← Book details Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 138

Sashe 11

Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dariya nayi mata, sannan na cigaba da karyawa ta, har na gama ta balla min maganin da na gani ta Ciro a lock din gadon ta mika min. Da ruwan tea na sha ina son tmbayarta Addah amma nasan halinta bai zama dole ta bani amsa ba.
"Ya Addah take?"
"Lafiya lau!" Kallon fuskarta nayi naga kamar a dakile. "Wani abu ya faru ne?" "A'a." Ta fada tana leka wayarta, kawai na sha jinin jikina haka kawai Zuzu ba zata sauya ba. Sai na share kawai ban ce mata kome ba.
Tuna abin da ya faru a komawarta gida yasa baki daya, ranta ya kara b'aci da maganar Zahrh
Lokacin da ta koma gida, ta samu Addah tayi bakon wani mutum, tunda ta gansu a dakin Addah tasan mutumin ba na alkhairi ba ne, duk da ba yau din ya fara zuwa ba, sai dai kuma zuwan shi na yau kamar niman shi aka yi, shi din d'an bori ne. Haka yayi ta tsalle yana ihu, kafin can ya fara gyatsa. Ya fashe da dariya, yana nuna Addah da hannu. "Tabbas baki da arziki a jikinta a yanzu, sai gaba zaki ci arzikinta sama da yadda kika zata. Ƙaddara ta hadata da shi, maza ki nisanta ta daga wannan duniyar zuwa wata duniyar, domin kuwa kika sake suka kuma haduwa ba zaki kara morarta ba har abada."
"Nazimu ya zanyi? Ita Zulaihah bata da gobe ne?" Ta faɗa a hankali. Gyatsa ya sake yana dariya. "Gobenta yana manne da yarinyar da take asibiti." A dame ta kalli Nazimu ta ce mishi. "sauran yan matan fa?" "Hmmmm! Itace inuwarsu."
"Babu yadda za ayi a mallake min ita?" Shafa gemunshi yayi ya ce mata."ba zan iya wannan aikin ba,lokaci na zuba da zaki amfana da rashin haka, idan aka mallaka miki ita ba zaki tab'a samun biyan bukata ba."
"Nazimu kace na dauketa daga nan?" Gyad'a kai yayi yana gyatsa. "In sha Allah wani sati zamu wuce Taraba!"
"Dakyau. Ki nisantatta da nan domin zai bincikota."yana gama fadar haka ya fara kwara amai, nan Addah ta fito ta gaya musu zasu tafi Taraba, shiru kowa yayi a cikinsu. "Addah kinsan muna zuwa za a fara maganar munki aure fa."
"Ba zamu wuce kwanaki uku ba, tunda zamu bi motar dauko shanu ne,iya kwanakin da zamu yi uku ne, idan kuma kuna son zama anan shi kenan "
"A'a zan tafi naga Yakumbo na kwana biyu ban ganta ba."inji Ummi,
"Nima zan je na ga Nenne na!......
#Thedambuje
[2/16, 9:24 PM] Cutie cutie pie: *BAƘIN HAURE....🐾🐾*

{Greed for Money is the roots of all evils🫀}
Arewabooks:maidambu41
Wattpad:Mai_Dambu
Mallakar:Mai_Dambu

