← Book details Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 127 OF 138

Sashe 127

Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

***
Tun da ya isa south Africa, suka dunguma, zuwa Nigeria, a can aka shiga tattaunawa tare da saka, bayan ya saka uniform din shi. "Ba'are me ka sani akan yan fashin tekun nan?" Shiru yayi kafin ya sauke ajiyar zuciya. "Idan har wadanda muka kama shekarun baya ne, tow nasan suna gidan yari. Idan kuma wasu ne tow ba makawa masu nima na sun sanni kuma ni din suke nima, domin idan ba ni ba ne da tuni sun kashe mutanen."
Ya faɗa yana kallon board sannan ya cigaba da cewa. "Idan har yadda nake hasashe ne, tow dole a bani team dina da muka yi aiki da su shekaru shida da suka wuce, ina son a tara min su yadda zasu taimaka min yadda zamu yi aikin."
"A kira su duk inda suke nan da kwana uku."
Tunda daga wannan meeting, da farko yana kiran gida amma tunda team din shi suka haɗu kawai ya datse kiran gida suka shiga aiki, a haka suka tafi har maboyan yan fashin tekun, ba karamin aiki suka yi ba, shi yasa ba a jin labarin shi sai da ya kwashe wata biyu, a na uku ne yayi kokarin kiran gida a san ko lafiya tunda ya bar mace da tsohon ciki. Ranar da ya kira ta ɗauka kukan da take yi ne ya kashe mishi jiki. "Fatuna, kiyi hakuri in sha Allah ina kammalawa zan dawo kin ji, ki shafa min kan babbar mace."
"Amma me yasa baka kira ni ba?" D'aga kai sama yayi yana murmushi ya ce mata. "Saboda bana son na kasa aikina."
"Don Allah ka dawo tsoro nake ji, kada su cutar min da kai, don Allah ka dawo ka ji."
"Zan dawo in sha Allah."
"Amma kayi min alƙawarin tare zamu shiga dakin haihuwa don Allah ka cika min." Murmushi yayi yana faɗin. "Nayi alƙawarin haka, idan Allah ya nufa xan dawo, idan kuma ta Allah ta kasance kada ki yi kuka.". Fashewa da kuka tayi tana faɗin. "Allah ya tsinewa wanda ya kirkiro zuwan ka Nigeria, haka kawai basu nime ka ba sai da nake cikin tsannanin buƙatar ka, kasan yadda nake son kasancewa da kai kuwa. Wallahi Allah ya isa min." Dama da yar guntun tsiwa ya hadu da rikicin ciki ai kuwa tayi ta kuka da Allah ya isa bata yafe ba. Dakyar ya shawo kanta sannan ya roketa da kada ta manta ta saka shi cikin addu'arta, domin gagarumin aiki ne a gabanshi. Kuma yau zasu fita aikin don haka su tabbatar sun mishi addu'a. Yadda take wani irin kuka ya sa shi kashe wayar domin yasan ba zai iya jure kukanta ba, Zahra wata irin jigo ce a rayuwarshi ba iya ita ba, duk wanda yake tare da shi yana amfana da kasancewar Zahra a tare da shi don haka yasa shi kashe kiran, a daren ranar suka hau jirgin ruwa zuwa inda barayin suke.

Wani abun da Majid ya kasa ganewa, yadda ga zaratan sojoji amma ba a nime su ba sai shi, kuma abin da Zahra ta koka mishi kenan, amma bai ce kome ba, babu wani abin da yake iya juyawa ko ya sauya ƙaddara. Wacce addu'a take iya sauya akalarta, musamman wanda ya yarda da Allah ya kuma miƙa lamarinshi ga Allah sai kome yazo da sauki. Haka abin yake domin jikinshi a mace zasu tafi yake jin wani iri don haka ya ce a tsaya. Tsayawa suka yi ya kalli Yaranshi mafi kusanci da shi sannan ya ce musu.
"Ni zan tafi sannan ku bi diddigina ta nan, ban san yawan su ba, amma idan naje zan tabbatar da yawansu shi yasa xan tafi, kuyi kokarin ganin motsina ta nan!" Hikimar shi koda yaje wani abu ya faru tow ba zai kasadar janyo su a cutar da su ba, shi kuma yasan idan baya raye Zahra da Yarshi zasu samu kulawar dangi da na abokan arziki, kuma ya bar dukiya me yawan gaske da zasu kula da kansu.
Shi yasa da abokan aikin suka fita ya ce musu. Suyi kokarin ganin sun san inda yake ya bazama bin location din da barayin suke.

