← Book details Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 121 OF 138

Sashe 121

Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tunda aka daura auren, ta shiga dakin Addah ta ce mata. "Kina kwance yau Allah ya tabbatar na auri Kabir Lamido, don haka ina ƙara godiya ga Allah da yayi min wannan Ni'imar don ba zan lalace kamar yadda kika so ba, a kullum ina miki fatan shiriya."
Daga haka ta bar dakin, ta cigaba da kula da kanta. Babu abinda zata yi ta faɗa, sai da Zahrah ta kirata ta ce maza ta nemi wurin gyaran jiki ga nata gudunmawar, ta gayawa Majid shima ya turo mata.
•••
Babban Asibitin Poland.
Rike take da hannun Nenne, cikin kulawa tana murmushi. "Sannu Nenne cuta ba mutuwa ba."
"Ina zahra'u?"
"Tana can tayi aure."
"Yaushe?" Hawaye ne ya zubowa Munaisah. "Wata biyu kenan ana cikin na uku."
"Ke fa?" Inji Nenne, "ni wanda muke tare ba bakin fata ba ne, Bature ne."
"A'a ki auri bakin fata ƙabilarki."
"Babu kabilana da zai aure ni."
"Allah ya zab'a mana mafi alkhairi!"
"Amin Ya Allah."
Flash back.
Babu yadda Addah bata so Munaisah ta kashe Nenne ba, dake da gaske Munaisah da mugun son abin duniya amma bata tab'a jin zata iya kashe wani saboda duniya ba, sai ga Addah ta ce mata ta kashe uwar da ta haife ta, haka yasa ta samu Nurse din da yake son Zuzu ta bashi duk kudin da addah ta bata na kanta, ta bashi tace ya taimaka mata ya kula da Nenne, Zahrah zata zo in sha Allah.

Sannan ta tafi, a lokacin ba karamar wahala ta sha ba, domin har wasu sassan jikin Nenne an sayar, don haka aka dauki wata gawar aka basu, shi kuma ya ci gaba da kula da Nenne, haka ya samu labarin an d'aga sansanin, yayi bakinciki sosai don haka bai kuma jin labarin su ba, sai bayan Shekara guda, lokacin ta hadu da Baturen da suke tare. Kawai ta kira Nurse din ta tambaye shi Zahra tazo sai da suka yi fada kafin ya gaya mata gaskiyar abin da ya faru babu bata lokaci tazo wurin Mahaifiyarta. Ganin halin da Mamanta take ciki ya kazanta, yasa ta nimawa Mamanta takardar barin kasar. A lokacin tasamu mahaukatan kudi, don haka ta dauki Nenne zuwa Poland a can ta cigaba da jinyarta har zuwa yanzu. Ita kanta bata zata Nenne zata tashi ba, sai gashi Allah ya d'aga kafadarta.

Don haka ta ci buri a ranta zata dawo Nijeriya, zaman kasar wajen ya isa, sai da ta hada kome nata sannan ta samu Paul da zancen zata koma Nijeriya, shi ya mata duk wani cuku-cuku ta bar kasar da Mahaifiyarta, bayan ta ajiye mishi sakon kada ya nime ta, zata fara sabon rayuwa sabon yanayi sannan yaje gidan marayun da suke zuwa akwai yarinyar da aka saka mata suna Zahrah ya amsheta Yar shi ce da ita, suka haifa bata son duniya ta sani ne, kuma bata son ta koma da ita cikin danginta yasa ta ajiye yarinyar a wurin, ya barta haka don Allah. Yaji takaici don yana sonta ne. Amma da yaji sunan Yarsu da gudu ya tafi gidan ya samu yarinyar tana da shekaru uku a duniya, lokacin da ya je har ana shirin adopt ɗinta, ya amshi yar shi, yana kukan farinciki.ita kuma dalilin ta nakin yarinyar bata san yadda zata fuskanci Nenne da lamarin Yarinyar ba, bata san yadda zata dauki batun ba, domin tana ganin idan taji haihuwa tayi da kafiri mutuwa zata yi kwananta bai kare ba.

Da wannan ta rufe shafin Paul da Yarshi.
*** Zuwa yanzu Majid ya gama rena min hankali, ban isa nayi wani kwakwaran motsi ba, sai dai naji anyi sama da ni kamar wata yar tsana, gashi wani ikon Allah yadda nayi wani azababben kiba zaka rantse da Allah wani abu nake samu kawai kwanciyar hankali da na samu ne.

Ina gyara kayan drower ɗin shi, shi kuma yana banɗaki, ina an kare d shi. Ganin wani hotonshi da wasu sojoji yasa ni shagalta da kallon, kawai sai ji nayi anyi sama dani. "Don Allah sauke ni." Na fada kamar zanyi kuka. Fadawa gadon muka yi, wannan gado ba don anyi shi da karfi ba, ina ga da karyewa zai yi wallahi. Haka ya juyo kaina. "Kasan me?" Bakinshi ya haɗa da nawa, na kasa magana duk ƙoƙarina da na kwaci kaina, amma na kasa sai na hakura na bar shi ya sakankance kafin na shammaci shi na gudu abina, murmushi yayi mai ciwo . Ya fara gajiya da iskancin Zahra, sai ya zuba mata idanu.

