Sashe 82
Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A hankali muka wuce wannan hall din, wani babban falo muka shiga, su kuma asalin aikinsu akan tattalin arzikin kamfanin ne, wata kujera ya nuna min. " Anan zaki zauna." "Na gode sosai!" "Idan kina bukatar wani abu, ki min magana." Haka ya juya ya fita, sannan wani abu da na fahimta ana mugun ganin girmansa,ko ina muka wuce girmama shi ake. "Kass!" Naji karar chew gum. Juyawa nayi naga ashe dan daudu ne. Yadda na kalle shi sau daya na cigaba da aikina. "Ya da kallona ko idon ya miki yawa ne, kwakulo daya mu raba, ana bikin dan zakara biri abokin ango su mage ne yan mata." Ya faɗa yana murguda baki, *mamaki baya karewa* Na fada a raina domin na fahimci wai habaici yake min. Ban kuma kallon shi ba, don na gano bai da mutunci ko kaɗan. Karfe biyu naga ana ta fita, ashe wurin cin abinci suka nufa, ni ban sani ba na zauna a office din, sai ga mutumin da ya kawo ni office din. "Baki fito ba, da fatan lafiya dai?" Murmushi nayi ina faɗin. "Lafiya lau. Ina son nayi sallah kafin naci abinci ne." "Ko na saka a kawo miki ne?" "A'a yallabai zan je da kaina." "Tow shi kenan, muje na kai ki masallaci." "Tow!" Na rufe computer din, na mike tare da bin bayanshi. Sai kallonmu ake, ni dai haka kawai Allah ya haɗa jini na da nashi, nakuma ji ina son shi a matsayin dan uwana. Har can masallacin ya raka ni, shima ya wuce bangaren maza. Bayan na idar shima ya fito, amsar jakar bayana yayi ya yana faɗin. "Kawo na rike miki kanwata." "Tow " na mika mishi, wurin abinci muka wuce, wasu naci suka fito sallah, a lokacin an watse, zama nayi, na yi shiru, masu tambayar me za'a zuba maka suka zo, na duba abinda xan iya ci,na faɗa shi kuwa ganye ne sai tea da short cake. "Don Allah ko zaka taimaka min da wayarka." Mika min yayi na amsa, "Ba'are shine password din!" Ina sakawa ya nuna min ba daidai ba, tura mishi nayi na ce mishi. "Yaki budewa." Amsa yayi yana faɗin. "Kina tsoron kada ki shiga wani wuri ne?" Bude min yayi ya mika min, ganin xan bawa kaina wahala na karanto mishi number, amsa yayi ya saka min sannan ya kira yana me mika min. "Assalamu alaikum! Baraka ina Mamanku?" "Laaaa Tente kece?" Murmushi nayi nace mata, "Eh!" "Mama ga tente." Mikawa Maman wayar tayi muka gaisa, sannan ta ce min."kin isa lafiya dai ko? Ya aikin da inda kika je?" "Alhamdulillahi, wurin zama aka bani yanzu zan tafi domin nags yanayin wurin, idan yaso wani sati sai nazo na dauke ta." "Allah sarki, muna kewarki." "Nima haka Ina Amirah sugrah?" "Gata nan!" "My heart kina lafiya!" Ba hmm balle humm, haka take ba baki sai wayon azaba, haka na gama hira da ita, na ma manta wayar aro ce, bai ce min kome ba sai da na gama don kaina na bashi wayar a kunya ce. "Kayi hakuri na cinye maka kati ko?" "Idan baki gama.wayar ba, ki cigaba kanwata ce ke ai." "Na gode sosai na gama" "Tow maza ki ci abinci."cikin farin cikin waya da Amirah na ce na koshi ma, mikewa yayi ya amsa min cake da donuts, meatpie da samosa. Sai kayan sanyi a cikin jakar kamfanin. "Muje na saka a kai ki estate dinku, ki gyara gidan." "Na gode sai dawainiyya kake dani.". "Ni yayanki ne babu bukatar min godiya " Haka muka fito ya kai ni na dauki kome na, sannan da zamu tafi ya ce min. "Kina da waya kuwa?" "Eh ina da shi amma ta b'aci ne." "Account fa?" "Ina da shi, amma ban rike number ba." "Allah ya kyauta, ki nemo saboda kudin da kamfani zata na biyanki." "Tow;" na fada muka tafi gidan da mutumin. .... "Sannu uban yan kwashe- kwashe." "Yawwa uban yan mugun hali ba banza Nana take cin mutuncinka ba.". "Amma me yasa ka wani biye mata, sai gulmar ku ake har a whatsp." Dariya yayi yana zama tare da faɗin. "kawai naji ina son na kula da ita ne, kamar yadda nake kula Anisah da Jamilah da Zaytoonah. Yarinyar tana da nutsuwa kaga yadda take nan, wallahi ko waya babu a hannunta." "Waye ya damu?" Inji Aryan, "Ni na damu, domin daga ganin tana da Yarta da ba sa tare." "Kana nufin yarinyar nan tana da Y'a?" "Tow meye a ciki?" "Babu amma naga." "Ka duba da kyau ba yarinyar ba ce fa, ka kara kallonta kawai jikin ne dai irin model." "Hmm ba sa'ide har ka gano haka." "Don ma a kanwa na dauke ta, da a ce a macen aure na dauke ta, kaf -kaf zan yi da ita domin kamfanin nan cike yake da tuzurgwauro." "Amma dai ba da Hammayo kake ba?" "Kai dai ka sani, wallahi don ban faɗa ba." "Ka fadi gaskiya ma idan Hammayo ya zo." "Ko Gatari ba" Ya faɗa yana dariya, a haka suka wuce office dinsu. ..... Gidan da aka kai ni apartment ne babban, sannan kowane da daki biyu da banɗaki da kitchen, sai yar baranda a bayan apartment din, domin gidan sama ne mai dauke da hawa dari da wani abu. Akwai gado da kome a cikin gidan...... 