faduwar gaba, sannan wani abin tashin hankali yadda Hajiya zata ji yana luwadi, yayi kuka yayi kuka amma babu abinda ya sauya domin dai bayan kwana biyu Sajjid bai kyale shi ba, cigaba yayi da matsa masa lamba, tare da amsar kudin shi har a gadon asibitin da yazo, lallai Amaan ya kwaso takardun dukiyar Majid ne. Shi yasa ya zo mishi tare da bashi wasu zabin abubuwa uku.
Na farko ko ya kawo mishi takardun Abdul Majid Mamman Ba'are. Na biyu ko ya turawa Hajiya videon nan, na uku ko ya gayawa Duniya Tsohuwar Chairwoman na BA'ARE GOLDEN EMPIRES, karuwa ce da aka kamata har aka rufeta yana da shaidun da abin ya faru da su, kuma zai gayawa duniya cewa bakincikin haka yasa Mamman Ba'are mutuwa, karin tashin hankali shi ne yana kalubalantar Aryan da Jamilah da Aneesah ba jinin Mamman Ba'are. Sai ya zab'a a cikin wannan yanayin.
Amaan sai a yayi fatar da mutuwa yayi da Rayuwar da ya jefa kanshi, yayi kuka yayi bakinciki a duniyar nan yaji kamar ya mutu ma, amma yasan darajar rayuwa, yasan matuƙar Hajiya taji abin da yasa shi zama haka zata tsane shi, zata cire shi cikin Yaranta,. Hajiya zata yi alawadai da shi. Haka yasa bakiɗaya yaki zama gidan Hajiya. Haka ya dawo gidanshi,
Ana gobe sallah Majid suka je gidan suka same shi, a daki kamar mayye. "Wai lafiyarka zaka bar inda kake samun kulawa ka dawo nan da zama?" Kallo daya Majid yayi mishi ya fahimci yana cikin tashin hankali, daurewa kawai.
"Amaan Mamman Ba'are!" Yaji muryan Majid ya ratsa kunnen shi.
"Meke damunka? Kasan dai nasan abin da kake boyewa."
Kuka ya fashe da shi, har jikinshi yana rawa, a hankali wayarshi tayi kara. Yana dubawa ya dauka har jikin shi yana rawa ya ce mishi. "Meye?" "Ina gargadinka da ka iya bakinka."
"Tow naji."
Kashe wayar yayi yana mikewa yana faɗin. "Muje babu abinda yake damuna."
"Shi yasa daga waya zaka ware kamar babu wani abu?" Inji Aryan.
"Kyale shi, yana kara cilla kansa cikin tashin hankali." Daga haka suka fita, sai mita Aryan yaƙe, haka suka nufi gidan Hajiya. Anan suka yi shirin sallah.
***
Tun ana jibi sallah, na dauki su Barakatu muka je saloon. Aka mana lalle da wanke kai. Sannan muka dawo, ana gobe sallah, kuwa munyi cin-cin da cake, donuts. Saboda gas ɗina Babba ne.
Ranar sallah muka shirya aka zo aka dauke mu zuwa masallacin idi. Bayan an sauko idi, muka dawo gida muka cigaba da bikin sallah. Ni kan ina gida su Baraka da Amirah sun tafi, yawon sallah.
***
Za a iya kiran yau da ranar sallah, amma a zahirin gaskiya ranar yau tana cikin wasu irin ranakun da Majid Mamman Ba'are ba zai manta ba, domin ana sauko sallah idi. Labarin rasuwar Maisarah ya karad'e cikin gidan bakiɗaya, kafin a ce wani abu.
Ana cikin wannan jimamin, aka sake videon Amaan Mamman Ba'are, a internet bakiɗaya, Hajiya bata sani ba sai da ta shiga gidan rasuwa taga yadda ake kallonta ana cewa. "Eh danta ne na biyu."bata ce kome ba, sai da ta isa dakin Maman Maisarah zata isa wurin gawarta, Hajiya Turai ta ce mata. "Sa'a da alamu tarbiyyar Amaan ya sha bambam da na su Majid waye ya sani ko dukkansu daya ne."
"Ban gane ba? Wacce irin magana ne haka "
"Sa'a ai kina da waya ki duba mana, waye ya sani, Yayanki dai bamu yarda Yayan Mamman Ba'are ba ne."
Zata yi magana Hajiya Tani ya ce mata. "Duba wayarki da bada amsa karamar mara kunya."
A hankali ta duba wayarta dake datar a rufe take bata ga kome ba. "Sa'adatun me make ji? Dama Mamman yasan kina bin maza a can Kanon ya dawo dake nan innalillahi'wa'inna'ilaihi'raji'un, Wayyo Allah na."
Bakiɗaya maganganunsu ya kara gigita Hajiya, bata san me suke nufi ba. Sai da Anisah ta kirata tana faɗin . "Wayyo Allah na, Hajiya su Hammayo sun mutu.....
********Barkan yan uwa masu kamshin furanya, ni dai anan xan tsaya sai Allah ya kai mu bayan sallah. Sannan ku saka ni cikin addu'arku Hajji nan ko Umara Ya hayyun Ya Kayyum ya kiramu duk me niyyar Alkhairi Assalamu alaikum da sauran free page's In sha Allah.... Kada ku manta 300N ne babu yawa 🥰😍🌹 Allah ya amshi ibadarmu Ramadan Kareem 🫀🥰😍🌹
#Mai_Dambujebuje🥰❤️🥳🫀
[4/13, 4:03 PM] Cutie cutie pie: *BAƘIN HAURE....🐾🐾*
{Greed for Money is the roots of all evils🫀}
Arewabooks:maidambu41
Wattpad:Mai_Dambu
Mallakar:Mai_Dambu
😹 Appy sallah ina jiran goran sallah na🙄
034