Wannan ita ake kira tafiyar ƙaddara, wanda cikin shi babu guziri babu kome sai wani ikon Allah da sa rai. Haka ya damki hanyar tare da matukin jirgin. Kuma yana da yakinin tunda suka ce shi suke nima tabbas shi din ne babu makawa, gara yaje can ya ga me yasa idan ma ya mutu ya mutu ne a matsayin jarumi ba rago ba. Kuma abin alfahari ga ƙasarshi da kasar Nijeriya.
***
Zuwa yanzu cikina ya shiga wata tara, rabona da shi wata uku cif da kwanaki haka yasa hankalina ya kara tashi, ga tsananin kewar shi da begen shi,. Abin ka da sabon shiga kullum sai nayi mita nayi kuma Allah ya isa ban yafe ba. Dake yau Laraba ne ina zaune a tsakar gida, an shimfida min tabarma, sai mita nake yi ina cin.taliya da mai da yaji wanda aka min miyar jajjagen tattasai sai yajin da yake gefena.
Ga ruwan zafin tea da na'ana da nake kurba, "Ni kan tun daga ranar da kuka yi waya da Abdul ya kuma kira kuwa?" Kamar zan yi kuka nace mata. "Bai kira ba, na gwada layin baya shiga."
Na d'aga kofin zan kai bakina, naji wani wata faduwar gaba, sai da na sake kofin ina faɗin. "Innalillahi'wa'inna'ilaihi'raji'un! Allah na tuba ka yafe min,Allah na tuba, Allah na tuba. Subhanalillahi walhamdulillahi Allahu Akbar!" Na fashe da wani irin kuka, wanda tunda nake ban tab'a jin nayi irin shi ba, kuka nake ga duk me saurarona yaji kukan.yasan na gigita ne bana lafiya ba.

Kafin kace me Mama da take shanya kayana a igiya ta zuba min ido , Goggo Sume da Yafendo suka yi min cirko-cirko. Malamijo suka kira ya tsaya a kaina ya shiga min addu'a, yasa aka bashi ruwa yana tofa min, Goggo Sume tana shafa min. Kafin wani lokaci na fara ajiyar zuciya. Can barci yayi gaba da ni, ina ajiyar zuciya.

Tunda na kwanta nake mafarkin shi yna murmushi, yana faɗin. "Ki tashi ki min addu'a, ina bukatar addu'a. Kinji tashi ki min addu'a ina bukatar addu'a." Ko minti ashirin ban yi ba na farka a razane, ina faɗin. "Don Allah kuyi mishi addu'a ya ce yana bukatar addu'a." Ganin yadda na birkice yasa Malamijo saka Yayansu Mama Alhaji Ahmed da yazo gidan ya kira Hajiya, kafin wani lokaci labarin halin da ake ciki ya iso mana, wayyo Allah raxanar da na shiga ya haifar min da sarkewar hakori domin har na fara tattauna harshe na, "Ku bani cokali innalillahi'wa'inna'ilaihi'raji'un!" Haka aka saka tsumma aka naɗe a jikin cokalin aka tusa min a bakina, sannan aka dauke ni don har na fara zubar da ruwan haihuwa. Aka nufi asibiti da ni.

"Innalillahi'wa'inna'ilaihi'raji'un! Tashin hankalin da ba saka mishi rana, yarinyar nan taji halin da mijinta yake ciki a jikinta ne Ya Allah na tuba, Ya Allah nayi kuskuren inazan ga Isma'il da Yar Uwarshi!" Haka Malamijo yake fada yana nanatawa, kuka yake sosai, duk abinda ya faru ga zuri'arsa gani yake kamar har da abin da yayi na kuruciya ya zalunci yaran dan uwanshi ya barsu. Haka aka kai ni asibiti ana shiga da ni. Aka ce aiki Kawu Ahmed ya saka hannu aka debi jininshi aka saka min, zuwan wani babban likita yasa kowa ya shiga gaishe shi yana ganin Zahra ya ce musu. "Yarka ce Amadu?"
"A'a Madobi yar Aminatu ne da dan Sa'a yake aure, tow yau aka samu labarin mijin an kashe shi shine ta shiga tashin hankali."
"Maza a wuce da ita ayi mata aikin!" Kafin kace kwabo an wuce da Zahrah aka shiga da ita aikin kafin awa biyu har an fito da ita, da katuwar Yarsu gwanin ban sha'awa, a cikin wannan yanayin aka.fito da ita aka wuce da ita dakin hutu.....
300₦
0016341139 unity bank zahra'u yahaya Ali
Katin MTN 400
#Mai_Dambu ce
[5/29, 07:48] Hlm: BHB272

Duk yadda al'amarin yake ya wuce tunanin mutane, domin kuwa an nemi Majid sama da kasa an rasa, gashi nan sun ga location din da ya nufa amma daga baya babu shi babu labarin shi. Wurin sati daya da faruwar al'amarin, haka gamayyar sojojin ƙasa da ƙasa suka tafi har inda aka ga al'amarin yana nan, babu shi babu labarinsa, sai dai sun samu turawan lafiyarsu lau. Sannan suka dawo da su. A bakin su suka ji labarin abin da ya faru.

A lokacin da aka kama su, burin shugaban barayin a kawo mishi Abdul Majid, ko a mace ko a raye. Sannan suka ce idan aka kawo zasu sake su. Duk da cewa basa tunanin Majid din zai zo amma kuma wani ikon Allah, sai ga shi nan ya taso ya zo, tunda ya fara tunkararsu sai abin ya zama kamar an san da zuwan shi. Tuni suka zagaye shi tare da cewa. "Ka ajiye kayan aikinka, kai kawai muke so." Lumshe idanunshi yayi ya ajiye kome ban da abin dauka, sannan aka wuce da shi can wurin da aka daure turawan, kafin su karasa zuwa aka fitar da su aka saka ya cire kayanshi, suka bashi wani sannan suka dauke shi a jirgin ruwa bayan sun rufe mishi fuska baturen yake cewa duk abin da yake faruwa idanunsu a rufe, haka suka tafi suka bar su a wurin, duk da sun cire rai za a kawo musu ɗauki sai gashi nan anzo.
Chapter 127 · 0% Book details