Sashe 4
Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kai tsaye headquarters dinsu ya nufa, anan ya hadu da Commodore Magaji Abba Chindo, kanshi ya sunkuye yana kallon kasa. "Kun san abin da ya tara mu, mun samu labarin za a fitar da mai ta ruwa. Aikinku shi ne ku dakushe yunkurin yan tada kayar baya shine aikinmu,mu mazaje ne a fagen yaki idan kunso idan kun koma cikin matayenku tow ku daura zanin matayenku,kune kuka sani ba mu ba ku ajiye personal emotion dinku domin dakile aikin yan ta'adda. Muna da Kyakyawar yakinin duk wani sojan kasar nan yana tsaye ne domin bawa al'umma kariya da taimakon gaggawa. Yan kasa ne kaɗai zasu fahimci yadda tasirin kishin kasa yake kun ji ko? Kada wani yayi harbi idan muka kama su, aikin mu shine mu kawo su headquarter ba kashe su ba, domin suma fararen hula ne."
"Yes Sir!" Suka fada da karfi. Sannan suka wuce inda aka ajiye mota, suka shiga shi kam bai wani damu da ya shiga gaba ba, yafi damuwa da baya, haka wani sub-Lieutenant ya bude mishi gaban mota ya shiga, har zai zauna Magaji Abba Chindo ya zo daidai kunnen shi. "I hope kayi ban kwana da danginka! Domin bana fatar ka dawo a raye."
D'ago kai yayi yana murmushi, ya ce mishi. "Kai ne bakon mutuwa!" Ya faɗa yana murmushi. "Wannan murmushin sai ya zame maka mutuwa." Yar dariya yayi ya ce mishi. "Ban sani ba, idan akan aikin da kasan idan na bari ba zai kare ni da kome ba, domin kuwa hmm!"
"Domin me? Kai da aka watsar da kai." Juyawa yayi ya kalli MAC. A fusace yake amma kuma baya jin zai yarda su yi faɗa. Sai ya dauke kanshi yana me kallon gefen driver. "Muje ko!" Wato daga cikin abin da Allah ya hore mishi iya sarrafa fushinsa.
Zai yi wahala ka ga tunzurar shi, idan kuwa ya tunzura yana zame mishi mugun yanayi ne mai matukar tsoratarwa, shi yasa baya son fushi baya son fada, baya son hayaniya, yana ajiye kanshi da yanayin shi a wani aji na musamman. Fushinsa ba haka kawai yake yin shi ba. Maganar Magaji bai dauke ta a bakin kome ba. Har suka bar headquarter suka nufi bakin ruwa. A ka'idar operation Anaconda, kome suka hadu da shi, lakwame shi zasu yi amma daga abinda Commodore Magaji Abba Chindo ya a gaya musu ba a basu damar harbi ba, ba a basu damar kome ba sai dai dakile fashin da za ayi, a motarsu na tafiya kai tsaye ya kira Admiral shugabansu.
"Sir wannan mission din yana da matukar hatsari, idan muka samu kanmu cikin tarkon makiya ya zamu yi? Kasan masu wannan aikin suna dauke da miyagun makamai, sir a bamu damar kare kanmu da rayuwarmu don Allah a tura wannan sakon zuwa ga Oga!"
Admiral duk da ba musulmi ba ne, yana matukar ganin girmanshi, musamman yadda yake da jajjircewar aiki, daukar kasada a kan kowani aiki. Infact shi yana cikin SISA, wato (special intelligent Soldier Agent) sannan ya ajiye haka a matsayin personal life din Yaron, ko wannan operation Anaconda plan din yana cikin sojojin da suka kirkirota musamman yakin south south. Sannan asalin labarin daga bakinshi suka jiyo shi, haka yasa suka kara bincike aka tabbatar za a fita da mai ta teku. Shi yasa aka tura su.
"Ku kare kanku, idan kuka faɗa tarko!"
"Yes Sir!"
Commodore Magaji Abba Chindo, kiran wasu sojoji guda uku, ya umarce su da su je har gidan da ya dauko yarinyar nan, su ci uban Uwarsu, kada su d'aga mata kafa.
**
Unguwar hausawa.
Koda yake ana kiran unguwar ce da sunan unguwar hausawa, amma a zagaye yake da Musulmai da kiristoci, musamman inyamurai. Tun karfe shida na safe ya dace a ce an dawo da ita, amma shiru har karfe takwas.
"Ada wetin happen? I see you dey pass up and down, shebi your Ethiopia girl neva come back?" Inji wata Beyarabiya, cikin takaici da bakinciki Adda ta ce. "Bise kyale ni da yar iska haihuwar asara, me aka yi da haihuwar bakinciki, shad'ari ya haifa mana irin masifa, kaf cikin al'ummar fulani babu miyagun iri kamar anagamba." Ta faɗa tana watsa hannu. Fitowar wata budurwa daga wani daki tana yatsina fuska ta ce mata. "Addah hala irin masifa bata dawo ba ko? Kowa na fitowa bariki arziki ita wannan a barikin ma tsiya da masifa take kara janyowa kanta. Kuma wallahi sojan nan bai da mutumci, ba lallai ya saka condom ba, a tsarinshi baya saka condom. Shi yasa lokacin da ya tab'a daukar Ummi ta dawo tana ta mita, domin tace bata da infection dan shegiya ya zuba mata, mugu. Tow gashi ya dauki Zahrah."
Kwafa tayi tana faɗin."ai ni ban ga amfanin haihuwar Zahrah ba, shegiyar yarinya ta dauko bakin jinin Uwarta. Ke kan ai Munaisah kyanki jarinki gaki tabarkallah, ita waccan yar iskar."
