← Book details Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 138

Sashe 21

Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

mishi ya rufa min asiri, ba ya tona min ba. Yakumbo abar maganar Allah ya baku lafiya." Rike hannuna tayi tana faɗin. "Lallai Allah ya albarkaci rayuwar Aminatu a duk inda take, ta haifi daya tamkar da dubu. Zahra'u Alfarma daya zaki min, ina son na mutu a wurin dan Malam." Kallonsu nayi kafin nace mata. "Yakumbo in sha Allah za a maidake wurinshi." Daga haka na fita, ICU na nufa, a hanya na tsaya tare da jingina da bango,na rasa me ke min dadi, sai da nayi nazari kafin na wuce wurin su Zuzu. "Sai yanzu?" "Eh!" Na fada ina me zama a gefen Munaisah. "Zuzu Yakumbo tana son komawa gida, ko muma mu koma ne?" Gyada kai tayi kafin ta ce min. "idan mun koma wurin waye zamu zauna?" "Wurin Ya Dan Malam mana!" Na fada mata, ina kallon reaction ɗinta. "Hmm! Shima nima yake, ba laifi idan kin saka su Yakumbo a motar, amma har ga Allah na yafe Nigeria, domin nasan sun kashe min har mahaifina." Ta fada tana kallon kofar icu ɗin. Kaina a kasa ban kuma magana ba, har dare ya fara yi na riko hannun Munaisah. "Sister taso muje." "A haka xan bar Nenne a nan? Idan wani abu ya same ta fa." Girgiza kai nayi sannan na riko hannunta, "Muje babu abinda zai faru, in sha Allah." Daga haka muka juya zuwa dakin mu, dukkansu sun kwanta nice kawai nake zaune, ga Addah da bata zama haka kawai ta tsiro da yawo, ina zaune a wurin har wani lokaci na tashi na shiga ban daki nayi alola na fito na shimfida dan kwallin kaina na fara sallah. Sallar nafilla nayi ta jerawa, ina rokon Allah ya yafewa iyayenmu da suka rigamu zuwa gareshi, ya musu rahama. Ni kuma Allah ya bayyana min mahaifiyata. Su Nenne kuma Allah ya basu lafiya. Haka na cigaba da sallah har wurin karfe biyu, a lokacin Addah ta shigo. Gadonta ta nufa ta kwanta. "Addah ke daya ce me lafiya a tsakaninsu Yakumbo, amma Addah kin ki bamu lokacinki sai ki tafi yawo ba zaki dawo ba, sai dare ya raba." "Tow Zahrah sai ki rufe ni da duka, dake an ce miki yawon banza nake tafiya ba." Ban kara ce mata uffan ba, ina jin Zuzu tana kwafa, idan na fahimta idanunta biyu. Kawai ba zata yi magana ba ne, haka na kwana, kusan kamar nurse domin ina jikin Munaisah ina kula da Yakumbo. Wannan al'amarin ba karamin tab'a rayuwata da lafiyata yake ba, da gari ya waye bayan mun yi sallar asuba, sai ga wasu mutane uku, biyu maza daya mace. "Zamu mai daku sansanin gudun hijira ne, domin mun samu labarin yadda wasunku suke fita yawon dare." Dukkanmu Addah muka zubawa idanu. Matar nan tayi mirsisi da idanunta, ta nuna ni. "Ga yar iskar da take bin maza, nayi fadar nayi maganar na gaji." Wato wani irin razana muka shiga, domin babu wanda ya kawo Addah zata iya min sharri, ni kuwa banyi mamaki ba, domin fiye da haka idan akace zata min wallahi zan yarda, matukar Hajiya Addah ce kaɗan da aikinta, amma kuma abin da tab'a rai. "Tow koma waye, zamu tafi da ku." "Addah ki fara gina wutarki kafin ki tafi lahira." Inji Zuzu, sake bude baki tayi zata kara magana. Na rufe mata baki saboda ko Munaisah da muke tare itama bata ce kome ba, hakan yasa na gane ni ce bare a cikinsu, dukkansu abu daya ne. Haka na shiga haɗa kayanmu. "Muna jiranku." "Ranki shi dade, akwai yar Uwata da bata da lafiya an kaita ICU ko zan zauna a jikinta?" "Ba zaki zauna a jikin kowa ba, domin kuwa kika zauna a nan ba jinyar zaki yi ba, yawonki zaki shiga yi." Inji Zuzu. Haka suka fita, ko ya aka yi sai ga Nurse Ali da Rabeka. "Yar fillo, ga wannan katin yanzu na amsa miki keda yar Uwarki. Koda zaku fito daga camp zuwa nan tow ku tabbatar kun rike wannan katin, sannan Fulani zata tsaya tunda Mamarta ce, ke idan an jima yayi sai kizo ki canjeta. inji Doctor Moses."
Chapter 21 · 0% Book details