Sashe 128
Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Hankalin kowa ya tashi musamman da suka ce basu san inda aka wuce da shi ba, sannan babu labarin inda yake, duk yadda ake tunanin al'amarin ya wuce tunanin me tunani. Sannan kuma babu wanda yake da sanin yana raye ne ko yana mace, tun ana boyewa ahalin shi har aka fada musu gaskiya ba'a san inda yake ba, gara Hajiya tayi matukar hakuri sannan ta bukaci gwamnatin kasar Nijar ta shiga lamarin Majid yana rike da kamfanin su da matar shi da tsohon ciki, yadda Hajiya ta fito tayi magana ne yasa aka saurari al'amarin tare da mai da hankali akan al'amarin Majid, Nana kuwa tayi suma ya kai bakwai an kashe mata jika, tana farfaɗowa zata ce musu ya labarin Alhajin Allah, kafin su bata amsa ta kuma sumewa, haka abin ya kasance mai dan kwarin gwiwa kenan Amaan.
Da shi aka zo Nijeriya, don bakiɗaya hankalin kowa a tashe yake. A can inda suka sace shi kuwa, Commodore Magaji Chindo ne da wasu Yaranshi suka dauke shi, asalima ba iya su ba, har da wasu manyan sojojin, don ba ƙaramin haushi Majid yake basu ba, akwai wani janar ne lokacin yana ganin yadda Chief of Army yake kula da al'amarin Majid, yasa suka tsangwame shi, sai gashi ya samu matsayin shugaban bataliyar sojojin ruwa shi yasa suka shirya daukar fansar su, musamman Magaji Chindo da yake nan babu abin da ya raba shi da mace tunda ba amfani da kayan aikinshi ba.
A hankali aka tsananta bincike a cikin tawagar Nijar har da Mohan Muhammad Mamman d'a ga tsohon shugaban kasar Nijar, shugaban kwamandan Rundunar sojojin Nijar bakiɗaya, sannan akwai mataimakin shi Ibrahim Ibrahim Khalil dan Ba'are.
Wannan gamayyar sojojin nijar sun tashi kan mutane, ana haka sai ga rundunar kungiyar sojojin Baihak Salahudeen AbdulMutallab Hatim wato Saraki, wanda ya kasance Kani ne ga Muhammad Maina, kuma abokin Majid wanda suka yi wani karatun horarwa a kasar busuwana, akan tattalin arzikin kasa da kasa. Kara iya kara mutuncin iya mutumci.
Ana cikin wannan yanayin ba ayi zato ba, sai ga tsohon dilar kwayoyin nan wato Sultan Yazid Hamir na kasar Algeriya, ya kawowa tsohon kishiyin shi taimako ba don kowa ba, sai don Zahrah wacce yake mata kallon kanwarshi. Waɗannan zaratan mazan sun zauna tare da tattaunawa. Tare da binciken kwafkwaf duk yadda ake tunanin ba zasu kai labari ba, sai ga mazaje sun zakulo inda yake da taimakon network din da yake cikin ruwan. Wanda manyan jeragen ruwan suke amfani da shi, tare da wayar da ake amsawa daga tekun zuwa gari, cikin wani irin sarrafa computer Dan Ba'are ya ce.
"Abin hari hana waya da wani, ku binciko mana shashin sadarwa." (Idan baku manta ba, Dan Ba'are a cikin Bororoji, yaƙe kuma akwai dangantaka me karfi a tsakaninsu da su Majid. )
Ai kuwa tuni layin glob suka tambayar anan headquarters su ake wayar tuni aka fara bin address din da suka turo abin mamaki sai gashi Office din shugaban rundunar sojojin suka samu nasarar isa, yana waya hankalin shi a tashe bai rufe kofar ba, yana faɗin. " Magaji ka rufa min asiri, ka dawo da shi domin idanun duniya yana kanmu."
Shiga office din Mohan da Salahudeen Saraki suka yi tare da cewa. "Idan Magaji ya haifu dan halak ya kashe Majid don Allah!" Suka kwace wayar tare da kama shi Mr Bukola, kafin wani lokaci har an binciko inda su Magaji suke aka musu wani irin shiri sojoji ta saka da ta ruwa aka tura musu men at work.
Za iya cewa an samu nasarar kama Magaji, sai dai tsugune bata kare ba, domin babu Majid babu labarinsa. Abin tambaya anan ina Majid? Ina suka kai majid? Haka suka yi ta niman shi babu labarinshi. Duk wahalar da Magaji ya sha yaƙi fadar inda Majid yake, dole aka tattara kayan Majid, suka dawo da shi domin Magaji ya gaya musu kafin su zo ya faɗa ruwa, wanda Mohan ya tabbatar karya ce. Ko kashe shi za ayi ba zai fadi gaskiya ba. Haka suka hado kayanshi har Nijar, aka bama Hajiya, wacce tayi kuka har ta godewa Allah. A hankali aka yi zaman makoki, domin kuwa an gaya musu ya mutu.
**
A hankali na bude idanuna, bayan wasu kwanaki da bansan adadinsu ba, sannan bakina yayi min nauyi kallon dakin nayi kafin na shafa cikina naji wayam, yunkurin tashi nayi aka rike ni. "Ina Ya Abdul yake?"
"Kiyi a hankali, domin jikinki da ciwo."
