Sashe 52
Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read
Yadda take kuka kamar karamar yarinya, domin Majid yana matukar bata tausayi, idan ta cire Matsalar Amaan tow Majid ya sauke kaso mai nauyi a zucuyarta. Bakiɗaya ta rasa inda zata saka hakkin Majid domin abin da ya same shi kamar laifinta ne, da bata yarda ta bi Alhaji Mamman Ba'are a lokacin ba tow da wannan abin bai same shi ba.
---
Amaan Mamman Ba'are.
Kallon juna suka yi, kamar zasu cinye juna kafin murmushi ya kwace mishi ya ce mishi. "Ban yarda da abin da kake faɗa ba." Lumshe idanunshi yayi ya bude a kan fuskar Sajjid. "Baka yarda ba kenan?" Dariya Amaan ya saka yana faɗin. "Lallai kuwa, hmm dukiyarshi bata da wani amfani tunda babu me ci haka zata yi ta habbaka yadda zamu san me zamu yi mishi."
"Hmm! Ban yarda Abdul Majid bai da lafiya ba. Na fi yarda da cewa bai da ra'ayin aure amma ace bai da lafiya ai maganar kawai tatsuniya ce." Mikewa Amaan yayi yana faɗin. "Zan tafi idan lokacin da ka sani sai ka tsaya muyi magana." Sajjid bai ce mishi kome ba, har ya bar gidan. Wani irin murmushi Sajjid din yayi, ya kira Mahaifiyarshi ya gaya mata, shiru tayi, yanzu ne ya dace ta tashi ayi ta ta kare ko kuma ayi ta kasa. Idan Majid bai da lafiya kason shi Hajiya da Yan uwanshi ne zasu more tunda mutuwa zai yi a wurin aikinshi.
"Mutuwar Abdul Majid Mamman Ba'are baya hannuna, amma nasan dukiyarshi zata iya dawowa hannunmu idan har aka bi a sannu. Kana jiye mana abin da zai kai Sa'adatu lahira."
"Ba iya shi ba, akwai labarin da nake son nasani amma yaki gaya min. Ina son idan na samu labarin zan gaya miki."
"Wane labari ne haka?"
"Ya ce min a sanadin haka aka kai, Majid gidan kangararun Yara, domin fitar da Hajiya tayi. A wannan ranar shi ya saka Majid ya fara sace-sace har aka kai shi gidan horar. Idan ya tuna abin yana jin tsanar Hajiya."
"Kai haka ya ce? Lallai nayi babban kamu. Tow kada ka sake ya fahimci cewa kana son jin lallai ya baka labarin, zan cigaba da aikina anan da kanshi zai baka labarin."
"Shi kenan, amma ni gaskiya na gaji da wannan harkar." Shiru tayi ta ce mishi. "Na dan lokaci ne, ka saka idanu yadda zan tarwatsa Sa'adatu."
"Yawwa Hajajju sabuwar Chairwoman ba BA'ARE GOLDEN EMPIRES!"
Murmushi ta saki ya sauke wayar yana faɗin. "Hajiya Tani, kifi na ganinki mai jar koma. Ina harinki kina harin Hajiya Sa'adatu."
---
Hajiya Tani.
Jikinta ne ya bata ana tsaye a falonta, ta kashe wayar ta fito, ganin Hajiya Fauziya Mamman Ba'are yasa ta sha jinin jikinta kamar babu abinda ya faru ta kakaro murmushi ta ce mata. "Kina son wani abu ne?" Girgiza kai tayi ta ce mata. "Naji kin ambaci sunan Sa'adatu ne akwai abinda ya faru ne?" Wani sirrintaciyar murmushi tayi tana faɗin. "Hajiya Fauziya taya zan yarda na gaya miki gaskiya, bayan kema idan kin samu yakata zaki yi." "Haba wani yakarki? Kawai gaya min zan taimaka miki da yad'a shi." " Ba yad'awa ba ne, so nake ki saka ya Haladu yabawa Abdul Majid auren Afiyyah."
"Kina ganin haka mafita ne?" Girgza kai Tani tayi tana faɗin. "Haka shine zai bamu damar fitar da abinda kike son faɗa." "Akwai labari kenan!" Murmushi Tani tayi tana faɗin. "Mai girgixawa."
Daga haka suka fita, kamar yadda suke son sanin me ya janyowa Majid ya samu wannan matsalar duk yadda aka yi Hajiya tana da wani dark secret da take boyewa idan haka ne kuwa tow tabbas Hajiya ta kusan mutuwa.
