← Book details Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 87 OF 138

Sashe 87

Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Kallon shi tayi cikin tsananin tsoro ta ce mishi. *Me yasa sai ni?*
Dariya yayi har yana tari ya ce mata.
_Saboda bakiɗaya kamfanin mutum daya sukewa aiki! Ba a karkashin Majid suke ba umarnin Sajjid suke bi, domin ya saye su bakiɗaya._
*Meye?* Ta faɗa tana zare idanu.
_Kiyi ƙoƙarin, gano yawan masu aiki da Sajjid na fitar da manyan cikinsu gashi nan a ciki sauran kuma zaki iya zakulo su._
Ajiyar zuciya ya sauke tare da Mikewa, sai kuma ya durkusa yana ta aman jini. Ya sani ya jefa rayuwarta cikin hatsari, amma zata iya taimaka mishi. Sai da ya gama ya mike.
Irin wannan azabar Alhaji Mamman Ba'are yayi ta ji, lokacin da aka yi ta zuba mishi guba yana ci, da ajali ya zo yayi ta kashin jini, Maisarah da bata san hawa ba. Bata san sauka ba itama an kashe ta hanyar karya mata wuya. Shine na ukun da yasan waye yaƙe bibiyar gidan.
Yasan Sajjid da Tani ba su ne matsalar Familyn ba, asalin masu fitinar Familyn yan cikin gidan nan ne. Sannan abin da yasa suke wannan fitinar don gadonsu yafi nasu yawa ne, sannan sai wasu daga gefe can.
Zubar da kashin jinin yayi ya wanke banɗakin da maganin kamshi, sannan ya fito ya wuce gado yaji ruf da ciki. _Zahra idan na mutu, na sansu zasu iya cewa kashe kaina nayi a'a Zahra ba kashe kaina ba ne. Ayi binciken gawata da kyau nasan ni na kai kaina, amma ban kawo a kaina cewa masifa na cilla kaina ba, Zahra a cikin gidan mu ne amma akwai dodonnin da idanun basu ganinsu kema ina jin kwarin gwiwa ne yasa na gaya miki._
Magani ya ɓalla ya sha, sannan ya gyara kwanciyarshi barci me nauyi yayi gaba da shi.

Kwana biyu da faruwar al'amarin. Ranar na futa aiki a inda muke hawa motar da zata kai ni makarantar su Amirah, naga wasu mutane biyu. Tsoro ne ya kama ni na matsa can ina rike da Amirah. Mota na zuwa na shiga da sauri. Ina shiga cikin na zauna kafin mu tashi naga daya daga cikinsu ya zo zai shiga motar. Wani mutum ya bangaje shi ya fadi, sannan shi ya shiga motar har makarantar babu wanda yayi wani motsi, ina sauka mutumin ya sauka, ya wuce nashi hanyar sai da na ajiye Amirah, a lokacin wani irin tsoro ya kamani. "Maman Amirah sugrah!" Juyawa nayi naga abin mamaki. "Aseem." Rufe bakina nayi, ina kallonshi. A hankali na durkusa a wurin na fáshe da kuka. "Akhi!"
"Na'am ina Sultan?"
Shiru yayi yana kallona, "tashi muje." Ya nuna min motar da ya zo da ita, mikewa nayi na bi bayanshi. Har cikin motar na shiga ya ja ni muna tafiya ina kuka. "Naga kamar a firgici kike?"
"Ina cikin damuwa, Sultan kadai zai iya tsaya min yana ina?"
Murmushi yayi ya ce min. "Tabbas idan yana tare da ke ba zai iya barin wani abu ya cutar da ke ba, don haka babu wanda ya isa cutar dake."

300₦
0016341139 unity bank zahra'u yahaya Ali
Katin MTN 400
#Mai_Dambu ce
[5/29, 07:47] Hlm: BHB245
Ajiyar zuciya na sauke lokacin da ya kawo ni kamfanin ya juya tare da ciro wata jaka.
"Gashi nan, waya ce da duk abinda kike buƙata. Ga wannan ki saka a hannunki duk abin da zai faru ki danna wannan abin in sha Allah, duk inda kike Allah zai kawo miki ɗauki."
Murmushi nayi nace mishi. "Da gaske?" "In sha Allah, wannan ma ki sakawa Amirah."
"Ina farin ciki." Na fada ina kallon abubuwan, "bari na shiga."
"Zan dauko miki Amirah xan kawo ta nan."
"Hmm ko zaka tafi da ita wasa, don basu son Yara a kamfanin."
"Saboda ƙurar dalma ce ba don yaran, sannan kema kina amfani da wannan facemask din."
Amsa nayi ina faɗin."Na gode sosai." Sannan na fita a motar, na nufi get din kamfanin. Ina shiga na nufi department ɗinmu. Ina shiga na samu baki dayan three brothers suna tsaye, kamar munafuka haka na wuce zuwa table dina na zauna. "Ba a koya miki gaisuwa ba ne?"
inji Aryan, shiru nayi ina wiki-wiki da idanu. "Ina kwana." "Rike gaisuwarki." Haɗiye yawu nayi, ina jin suna magana da fulatanci. a raina nace munafukai hala sun dauka kowa kidahumi ne, sai da suka gama dube-duben su sannan suka fita. "Sun zo sun ishe mu da gulma, dama an san Fulani da gulma." Inji dan daudun nan. Bance musu kome ba, har aka tashi. Na rufawa kaina asiri, na daina cin abinci a cikin kamfanin.
Chapter 87 · 0% Book details