← Book details Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 104 OF 138

Sashe 104

Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

A ranar mun wuni cikin farinciki, har yar ƙaramar party muka yi,da yamma muka fita zuwa yawo sai dare muka dawo ai kuwa ina dawowa Yazid ya kira ni yana mita. "An ce min wancan bishiyar kukar yazo, sannan kin fita yawo. Ni fa bana son yana zuwa min wurinki."
"Ji shi kamar ba basarake ba, ko kunya baka ji ba, na ji ba zan kuma barin shi zuwa ba. Gobe zamu je damagaram," hayaniyar da naji ta wayar yasa ni kashe wyaar baki daya. Muka ci tuwo miyar kuka. Sannan muka yi hira, kafin muka kwanta.
A hankali nake tafiya a cikin duhu, "Mamina! Mamina!! Zo ki dauke ni Maminah!!" Juyawa nayi naga babu kowa sai duhu a hankali na kira sunanta. "Aminatu!" Ina waige-waige. Can na hangota a kasar haske tana kuka tare da mika min hannu, nufarta nayi naga wani wawakeken rami, Nawwas yana rike da hannunta yana tafiya da ita. "Nawwas!" Juyawa yayi ya min wannan murmushin da ya zauna a cikin kwayar idanuna. Zumbur na farka kaina yayi wani irin sarawa har sai da jini ya zubo min a hancina. Juyawa nayi naga tana ta barci, ban daki na shiga na rike hancina, ina wanke shi. Ina gamawa nayi alola na fito nayi sallah,kusan har asuba ina zaune a wurin ina rokon Allah ya kawo min kome cikin sauki, bayan na idar da sallah ne,.na wuce nayi wanka na tashe ta.
Na mata wanka na gyara mata jiki muka fito bayan tayi sallah, tazo taci abinci. Sannan muka wuce zuwa makaranta baraka ma ta shirya muka fita da ita dukkansu na ajiye su a makaranta, sannan na wuce office,.ina shiga Chairman yana jirana. "Baki yi barci ba jiya?" Banza nayi da shi, daukar jakar shi nayi muka bar kamfanin. Kaina sai wani irin sarawa yake kamar nace na fasa tafiyar amma babu hali, tunda muka nufi airport din naga manyan motar Bus.
Mata ne suke ta fitowa suna shiga cikin airport din. Haka muka shiga aka ce jirginmu ba zai tashi ba, sai an sallame waɗan nan yan gudun hijiran, wani daki aka kai mu muka zauna.
..."Ke Ummi kin ga kamar Zahra." Koda ta juya bata ga kowa ba, "ban ga kowa ba." "Yanzu ta shiga da wani Kyakyawar Bature." "Hala don bakya son tafiyar ne kike tunanin kin ga Zahra." Shiru Addah tayi don tasan Ummi ƙaryatata zata yi. Don haka tayi shiru.
Ina zaune aka kira ni, Yazid ne don haka na fara waya a dakin, kura min idanu da yayi yasa ni fita daga dakin na bar cikin airport din,.na samu wuri na xauna muna ta hira, sosai har da kyalkyalewata.
Sosai muke hira fa, abin gwanin ban sha'awa. Ina gamawa na juya na koma ciki.
"Ke Ummi kin ganta fa!" Ta nuna mata bayan Zahrah. Tsaki Ummi tayi tana faɗin. "Kama ce kawai amma babu wata Zahrah anan" ita Addah ko cikin dubu ta ga Zahra zata gane ta amma Ummi sai Musa mata take haka yasa tayi shiru tana kallon ikon Allah.
Ina shiga ya kalli agogon hannun shi, "minti ashirin fa, fisabilillahi idan da adalci wannan lokacin yayi tsawo dayawa. Ki gayawa dan kwaryan nan ya daina kira a lokacin aiki bana so." Ya mike ya fita abin shi yana mita, wannan mutum da mita yake, haka ma Yazid mita na rasa gane kan wannan al'amarin kowa mita sai kace Yara.
Bayan fitar shi na cigaba da duba, makasudin zuwan mu damagaram, ina dubawa ina tura sakon ta Email din shi, har lokacin bai shigo ba, ina cikin yi naji gabana ya fadi. A hankali kalaman Baffa'm yake dawo min raina kamar a mafarki. _Ki yiwa zumuncin hidima_ iska ne ya cika min bakina da hancina, dakyar nake jan numfashi, Allah ya taimaka sai gashi ya shigo dakin. Da sauri ya mika min ruwa na Sha. Na dafe kaina ina jin wani irin sarawan da yake yi, ga faduwar gaba da nake ji, d'ago kai nayi yaga jini na bin hancina. Mika min hanky yayi na tare jinin hancina. Kiran waya yayi yana faɗin. "An janye meeting din nan, zuwa wani sati." Sannan ya kashe wayar. "Muje asibiti." Girgiza mishi kai nayi, xan yi magana kamar wacce aka cika min bakina da abu haka na zube kasa, ina aman gudan jini. Durkusawa yayi a gabana ya janyo ni a jikinshi. "Zahrah baki da lafiya ne?" Sai da ya bani ruwa na sha, sannan ya d'ago ni na zauna da kyau yana min fifita. "Ina ke miki ciwo?" "Babu ." "Ina ke miki ciwo?" Ya faɗa min da karfi, "kirjina da kaina!" "Zahrah kina yawan tunani ko? And da alamu baki yi barci ba jiya. Tashi mu tafi asibiti."
"Chairman " "a'a Chairwoman! Oya tashi."
"Ciwo ne fa daga Allah kawai zan ji sauki."
Riko ni yayi a hankali ya kwashi kayan muka bar dakin, a hankali yake tafiya dani, har muka iso inda yan gudun hijiran suke dab zamu fita naji an kira sunana da muryan da ko A barci na tashi ba zan manta da shi ba "Zahra'u...........
300₦
0016341139 unity bank zahra'u yahaya Ali
Katin MTN 400
#Mai_Dambu ce

