← Book details Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 138

Sashe 28

Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Na yarda!" Inji Nasiru Wodabbe, shima kuma Mamman Ba'are ya ce mishi."na amince."
Aka shiga buga cacca kamar da wasa, Nasiru Wodabbe ya shiga nasara akan Mamman Ba'are, har dai da ya cinye shi kome hatta wandon jikinshi sai da ya saka a cacca. "Mamman Ba'are kwashe kayanka, idan ka haifu namiji ka saka kamfaninka " kurawa Alhaji Nasiru Wodabbe idanu yayi, kamar ya zagi Uwarshi. "Zan saka amma ka sani idan nayi nasara ba zan maka da wasa ba."

"Na amince," saka kamfanin yayi cikin murna da kwarewa Nasiru Wodabbe ya fara buga wasa, tun a zagaye na farko ya fahimci kamfanin Ba'are GOLDEN EMPIRES ba sa'ar sa bane, domin a wasan farko Ba'are ya dawo da kayanshi wasa na biyu ya dawo da kome hatta zobensa na azurfa sai da ya dawo da ita. Murmushin yaƙe yayi suka cigaba da wasa, aka cinye kome cikin takaici ya ce mishi. "Na saka yar Yayana Sa'adatu."
Shiru Mamman Ba'are yayi yana kallon Nasiru Wodabbe,"Me yasa baka saka yarka ba sai yar dan uwanka." "Da ina da Y'ar
ba zan saka Sa'adatu ba, domin darajarta tafi karfin dan cacca irinka,na gaya maka."
Tab'e baki Mamman Ba'are yayi yana dariya,"bari na gaya maka ko gwal ce da kanta, bata fi karfin dan cacca irina ba sai ma tausayinta da naji da ta samu Baffa irinka."
Cikin fushi Nasiru Wodabbe ya kara buga wasan hannunshi, cikin rashin sa'a ya fadi Mamman Ba'are yana bugawa sai gashi yayi Nasara, "Na sameta kana da wani abu da zaka fanshe ta?" Idanunshi ne ya kad'a jajjur. "Kai tsinanne yarinyar da babu ruwanta, yarinyar da gwamnati dauki nauyinta saboda kasancewarta hazika, me ilimin addini da na boko, shine zaka samu a banza ba zan baka ita ba, ni na sakata a cacca amma ka fara ketare ni kafin ka isa gare ta."
"Ba zan ketare ka ba, yadda ka saka ta a cacca haka zaka bani ita har da kome nata." Shi kanshi Alhaji Mamman Ba'are, bai tab'a zatan Allah zai bashi irin macen da yake so ba, sai da ya buga kamfanin shi na gwal a cacan sai gashi Allah ya bashi ita a lokacin da bai zata ba.

Kafin wani lokaci rikici ya barke a tsakaninsu, sai ga manyan maza da bawa hammata iska, dakyar aka raba su domin har jami'an tsaro sun shiga lamarin, Alhaji Mamman Ba'are da yaga samu zai ga rashi ya daka tsalle ya ce ai ta zama tashi tunda wasa aka buga, wasa gaske dai yaki karbar kome ita Sa'a kawai yake so. Ganin haka yasa Alhaji Nasiru Wodabbe ya amince da shawarar da aka bashi a office din yan sanda aka daura auren Sa'adatu Aliyu Wodabbe da Alhaji Mamman Ba'are, a Office din yan sanda, da sadakinta aka bashi yana ji yana gani Alhaji Mamman Ba'are ya wuce tare da ɗaukar yan rakiya har gidan Nasiru Wodabbe, ganin kamar Mamman Ba'are bai da hankali yasa shi isa gidan kafin su isa, yana shiga kamar wanda aka wurgo shi, dama a Libya yake da zama da Matarshi da yar rokonshi. Sakamakon wani karamin abin da bai kai ya kawo ba, ya baro kasarshi.

