← Book details Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 97 OF 138

Sashe 97

Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Watana uku a wannan yanayin Allah ya kawo min Yazid, kunsan yadda abin yake ne? Idan kana son ka fahimci lamarin shine kayi tafiya a cikin tsananin zafin rana a sahara, kai baka fita ba kai baka cimma tafiyar ba, ga zafin rana ga rashin ruwa kawai sai a fara ruwan sama me karfi a saharar nan,haka Yazid ya zame min. Ranar mun taso ina takawa da kyar ashe sun yi baƙin larabawa daga Algers. Na fito daga elevator. Muka yi kicibis da shi, shi da su Aryan da Amaan. Sun gama meeting ne suka fito. "Zeehrah!" Kunne na ne ya fara shuuuu, na juya abinka da wanda ya gaji ya kuma cire tsammanin ganin wanda ya sani. Kallonshi nayi kafin naji kamar kifi ne duhuwa ne ya kwashe ni, ban san yadda aka yi ba, ni dai Bayan wasu lokuta na farka, na ganshi zaune yana kallona. "kin farka?" Juyar da kaina nayi na fashe da kuka, ina jin kamar raina zai fita. "Kiyi hakuri dominki nazo akan me yasa zaki yi fushi da ni."
Sauka kayi daga gadon, tare da niman kayana. Tashi yayi naji ya bani wani irin warm hug, ta bayana "kiyi hakuri kin ji nayi kuskure ni ne ba wani ba ne kuma ba fatalwa ba ne, don Allah kada ki azabtar da ni da fushin ki." Yadda nake kukan ya sashi saki na ya zaunar da ni sannan ya shiga ban daki ya hada min ruwan wanka ya fito yana mai faɗin tashi likita ya ce kina aiki fiye da kima, ke mace ce jikinki baya buƙatar wahala. Ban dakin na nufa, shi kuma ya fita, ina shiga da minti biyar sai aka buga kofar ban dakin. "Karba!" Ya mika min kaya na amsa, na yi wanka na shirya sannan na fito da alolana. Abun sallah ya shinfida min ina fitowa nayi sallah da yake kaina, sannan na fara ƙoƙarin kwanciya. "a'a ci abinci." Haka ya zuba min abinci ya zauna yana bani a hankali. Turo kofar dakin aka yi Amirah ce da Siyamah. "Marhaba ya Sultan Yazid." "Sannu da kokari Siyamah, aikinki yana kyau." Shigowa da gudu Amirah tayi ta rungume shi. "Abihna shi ne ka daina zuwa ko?" Kallonshi nayi ya rike kunnenta yana magana dariya tayi, suka tafa. Ni ya cigaba da bawa Abinci."Abihna Mami ta koma Baby."
"Eh she always look like baby ai."tura baki nayi ina faɗin. "Ba zaka daina tsokana ta ba ko?" "Tow Allah ya baƙi hakuri." Shigowar su Hajiya ya sa na d'ago kai.har da shi ma. "Ahh bude baki." Ya damu da ni a gaban kowa zai iya bani kulawa, haka ya saka min tsokar nama, ina rufe bakina. "Baki san likita yace kina skipping abinci ba ko? Kina wasa da cikinki idan ciwon gyambon ciki ya kamaki mu na jikinki mune a wahale oya bude min na zuba miki abincin." Ya faɗa yana kara zuba min, Amirah da take bayan shi ta ce mishi. "Abina idan bata ci ba, ayi mata irin yadda, Ma Siyamah take min, sai ta ce min idan ban ci ba,akwai dodo da zai zo ya duba cikina idan babu abinci ya kai ni duniyarsu, sai naci abinci cikina yayi kato."
Dariya yayi ya juya yana kallonsu Hajiya, "Barkanku da zuwa."
"Zahrah ya jikinki!" "Inji Amaan, cikin tsananin kulawa, "da sauki." Mikewa yayi ya ce min. "Girl maza ki karasa abincin nan, kafin na dawo." Ya dauki sandarshi yana dogarawa, wani irin tausayinshi ne ya cika min rai. Haka ya fita ya bamu wuri, da yazo fita daga cikin dakin ne suka yiwa junansu wani irin kallo, kafin ya ficce daga dakin.
Tambayar ya jikina suka yi, Hajiya take tambaya na. "Me ya faru?" Aryan ya ce mata, "tana aiki sama da tunanin me tunani, bata hutu ga ciwon kafa da take fama da shi." Kallonshi Majid yayi cikin fushi ya ce mishi. "Hammayo ai gaskiya na fada, kawai don son kai da mugunta da ba zaka iyawa wani dan uwanka ba, kana yiwa yar mutane, ni a bangaren zalinci bana goyan bayanka, akan haka kahana Amaan zuwa Office dinka adalci kake yi ko zalinci, ko ina a cikin kamfanin kowa yasan kai azzalumi ne, baka da sani akan kasuwanci bai dace ka zalinci kowa ba, amma kai ita ce abar zalincinka."

Yana gama fadar haka ya fita, Amaan ma ya fita ya rage daga ni sai Hajiya. "Kiyi hakuri kin ji." "Ba kome Hajiya." Na fada ina murmushi. Shigowar Yazid ya mika min takardar sallama, "sannunku an sallame ki, kuma sun ce ki huta ko na tsawon wata guda ne, jinin jikinki ya dawo."
"Tow aikin fa."
"Karatun da kika yi, ba yana nufin ki zama baiwa ba ne, idan kina so idan kin dawo hutu zaki duba aikin idan kuma bakya so, kina dawowa ki ajiye musu aikinsu babu dole."
Kasa magana Hajiya tayi, fuskarta ya nuna tashin hankalinta, amma ya xan yi haka na mike tare da kokarin hada kayana. "Babu bukatar kiyi kome." Shi ya shirya min kayana, ya cewa Hajiya. "Ita mace abar tausayawa ce, ba laifi idan ace aikinta take yi, amma Hajiya Zahrah ba talauci yasata amsar aikinku ba, ita kanta bata bukatar kome daga gare ku. Idan yar Uwarshi aka yiwa haka hala sai ya kusan mutuwa." Sannan ya riko hannuna muka bar asibitin,
Hajiya.
Kallon Majid tayi, da ya rasa meke mishi dad'i. Shi bai ga wani kuskuren da yayi ba, amma kowa yake blaming din shi da kuskuren yarinyar can.
Chapter 97 · 0% Book details