*ZINARIYAR MACE⚡*
*Wai shin 'yar'uwa menene matsalarki? zubewar nono, ko kuma rashin kwankwason juyawa a falo maigida ya shiririce ya manta da tibi da matan tictok, menene matsalarki ne? rashin ni'ima ko kuma mugun sanyin da ya yi miki katutu, shin rashin taushin fata ne ko kuma kuraje da tabbani, ko bala'in ramar da ta addabeki kuma babu rashin ci ba rashin sha a gidan auranki, gwaigwayewar gashi ce matsalarki ko kuma kaushi da faso na tafin kafa da bushewar fata, kina bukatar fatarki ta yi glowing kalarki ta fita kuraje su mutu, ko kuma kina bukatar azababbun turaruka da humra tare da turarukan wuta. Na san dai kuna da yawa matan da tumbi ya yi musu karan tsaye ina nufin ya katse muku hanzarin yi wa maigida gwalli da muskuce-muskuce a falo😃 Nesa fa ta zo kusa AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE sun tanadar muku da nau'in magungunan da suke magance kowace irin matsala da izinin Allah. Babban burinmu shine sha'ani na aure ya inganta a samu daidaito. Muna da.*
Na gyaran nono.
Na sanyi.
Dilka tare da hadin sabulu.
Duk Wani nau'in maganin mata.
Humra turarukan wuta perfumes, original miski tahra 3in1, ciccibi budurwar kaza. Had'addun supplement irin wad'anda ba su da matsala. Maganin Sliming wato narka tumbi. Abubuwan da muke sayarwa suna da yawa, kuma babu asarar dukiya. Muna garin kano kuma muna tura kayanmu kowane gari fad'in Najeria da Nijar har ma da kasashemn ketare. Kai tsaye a tuntu'bemu ta lambobin wayarmu domin karin bayani.
*08089965176*
*07084653262*
*006*
Juyawa tayi ta kalli Zulaihah,kafin ta ce mata. "Baki da ra'ayi ne mu barki anan?" Murmushi tayi iyakarshi lebbenta. Ta ce mata. "Ina da ra'ayin idan na tafi nima ba zan dawo ba, aure zan yi domin na samu mijin aure " dariya Addah tayi sannan ta ce mata. "Ta yaro kyau take bata karko, Allah ya kai mu zulai." Har ta juya zata tafi ta ce mata. "Ki sani matukar muka tafi kika zauna a can, duniya sai ta san me kike aikatawa balle mijin da nake da yakinin shi kike hari." "Addah barazana kike min?" Itama ta mike tsaye, tana kallon Addah. "Kashedi nake miki, kuma idan na miki barazanar ai ba laifi ba ne. Saboda ai da kome nawa kika kawo haka, sannan idan nace zan miki barazana ba laifi ba ne." sannan ta juya ga Ummi ta ce mata. "Ko nayi laifi a cikin wannan maganar?" Girgza mata kai suka yi, domin Allah ya zuba musu shakkar Addah idan ka cire Zulaihah, da sam bata shakkarta, ɗakinta ta koma ta kalli Nazimu. Kamar zata fashe da kuka. "Yarki bata da matsala, halayyarku ce da bambanci, ita ba zata iya abin da kike yi ba, domin tana da kirki da nutsuwa shi yasa halayyarsu da jininsu ya hadu da Yarinyar can, don haka ina baki shawara da kada ki sake, ki takura Yarki domin duniya ki sarara mata."
Gyad'a kai tayi tana faɗin. "Itama tana da farin jini fa." "Eh mana, amma kuma kila yawan takurar da kike mata zaisa ta iya rabuwa dake na har abada."
Dafe kirji tayi tare da cewa. "Don Annabi?" Wannan ne karon farko da Addah ta kira sunan Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama,domin ba dabi'arta ba ne kiran sunan Allah. Yadda Nazimu yayi kasa da murya yasa ta nutsuwa tana sauraron shi, sannan can yana gamawa ya mike ya fita, Munaisah ta shiga dakin ta gyara, "Ya gaya min maganar chef yace wai yau ki saka wannan turaren zaki samu alkhairi sosai a wurin shi."
"Kai Addah ni ai mota nake son ya saya min." "Banza sakarya motar kaniya, idan kika samu kudi saniya zaki saya da shi a fara ajiye miki."
"Kuma haka yayi fa, Addah ya batun Zahrah?" Tsaki tayi tana tab'e baki, zata tafi can ta hadu da wancan dan iskan Yaron, su kare kalau ni ina zargin anya Yaron nan bai gama lalata Zahrah da take jin ba zata iya wani abu sai da shi ba." Addah ta faɗa tana kallon Munaisah, "Uban waye ya sani, shegiya munafika ni ban son tayi aure domin haka zai saka a samu a gaba da munki aure sai zaman bariki." Shiru Addah tayi tana kallon Munaisah ta sake murmushi ta ce mata. "Da ni kuke zancen, ki bar kome a hannu!"
Daidai shigowar Zulaiha. "Wa makaru wa makrallahi wallahu khairar makiri." Tana fadar haka Addah ta zuba mata idanu, "zan tafi asibiti."
"Allah ya tsare." Juyawa tayi ta fita, amma ranta soye yake...
"Ke tunanin me kike yi ne haka?" Tab'e baki tayi tana faɗin. "Babu kome!" Ta fada tana kallon wayar. Ba zan iya ganinta cikin wani yanayi na Kyaleta ba, don haka na ce mata. "Zuzuna gaya min!" A hankali ta d'ago kai tana kallona kafin hawaye ya zubo mata."Zahrah kin ji dadinki,tunda kike baki tab'a zina ba, sannan baki tab'a yarda kin lalata tarbiyyar da Kawu shad'ari ya miki ba, Zahrah wani sakayya zan bawa mijin da ya aure ni?" A hankali ta fashe da kuka, sosai tana yi tana karawa. "Kada ki manta Allah xai baki mijin da zai kauna ce ki a duk yadda kike, kin ga yanzu da kin yarda kin amince kin koma diplomar nan, ai da yanzu saura watanni zamu gama, na gaya miki ba zina yake bada abinci ba, a'a yarda da Allah, Zulaihah kin bi na Addah kina lalata gobenki, bayan su mazan abin da yake jikinki suke bi idan suka gama dake zasu gudu."
"Ya zanyi?" Ta fada cikin kuka, tana kara jin tsanar kanta. "Kiyi hakuri kawai." Na fada mata, a hankali ta warware min tafiyarmu taraba, amma kuma tana jin addah tana kulla min sharri. Murmushi nayi na ce mata. "duk abinda Addah zatayi, ba zata hana Allah ikon shi ba, don haka ta gama abin da zata yi saura ta barwa Allah ikonsa."
Daga haka muka cigaba da hirarmu.
**
Kwana biyu mai kyau aka yi ana bata kashi a tsakanin, Captain da yan tada kayar baya, kafin aka fitar da su Commodore Magaji Abba, wanda yaci bakar wahala. Sannan sojojin ruwa da na kasa suka kame sauran yan tawayen aka tafi da su, a daren ya dawo gida a gajiye anyi anyi ya tsaya a asibiti amma ina, domin shima akwai rauni a jikinshi, yana shiga ya samu Aryan yana kwance a falon. Wucewa dakinshi yayi ya nufi ban daki ya shiga cire kayanshi, yana gamawa ya ga inda aka harbe shi biyu saboda bullet proof da ya saka ne basu ji mishi rauni ba, wanka yayi ya fito ya sha magani, ya sauke salolin da yake kanshi. Sannan ya fito ya hada tea ya sha, kafin ya dawo daki ya kashe wutar gidan baki daya, akwai yarda da Amana a tsakaninsu da duhu.
Chapter 11 · 0% Book details