Fitowar wasu yan mata da kayan barci, yasa tana kallonsu. "Zully kin tashi?" Dauke kai tayi kamar bata gansu ba, ta koma dakin ta dauko brush da marclean, ta kuma fitowa. Bakin magudanar ruwan ta tsuguna tana wanke bakinta. "Zulaihah hala laifin tura Zahrah kwanan waje ko?" Nan ma bata tanka mata ba. "Daurawa kai jaraba, wai tana jin haushin abin da ya faru ne?"
"Munaisah babu ruwanki da ni, domin zan ci mutuncin ki." Inji Zully din. Kumshe dariya tayi tana faɗin. "Bani na kar zomon ba, yau wata yarinya zata sha wutsiya gatar gato!" A fusace Zulaihah ta wuce bata kula su ba, sauran yan matan suna mata dariya, domin a duniya rayuwar Zulaihah idan za a ce ta bada shi domin ta kare Zahrah zata bada. Ta tsani irin rayuwar da mahaifiyar take daura yan mata a kai, suma dake son abin duniya da kwadayi yasa suna bada jikinsu me daraja, suna fadawa bariki.
Tashi Addah tayi ta nufi banɗaki ta kama ruwa, sannan ta fito domin ka'idar kiran wayar Mahaifin Zahrah karfe goma na safe, ji tayi kamar zuciyarta zata buga domin karfe goma saura. Wannan wacce irin masifa ce Zahra zata cillata cikinshi? Tunda take kawo yara babu wacce ta tab'a wuce shida na safe bata dawo gida ba, sai Zahrah. Abin karyawa suka yi baki daya taliya da mai da yaji, sai Zulaihah da ta fasa kwai da sadine ta soya da yar attarugu da tumatiri sai albasa, ta shiga daki ta ajiye musu tasan idan ba wani lalura ba, babu yadda zaayi Zahrah ta kai wannan lokacin, idanunta yana kan wayarta, duk wani motsin lokaci tafiya yake da sautin bugun zuciyarta.
A hankali ta kara rike wayar, goma tana cikawa wayar Addah tana kara. Jikinta na rawa ta fado dakin. "Zulaihah ban san me zan gayawa Shad'ari ba, don Allah taimaka ki mishi karya wallahi nayi danasanin turata."
Amsar wayar tayi cikin sanyin murya ta ce. "ina kwana Kawu?"
"Lafiya lau Zulaiha, ya kwananku da na Addah?"
"Lafiya lau Kawu!"
"Ina kawarki?"
"Baffa yau makaranta sun tura su, wani nazari sai nan da kwana uku zasu dawo in sha Allah."
"Tow Masha Allah, Ubangiji ya dawo da su lafiya, Zulaihah don Allah ki kula da Zahrah kin san yadda take bata ji, sai anyi da gaske." Murmushi tayi tana faɗin. "Kawu Indai akan gaskiya ne, ba zan gushe bata goyan baya ba, har sai na koma ga Allah."
"Allah ya muku albarka!"
"Amin Ya Allah, Kawu har yanzu babu labarin Ammynmu ne?" Shiru yayi kafin ya ce mata. "Na tafi har ye'ude ban samu wani labarinsu ba."
"Allah sarki Ubangiji ya bayyana ta!"
"Amin Ya Allah, ya Munaisah ita ko wayar ba zata yi da ni ba ne?"
"Bari na mika mata." Ta mike zuwa waje, ta mikawa Munaisah. "Baffanku!" Amsar wayar tayi ta saka a kunnenta. "Barka dai Baffa."
"Hmm! Ke Wato sai na nime arzikin magana dake, amma ina jin kina kiran Innarki ko?"
"Kayi hakuri Baffa!" Ta fada tana wani had'e rai, Indai zata yi waya da shi tow bata sake jiki tayi wayar kamar yadda take da innarta......
#thedambuje
[2/16, 9:24 PM] Cutie cutie pie: *BAƘIN HAURE....🐾🐾*
{Greed for Money is the roots of all evils🫀}
Arewabooks:maidambu41
Wattpad:Mai_Dambu
Mallakar:Mai_Dambu
*003*
*Zahrah*
Lumshe idanuwa na nayi ina kallon dakin da nake, gari ya waye garai sake lumshe su nayi na kara tabbatar da inda nake, amma wani ikon Allah na kara fahimtar ashe ba lahira aka kai ni ba, a duniya nake, tashi na fara kokarin yi aka ce min. "Ke ki kula da ciwon jikinki mana." Kasake nayi jin mutum ce ke min magana ba daya daga cikin Mala'ikun da suka zare rayuwata ba, bani da karfi ko kaɗan don haka na ce mata. "Don Allah ban mutu ba ne?"
Juyowa tayi ta kalle ni,sannan ta ce min. "Kina da number yan uwanki?" Dafe goshina nayi ina tuna na bar wayata a dakin wancan dan iskan. "Baki ji ba ne?" Sake kallonta nayi na fara fada mata number Zully."Zero eight zero....."har karshen number, kiran layin matar tayi. Aka ce ana amfani da wayar. "Don Allah kira min wannan number." "Zero seven zero..." Lokacin da ta kira wayar ta shiga, an dauka sai dai ihun da ake yi yasa ta kura min idanu. "Ke ungo wayar kiji abinda yake faruwa." Ta mika min, ihu da kuka tare da jin alamar ana musu wani abu yasa na mike gabakidaya, nasan wasu zasu ce hala ban san halin da nake ciki ba ne?