[5/29, 07:47] Hlm: BHB256
Ji nayi numfashina kamar ya bar gangar jikina, daganan wasu abubuwan ban sani ba sannan ban san ya aka yi muka zo asibiti ba, sai farkawa da nayi rike da kaina. Dube -dube na shiga yi yana kallona. "Kina niman su ne?" Lumshe idanu nayi tare da ware su akanshi. Tabe baki yayi yana faɗin. "Suna can hukumar shige da fice na kasar nan, na ce a ajiye min su."lallai ina son ganinsu." Na fada jiki ba kwari, kuma na kasa tashi. Wani irin kallo yayi min kafin ya ce min. "A haka zaki je wurinsu? A haka zaki ki gansu? Don't fool yourself, kin san ba zan barki a wannan lokacin ki fita ba oya koma ki kwanta." Ya saka safar hannu, tare da ɗaukar allura ya fasa ya ja ruwan ya saka a cikin wani kwalbar magani, "don Allah kada ka min allura."
"Idan ban yi miki allura ba me kike so nayi miki?"
"Ni bana so." Jijjiga kwalbar yayi sannan ya ja ruwan cikin kwalbar yayi min allurar, "baka da imani, duk yadda naso kada ka min allurar sai da kayi, ita wanna matar Yayar Babana ce, ita wannan ta kusa da ita Ummi yar uwata ce, ina son na gansu gashi ka min allura taya zan gansu wannan ba yi ba ne. Bana son wahalar da zuciyata ta sha, bana fatan wani ya sha irinshi. Na tashi ban san Mamana sosai ba, ta tafi ta bar ni. Na gama Secondry aka tura ni wurin Addah a river, a can ne zan yi karuwanci na ci abinci......" Yarrrrr yaji kamar an zare mishi laka, ya kura mata idanu. Bakiɗaya tausayi take bashi yanayin ta irin na mutanen nan ne masu matukar hakuri, da son nasu.
"Allah ya baƙi hakuri sleeping beauty." Ya faɗa yana murmushi, yana shafa kanshi.
Daukar wayar shi yayi, "Waɗannan mutane biyun please a kawo su Ba'are guest house." Daga haka ya koma ya zauna, yana zaune yaji kar'ar vibret na waya. Duba jakarta yayi ya ciro wayar, "My King!" Wani yatsina fuska yayi yana wani kyabe baki kamar ya ga kashi. Kashe wayar yayi bakiɗaya, tare da jan tsaki. "Tsuk!" Ya cigaba da zamanshi. Ya tsani gayen nan.
**
Yazid.
Ganin kiran da yayi bata dauka ba, yasa shi kiran mutanen shi, ya tambaye su. "Ina Zahrah?" "Ta tafi damagaram." "A'a bata da lafiya." Domin jikinshi ya bashi bata da lafiya, tashi yayi yana zaga office din shi kafin can ya kira pilot ya ce. "A shirya zuwa Nijar!" Shiga dakin da yake sauya kaya yayi ya fito, ya shirya tare da barin office din shi na cikin fadar masarautar. Ana ganin fitowar shi aka dauko Motarshi. Ya shiga biyo shi manyan masu mukaman fadar suka yi. "Sultan ka manta yau ne." "Na har baya da kura." Ya faɗa yana zuge glass din motar, shi kan ya gaji da wannan masifar mulkin yana son yayi rayuwa cikin yanci da walwala.

Suna isa inda jirgin masarautar yake ya fito, ya shiga tare da barin masarautar shi bai son hayaniya shi yasa ya zabi rayuwarshi. Yana isa ko minti biyar ba ayi ba, suka bar fadar, shi ya tsani damuwa, yana shiga ya lumshe idanunshi, tafiyar awa uku, ta kai su kasancewar jirgin karama ce, haka yasa koda suka isa kai tsaye a airport ya fara baza nimanta, wani ikon Allah anan ya samu ganinsu Addah domin akwai cctv, haka yasa shi jin wani irin takaici,ganin yadda Majid ya tsaya aka ciro su cikin layi ya saka hannu. Wannan bakincikin da me yayi kama, Majid yasan bala'in Addah ba ne.
Haka ya juya tare da nufar Ba'are Clinic, yana shiga kamar sun san da zuwan shi aka mishi jagora har dakin da take, yana shiga ya samu tana barcin magani.
Chapter 104 · 0% Book details