"Sa'ade ki yafe min, na miki rashin adalci. Kiyi hakuri in sha Allah gobe zaki yi dariya." Ya fada yana dauke kanshi ya kalli Matarshi, Raliyah. "shiryata za a zo ɗaukarta na aurar da ita " "ka me?" Ta tambaye shi jikinta yana rawa. "Eh na gaya miki na aurar da ita, ina ga ai da Hausa na fada ba larabci ko fillanci ba."
"Amma me yasa? Kasan Lamido yana can yana jiranta."
"Haka Allah ya nufa ita ba matar shi ba ce." Ya dawo kan Sa'aden ya riko hannunta. "Kinsan ba zan tab'a cutar dake ba ko?" Gyada kai tayi kanta a sunkuye. "Tow kiyi hakuri kin ji." Ya fada yana Hadiye kukan da ya zo mishi, haka ya hada har da kome nata, ya tsaya Raliya ta shiryata.........
(Hmmmmmmmm ku bi alkalamin ƙaddara)
#Mai_Dambu
[2/16, 9:24 PM] Cutie cutie pie: *BAƘIN HAURE....🐾🐾*

{Greed for Money is the roots of all evils🫀}
Arewabooks:maidambu41
Wattpad:Mai_Dambu
Mallakar:Mai_Dambu

Assalamu alaikum barkanmu da warhaka da fatan kuna cikin koshin lafiya, karku manta da wannan Kamfani mai albarka mai kawo muku kayan bukata cikin sauki da Aminci da Inganci.
Wato TA RASULU MULTIPURPOSE. YA SAKE DAWO MUKU DA KAYAN NAN MASU ARMASHI DA DANDANON KOWACCE MACE TAURARUWA CE.
_______________________
MARKADADDIYAR GYAD'A
HADADDEN KAYAN SHAYI
GARIN KOSAI NA TAFI DA GIDANKA.
GARIN TUWO
GARIN KUNU YAR ASALI
CURRY ME DADI
SPICES
TYME
YAJIN DADDAWA ME KYAU
GARIN DAN WAKE
JAN YAJI MAI DAD'I...
_____________________
BUGU DA KARI MUN TANADAR MUKU DA KAYAN FITAR SALLAH DA NA SHAGALIN SUNA DA BUKUKUWA.
ATAMFOFI, LESHINA, MATERIAL, SHADODDI, YADUDDUKA NA MAZA DA NA MATA, JAKKUNA DA TAKALMA.
WANI ABIN SAI KUN ZO TA RASULU MULTIPURPOSE DOMIN KASHE KWARKWATAN IDANU.
ZAKU IYA TUNTUƁARMU A WADANNAN NUMBOBIN.. 08086639163 - 09030168590.... MUNA DAKON SAYAN DAI-DAI KO SARI.....

*014*
Tana fito da ita ya kalli yarinyar, kafin ya riko hannunta har waje. Ya ja Alhaji Mamman Ba'are gefe. "Gata nan, ka da ka duba lalacewar da nayi ka hukunta ta da shi, wallahi billahil azim mahaifinta shahararren Malami ne kuma attajiri ne, soyayyar da take min tun tana yarinya yasa ni tawowa da ita yawon bariki, Sa'adatu bata rasa kome ba, hatta abinda zata ci Ubanta ya tanada mata, wallahi rashin ji ya sani fitowa da ita, Ba'are don Allah kada ka cutar da ita babu ruwanta."
Duk da zuciyarshi ta motsa akan yadda ya mishi da farko amma kuma yadda yake gaya mishi inda yarinyar ta fito sai yake ganin kamar bai mata adalci ba, amma halin Nasiru Wodabbe yasa shi jin ko kad'an baya tausayin yarinyar domin baki daya bata wuce shekaru goma sha shida ba, haka ya kad'e babbar rigarshi ya ce mishi. "Nasiha kake min ko me? Ka sani babu abinda ya dame ni, daga yau har zuwa ranar da zan gama amfani da ita a caca na ciyo ta."