Komawa nayi na kwanta, da taimakon Jamilah da Mama na tashi zaune bayan likita ya duba ni, aka ce aiki yayi kyau. Sannan aka cigaba da bani kulawa, sai dai yadda basu ce min ga halin da ake ciki ba, haka ban kuma tambayar su ba. Har kwana shida, sannan aka sallame mu,. Lokacin da muka isa gida, a ranar nayi kuka kamar raina zai fita, ina son Majid so na hakika, Majid yana da kirki da adalci ba wai don ina Matarshi ba. A'a gaskiya daya ce duk abinda nake so shi yakan fini son abin ne ma, ba karamin gata ya nuna min ba, ya koya min yadda zan so shi shi daya babu sirki, idan na kalli Babyna sai naji wani irin kaunarta da tausayinta zata tashi marainiya babu uba.
Bayan wasu kwanaki Hajiya tazo, a yadda naga Hajiya na fahimci tana kewar d'anta sama da ni, don haka na tattara soyayyar da nake mishi na shiga bawa Hajiya kulawa, duk da halin da nake ciki, sai na sakata taci abinci ta sha magani don ta kwanta a asibiti suka gaya min. Watan mu biyu, da Hajiya zata koma Mama ta bani shawarar ko xan bita na zauna da ita don ta saka rai a kan Jikarta. Sa'adatu muna kiranta da Alfah, duk wanda ya ga yarinyar nan wani irin so yake mata, Zaytoonah kamar tafi sonta da yarta Mimi, sai muka raba na rungume Mimi ita ta rungumi Alfah. Zuzu,Ummi, Munaisah ya Babangida sun zo min ta'aziya da kuma barka. Watan mu uku cif lokacin har mun koma Nijar Zuzu ta haihu Hajiya da kanta ta shirya min tafiya da Zaytoonah da Barakatu, Yazid kuwa baya sati biyu yazo ganin Alfah. Haka yasa yarinya ta samu wani irin gata .
Bayan dawowarmu daga Nijeriya,. Ranar da yamma ina zaune aka ce nayi baki. Ashe sun zo har sau biyu ina Najeriya. Fita nayi na shigo su Dean ɗinmu na Makaranta da wata mata , mai matukar izza da takama duk da ba wata babba va ce domin ko ta girme ni da kadan ne, fuskata cike da fara'a na ce musu. "Mu shiga ciki ko, Barka da zuwa,
"Yawwa Zahra ya hakuri kuma?" Inji Dean ɗinmu. "Alhamdulillahi!" Muka shiga falon Hajiya, cikin girmamawa suka gaida Hajiya, tana murmushi ta ce. "Kamar na san fuskarki."
"Eh matar tsohon shugaban alkalai ba!"
"Zainab Umar Ja'e ko ? Mrs Isma'il Wodabbe."
"Eh muna tare da shi ma, dake Maimuna Mijinta yana cikin tawagar Nijar da suka tafi niman Majid ɗin "
"Allah sarki, don Allah ya shigo zaman waje kuma."
"Kece Maimunar?" Murmushi tayi fararen hakorant suka bayyana, a raina nace tsarki ya tabbata ga Allah madaukakin sarki. Sai da tayi murmushi naga zahirin kyau a tare da baiwar Allahn nan, mika musu Babyn Hajiya tayi na wuce kitchen na samu Zaytoonah tana ta haɗa musu kayan kwalama, muka kamo tare, daidai shigowar baban mijin dean. Na zata malamijo ne har nace . "Tsohon nan da gajen..." Sai nayi shiru ina zare idanu, duk da malamijo bai kaishi duhun fata ba, amma kamarsu ta b'aci. Abin tab'awan muka ajiye ina kallonshi. "Yarinya kin san me kama da ni ne?" Gyad'a kai nayi. "Ikon Allah waye haka!"
"Mahaifina ne, Sheikh Aliyu Wodabbe." Shiru yayi kan shi a sunkuye, ya rasa me zai ce sai mikewa yayi ya ce. "Zainab idan kun gama ku same ni a waje."
"Hamma Ila!" Hajiya ta kira sunanshi. "Baka yi kuskure ba, kuma duk abin da kayi dai dai ne, amma duk abinda ya faru Malamijo yana can yana nimanka kai da Kabo, don Allah ka manta da kome wallahi iya jarabawar da muka gani ma ya ishe mu idan ka tafi hakkinku zai ta bibiyar rayuwar ahalinmu, ka duba ka gani da kuruciyarta ta rasa Mijinta, ta rasa abubuwa dayawa amma na mijinta yafi kome tsayawa a ranmu. Ga jinjirar nan ta rasa Ubanta saboda hakkinku. Don Allah kayi hakuri ka janye Allah ya bi maku hakkinku wallahi muna ganin Jarabawa "
"Kayi hakuri mana baban Almamoon, idan kace ba zaka yafe ba, Allah ma muna mishi laifi ya yafe mana balle mutum, kayi hakuri a fahimci abu ɗaya. Ni beenazir ta gaya min wai danginsu Khalil ne ashe duk ta ko ina dangine, haba shi yasa da muka hadu naji ina son Zahrah ina Yarki me rikici."
"Tana wurin iyayenta!" Na fada ina share kwalla, "Maimuna ko zaku bamu wuri ne?" Da sauri na mike itama sai da ta gama yangarta, ta mike muka haura sama, falona na kaita ta zubawa hotonmu idanu.