---- Kure volume na radio Nana tayi tana niman gidan rediyon Faransa, tana ƙara ware idanun. Bubbuga radio tayi tana tsaki. "Mtsew, ƙarfen nasara babu tabbas yanzu wannan raidiyon wai batiri yake nima." "Assalamu alaikum!" "Waye nan?" Ta amsa cikin masifa tana mikewa. "Nana Fauziya ce!" "Kin kashe maganar bashin da Mulaika taci?" Wani shiru Hajiya Fauziya tayi kafin ta ce. "Ayya Nana daga zuwa gaishe ki sai ki gwale ni." "Ahtow ai gaskiya na faɗa, ko kunyar Harirah baki ji, tana tattalin dukiyar Yaranta babu ruwanta iya shi ne a gabanta, ke baki da aiki sai bin malamai da munafunci, wallahi ina rabaki da wutar jahannama." Ta fada mata tana wani zumburo baki. "Wai Hajiya na hango wani abu da ba kowa ya hango ba, shine nace duk da babu wanda yake kallona da idon rahama." Tayi shiru gashi Allah ya jarabci Nana da bala'in son jin gulma don haka tayi kwalkwal da idanunta. "Ina jinki bana son munafurci zaki fara magana kiyi shiru."
"Hmmmm Nana ai ban san yadda zaki ɗauki maganar ba, shi yasa na kasa faɗa miki." Inji Hajiya Fauziya..
Wani galla mata harara Nana tayi ta ce mata. "Kin san na tsani a zo bani labari a tsaya ana kame-kame uwar me idanunki ya hango wanda nawa idanun bai hango ba?"
"Hmmm Hajiya naga Maisarah tana wurin dangin Mamanta, kuma kin ga zata fi dacewa da Alhaji shine nace mai zai hana a hada Maisarah da shi." Ware manyan idanunta Nana tayi kafin ta ce mata. "Amma Fauziya Allah ya miki albarka, ina na tab'a tunanin hakan."
"Amma Hajiya wani hanzari ba gudu ba, ko za a hada shi da Afiyyah ne?" B'ata rai Nana tayi tana faɗin. "wannan yar banza da shegen kugu kamar an zargawa biri igiya babu abinda zai hadata da bawan Allah tunda ai shi mutumin kirki ne, yarinyar nan ranar wasu irin kaya ta saka tana tafiya ina ganin jikinta Allah na tuba ita da Sajjidu kullum suna makale da juna kamar kadangaru ita dai wancan ko zuwa tayi kowa yasan iyayen Uwarta mutanen kirki ne, Turai kuma babu wanda bai san shaidaniya ba ce."
Hadiye yawu Hajiya Fauziya tayi domin kawo bambancin Maisarah da Afiyyah a fili take. "Amma Nana don Allah kada kice nice na ce ya auri Maisarah, don kinsan Alhaji Karami zai kullace ni." Galla mata harara tayi tana faɗin. "Babu wanda ya isa Miki haka domin sai naci uwatai, ke da kika hada alkhairi sai na watsa miki kasa a idanun. Tashi ki je amma ki daina munafurci domin ba abun arziki ba ne "
"Shi kenan Hajiya naji sannan Hajiya kin ji labarin Aryan shine sabon shugaban Kamfani ba Abdul Majid ba!" Sake Radio din hannunta tayi ya fadi kasa ta ce. "Ke dai had'a husuma ya zame miki jini ko? Ina zaki aikata abin arziki amma munafurci ya saka ki sabule ladar ki. Taya Majid zai bawa wancan kodadden bawan shugabancin ai sai dai Sa'adatu ta cigaba da rikewa har ya gama yawon sojancinshi."
"Hmmmm! Wallahi kuwa Nana ki tambayi Sa'adatun idan karya na miki ranar Monday zasu tabbatar da shi, sannan ya rabawa yan dakinsu matsayi ko kara bai raba mana ba."
"Lallai wato shine suke niman kashe shi, idan bai basu shugabancin kamfanin ba, kuma babu babban munafukar kamar Sa'adatu domin ta munafurce ni. Da ta gaya min da na saka Haladu ko Kamilu dayansu ya rike kamfanin abin gado ne da ba za abawa wani ya rike ba. Yau idan ban ci mutuncin Sa'adatu ba, shegiya Uwata ta haifan." Ta tashi don masifa a juye ta saka hijab dinta, ta nufi hanyar waje, Hajiya Fauziya tana dariya a ranta. Har kofar Hajiya ta rakota, sannan tayi tafiyarta ita daya ta jefi tsuntsu biyu da dutse daya, ta juya lamarin maganar auren Afiyyah da Majid, an maida maganar kan Maisarah da Majid, yanzu zata sake hada wani rigimar tsakanin Nana da Afiyyah, sannan ta nuna babu ruwanta a zancen kamar bata sani ba.