Ya shirya ya fita, wurin Hajiya ya wuce yayi mata hira, kafin ya wuce bangaren Nana, yana shiga ya kwanta rubda ciki. "Alhajin Allah lafiya kuwa? Ya Zahra matar wata?" Ta fada tana kallon shi. "Alhajin Allah meke damunka?" Shiru yayi yana mitsi-mitsi da idanunshi.
"Nana aure xan kara?"
"Kaci gidanku, yaushe kayi auren da zaka kara auren dan kaniyarka."
"Nana ki barni nayi auren Zahrah kashe ni zata yi." Ya fada yana kara rubda cikin. Gwalalo idanu waje tayi tare da dukar kirjinta, ai mayafi a hannu ta bar gidan, murmushin mugunta yayi yasan Nana ba zata kyale ta ba.
Ina tsaka da kwashe abinci, kawai naji an banko min kofar kitchen. "Zahrah ashe ke ba yar arziki ba ce? Na zata ke yar arziki ce da zaki bar Alhajin Allah a cikin mawuyacin hali, Anya akwai Allah a cikin lamarinki?" Yadda matar nan take shiga ba nan take futa ba, ihu da bala'i naji shi idanuna har ya cika da kwalla. Sai da naji hawaye na zuba min, "haba Zahra da hankalinki kike gudun mijinki a shimfida? Na zata wani ya gaya min karyata shi zan yi, Zahra idan Alhajin Allah bai samu nutsuwa dake ba, taya zai zama cikakken namiji me murya ɗaya? Don Allah ki cire kome ki rufa mishi asiri. Sai ya zama cikakken namiji, yana tare da makiya ba dare ba rana, idan har ya rasa tallafawarki makiya ba zasu barshi ba, sai sun yi nasara akan shi, da ace lokacin da Sa'adatu ta auri Mamman na bata irin wannan goyan bayan akan Mamman da yanzu wani labarin ake ba wannan ba. Don Allah ki taimaka Alhajin Allah ya zama namiji kamar sauran mazan "
Wato da Majid da Kakarshi, basu da kirki, amma kuma yadda take nuna min ta damu da jikanta yasa ni bata mamaki.

A bangaren Hajiya zan iya cewa bani da matsala da ita, domin duk wani abin cigaba da kyautatawa tana min, sannan tunda aka sako Amaan kusan a wurina yake cin abinci, sannan ga Nabeeha yar kawunmu matar Aryan, kusan a tare muke kai abinci. Akwai wata irin girmama juna da muke a tsakaninmu wanda haka ya haifar mana da kyakkyawar alaka. Yaranta a wurina suke zama idan suka dawo makaranta, sai Jamilah muna shiri sosai amma Anisah tana tare da Zaytoonah kamar munafukai.

Nana tana fita na wuce na karasa kwashe abinci, bayan ta bar gidan ya shigo yana marairaicewa. Kamar xan yi kuka yadda yazo min, haka ya tsaya muka gama kome na sauya kaya na kai nasu Hajiya sannan na dawo, na wuce daki nayi wanka. Bayan na gama wanka na fito na samu yana dakin, doguwar riga ya mika min. Shima shiri yayi ya wuce wurin drower na ya dauki abun da zai dauka ya ja.hannuna muka bar gidan, kai tsaye muka bar garin Niamey.

Ina kallon shi mun yi sallah la'asar da Magariba a garin Kano, daga nan muka wuce yola. Anan muka kwana washi gari ya dauki shatar mota muka kama.hanyar gembu. Wuri ne me kyau da Natural air kasancewar gari ne dajin Allah, sai ci-gaba da aka kawo garin, mun sauka a masaukin baki, Sai da muka huce gajiya sosai sannan ya fito dani muka yi ta yawo, yankin kamar ba a cikin Nigeria yake ba, kasancewar yanayinsu yayi daban da yanayinmu.
Sai sallah yake dawo damu, da dare aka kawo mana abinci, me rai da lafiya sai kayan fruit da aka kawo min na sha har na gaji, bayan sallar isha kuma muka yi sallah nafilla. Kafin nan sai da yayi min tambayoyi sosai akan Addini na bashi amsa,

Wannan daren me cike da tarihi, Majid ya koya min abubuwa dayawa har lokacin ban iya cewa ga abinda nake ji a kanshi ba, sai dai ni kaina nasan naji jiki naji yadda kowacce mace take ji, naji abinda ba kowacce mace take iya ji ba, matukar bata rike kanta ba, shima da zuciya daya ya zo min sai dai yadda abubuwan suka faru, yasa shi rufe idanun shi yayi yadda ranshi yake so dani wanda ya sani jin na fasa auren. Koda yake kowacce macen kirkin tana alfahari da wannan daren......
300₦
0016341139 unity bank zahra'u yahaya Ali
Katin MTN 400
#Mai_Dambu ce
[5/29, 07:47] Hlm: BHB267

Mutumin nan bai da imani, tausayinshi ƙalilan ne bai duba halin da nake ciki na rashin sanin kan abun ba, ya farmin da abu daya, tun karfe sha daya na dare sai gamu har wurin sha biyu da wani abu, kuka na ke wiwi kamar raina zai fita, yasha yakushi , duk na mishi bai ji ba, shagalin shi yake a wannan daren Majid ya dasa min tsoro da shakkar shi, wallahi bana jin akwai abin da zai saka na mishi rashin kunya ko wata tsiwa. "Don Allah kayi hakuri, nabi Allah na bika."
"Ba zan iya ba! Na kasa." Fashewa da kuka nayi ina ƙoƙarin ture shi, amma mutumin nan bai bar ni ba, sai da yayi yadda yake so, ina ganin shi ya mirgina daga gadon ya fadi, a kasar dakin ya kwanta rub da ciki. Zazzaɓi me karfi ne ya rufe ni, hakan shima zazzaɓin ne ya rufe shi, bakiɗaya sai aka rasa me kula da wani.
Chapter 121 · 0% Book details