"Na roke ka kada ka cutar da ita, don Allah. Ita bata maka kome ba ni nayi laifi." Ya fada yana niman durkusa mishi. "Abbati kada ka durkusa mishi, Indai akaina ne wallahi bana tsoron duk abinda zai faru kuma bana fatan naga hawayenka. Duk abinda kayi a kaina Abbati daya ne, ba zaka tab'a cutar dani ba." Cikin wani irin tashin hankali ya riko hannunta. "Ba zaki fahimci me na aikata ba, sai dai duk rintsi kada ki manta da Allah." "Ke muje, na gaji da wannan wasan kwaikwayon naku, sai kace uban wani ne yasaka shi saka ki a caca." Haka Alhaji Mamman Ba'are ya sako ta a gaba har inda motarshi take. A lokacin yana da wani aboki wanda suka taso tun suna agadaz daga baya shi da iyayenshi suka koma marad'i da zama. Wato Alhaji Abubakar Abzin.

Duk da shi yayi karatun boko, can marad'i yayi tunanin kai Sa'adatu domin a can zata fi sakewa. Haka kuwa ya faru domin daga Libya kai tsaye marad'i ya wuce da ita, a lokacin da Alhaji Abubakar Abzin ya ganshi da ita, ya sha mamaki amma sai ya nuna ba wani abu bane, domin yasan kulafuncin niman haihuwar d'a Namiji da yake, bai kai burin shi na niman mace mai ilimi ba, sai gashi ya samo yarinya karama me ilimi da nutsuwa.

Bayan sun kebe da Alhaji Mamman ya labarta mishi duk abinda ya faru. Sannan ya mika mishi takardunta, ya duba sosai ya ce mishi. "Kai ne dan boko, duba min ta ina yarinyar nan zata tayani rike kamfani na?" Ya tambaye shi yana leken takardar.
Gyaran murya yayi kafin ya ce mishi. "Yarinyar bata da matsalar kome, sai dai tana da fahimta ta bangaren kimiyya, idan da a zabinta zaka tambaya ba zai wuce ta ce zata karanci likitanci ko unguwarzoma. "

"Tow ina niman wanda zai rike min kamfani ina zan barta ta tafi asibiti, duba dai da kyau." Ture takardar Alhaji Abubakar Abzin yayi ya ce mishi. "Maganar gaskiya, idan har kana son ta zama yadda kake so, dole sai ka nisantatta da wannan rayuwar, ka kaita wani wurin ta rayu tayi karatu. Domin idan tana cikin matanka da danginka kishi da damuwa ba zai barta ba, sannan ita ce karama kowa zai zo mata da fitina da baƙin kishi. Don Allah ka nisantatta da gidanka ban ce kada ka kaita ba, zaka iya kaita amma kuma dole ka rabata da su. Domin kuwa matuƙar tana cikinsu ba zata yi karatun ba, kuma ba zata baka abin da kake so ba, karshe ta haifa maka yaran da kake so babu ilimin da kake bukata, zaɓi yana gare ka." Ya faɗa mishi yana gyara zaman shi, ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce mishi. "Kana nufin na dauketa daga cikin gidan kenan?"
"Duk yadda yayi maka."
"Shi kenan zan d'auketa amma ina zan kaita?"
"Nigeria, kano idan ka kaita can in sha Allah zata dawo maka da abinda baka zata ba."
Shiru yayi kafin ya sauke ajiyar zuciya, "ya zan yi da Nana?" Shiru Alhaji Abubakar Abzin yayi kafin ya ce mishi. "Nana ka ɗauke kai akan wani abun da take amma batun yarinyar nan ka tsaya kai da fata ka bata ilimi idan ba haka ba, gidanka duk jahilai za a ayi ta haifa maka. Karshe ga hanyar da za a ci abinci amma kuma babu damar cin abinci, sai dai a kashe kamfanin a zauna a haka. Amma a ƙalla aka samu mace daya da maza biyu zasu jagoranci kome da yardar Allah."
"Shi kenan in sha Allah haka za ayi." Ba don Allah ya bashi aboki na gari ba, tabbas Alhaji Mamman ba'are haka zai kaita cikin iyalinshi babu wani tsari ko plan. Sannan Alhaji Abubakar Abzin ya kara mishi kwarin gwiwa na ya tsaya akanta kai da fata, domin yasan Mahaifiyarshi ba karamar shu'umar mace ba ce, idan bata son mutum. Sannan yana son yadda yarinyar take da nutsuwa koda Allah zai bata haihuwa da Alhaji Mamman Ba'are, ya kasance Yaran sun fita daban.
Chapter 28 · 0% Book details