A fusace Nana tana bala'i ta shiga falon Hajiya, suna falon har da Majid kuma fa tun farko an zo an gaya mata ta ce babu ruwan kowa kamfanin sune amma yanzu da jaraba take cinta tazo sauke jaraba. Kallo daya yayi mata, ta koma daya daga cikin sofar falon ta zauna. " Sai wiki-wiki take da idanuws. "Barka da yammaci Nana " " yawwa Sa'adatu!" Ta fada a dakile. "Nana ya kike?" Inji Aryan yana cika bakinshi da kankana. "Kundun Ubanka mara mutunci, Abdul Majid kaga yadda yake min gaisuwar yan tasha."
"Haushin kaza huce kan dami, Nana kowa yasan kin shigo da jaraba ne, don haka ba zaki fara a kaina ba."
"Alhaji kai kake daure mishi gindi yake min rashin kunya, don kawai na damu da ku? Fisabillahi Alhaji kaf gidan nan a rasa waye zaka bawa shugabancin kamfani sai wannan me kama da zabiya?" Sai kuma ta kama share hawaye tana faɗin. "Yanzu Sa'adatu da saninki Alhaji ya dauki jagorancin nan ya bawa Aryan wannan mara kunyar yaron ni dai ban amince ba."
Ta fada tana yatsina fuska. Mika mata bowl din fruit din da Hajiya da kanta ta haɗawa Majid yayi. "Sha." A hankali ta dauka tana sha, ta ce mishi. "Duk gidan nan babu wanda ya kaika mutuncin da Alkhairi."
"Sha kawai Hajiya!" Haka ta sha, bata gama sha ba Aryan ya tawo da gasashen namar kaza ya ajiye a gaban Majid. Kallonshi tayi tana son ta hango iyakar muguntarshi.
"Nana me kike son gani a fuskar." Hadiye yawu tayi tana faɗin. "Lamari na duniya akan abin duniya sai a iya kashe mutum, kai Alhaji ina fatan ba barazana yayi maka ba ko?" Ta fada tana kallon Majid din, "to naga ga Yan uwan Ubanka, ka tsallake su ka bawa mara kunya kamfani."
Ganin Majid yana cin namar shi babu abinda ya ce mata, yasa ta ci-gaba da cewa. "Shi namar ka tabbatar da cewa babu guba a cikinshi?" Cak ya tsaya da taunar namar, yana me kallon Aryan ɗin, "Kika ce me?"
"Hmm nace ka tabbatar babu guba."
"Ai tun a ya'yan itacen da kika sha nake tsammanin ya na zuba gubar yadda kike tunani." Harararshi tayi tana faɗin. "Gubar zaka zuba ka fada min? Sa'adatu ki gayawa wannan futsararen dan naki ya daina shiga harkata da Alhaji "
"Tunda tare kika ganmu haka zaki bar mu, sannan da kike cewa a hana ni babu abinda zaisa a hana ni sai kiyi kuma."
Ya fada a fusace zai bar falon, "dawo ka zauna." Inji Majid ita kan Hajiya babu ruwanta. "Tow fisabilillahi zata zo tana irin wannan maganar, idan wani bai yarda ba wani ai zai yarda." "Koma ka zauna "
Zama yayi yana huci kamar zai fashe da kuka,"Nana asalin abinda ya kawo ki, akan kamfanin da na bawa Aryan ne ko? Dama can Aryan shine Magajin Mamman Ba'are,, Ni aikina yana da muhimmanci, idan nace xan riƙe kamfanin ba za a samu abin da ake so ba, Nana ni soja ne kawai abinda na sani na koma bakin iyakar kasa ko ruwa na kare al'umma, domin wannan aka haife ni." "Tow me yasa ba zaka bawa yan uwan Babanka ba."
"Kowa ya nemo na shi dukiyar Mamman Ba'are na Yaran Mamman ba'are ne, don haka kada na kuma jin haka idan ba haka ba, sai na saka an bincika min ke da laifin yunkurin hada husuma." Ya ciro bindigarshi ya ajiye a gabanta..
#Dambujeeeeeee🥳
[2/26, 7:37 PM] Cutie cutie pie: *BAƘIN HAURE....🐾🐾*