300₦ 0016341139 unity bank zahra'u yahaya Ali Katin MTN 400 or +234 703 513 3148 #Mai_Dambu ce [5/29, 07:47] Hlm: BHB242 A hankali nayi ta bin gidan da kallo, yo wannan idan mutum bai wasa ba sai ya manta da waye shi ko me ya kawo shi, haka yasa na gyara inda xan zauna daki daya da falon. Ina ga ko don suna yawan saukar da baki ne yasa oho,amma gidan kome ba laifi. Ina gama gyara cikin dakin aka kwankwasa min kofa. Fitowa nayi daidai ana kiran sallar la'asar, bude kofar nayi ina kallon wasu Mutane su uku dauke da kayan abinci. "Kanwata ni na kawo miki don nasan dole zaki bukaci abinci." Wani lokaci haka kawai sai Allah ya haɗa ka da masu taimakonka. "Sannunku!" Na fada ina basu hanya, haka suka shigo min da kayan Abincin, duk wani abinda zan buƙata. "Ki saki jikinki, kamar kina gida, nan ma kamar gida ne " a karo na biyu da aka mu'amalance ni a matsayina na yar adam. "Allah ya biya maka bukatarka na alkhairi." "Amin kanwata." Mutanen na gama shigar da kayan suka juya tare da barin dakin, "tow zan tafi, bakya bukatar da wani abu ne?" Girgixa mishi kai nayi, ina faɗin."Alhamdulillahi kome ya yi Allah ya saka da alkhairi." "Tow sai an jima." Yana fita na rufe kofar dakina, na yi alola da sallah. Ina idarwa na kwanta ina jin yunwa tashi nayi, naga har da takeaway sai robar fura da nono. A hankali na fara sha ina godiya ga Allah da ya haɗa ni da mutumin kirki,haka na sha na koshi naci jollop din shinkafar ciki wanda yaji hanta da nama, daya takeaway din rabin kaza. Sai ga hawaye, ai dole ranar Asabar na tafi na tawo da Amirah. Ba zan iya cin wannan abin arzikin ni daya ba, amma kuma ya xanyi da ita? Dole na duba koda daycare ne na sakata. Da dare ina kwance aka buga min kofa, daga ciki na ce "waye ?" "In ji Yallabai Amaan ya ce a kawo miki abinci." Bude kofar nayi na amshi abincin, na koma na rufe. Zama nayi tuwon shinkafa miyar kuka wanda tunda nake ban tab'a ganin yadda aka raya miya haka ba, bayan kamshin daddawa. Nama aka dake ta a miyar. Sai gudar tsokar nama da manshanun nguru, wanda kana ci kana jin kamshinsa. Yawuna ne ya tsinke, na zauna na saka malmalan tuwo biyu, na fara ci man shanu nan har bayan hannuna. Ina ci ina santi. "Allah ka sakawa Ya Amaan da alkhairi." Wato sai gani na tashi malmalan nan biyu, na kuma dinfari na uku. Daukar daya daga cikin goran da aka saka a cikin basket din nayi na bude tsumi ne, da ya sha kayan kamshin wanda shuwa suke ce mishi ardif, wasu suke ce mishi pito. Yaji kayan kamshi, kamar haka domin kana sha kana jin kamshinsu. 1. Pineapple 2. Cloves 3. Mint leaf 4. Ginger 5. Tamarinds flavor 6. Tamarinds 7. Cinnamon stick ( optional), tass na shanye har da neman kari, ban yi kasa a gwiwa ba na shanye daya goran wanda shima zobo ne, kai jama'a wasu matan Allah ya halicce su ne domin sarrafa maiwa zuwa dawa. Ban daki na shiga nayi brush na dawo na saka littafan da yake gabana, ina yi ina hamma man shanu ya fara ratsa ni, ban yi aune ba sai barci, a falon na kwana. Washi gari. Kitchen Amaan ya nufa bayan ya dawo daga masallaci, "Hajiya idan zaki hada abin karyawa a hada har da na bakuwa kamar na jiya." "Yaushe ka zama Uban Teresa?" Juyawa yayi yana kallon Majid da yayi maganar, "Ba haka ba ne, kawai ina jin yarinya ne a raina." "Idan kana sonta sai ayi wani abu?" "A'a Hajiya ba soyayya ba ce, fiyye da soyayya nake mata, bana jinta don na aure ta. Akwai wani abu a tattare da ita idan ka saka idanu akanta, zaka hango maraici da kaɗaici. Sannan rayuwata nayi kuskure dayawa ina jin kamar idan na kyautatta mata Allah zai kankare min wasu daga cikin zunubai na. Rayuwar duniyar ma guda nawa ce?" Wannan kalmar da ya rufe maganar shi da ita yasa jikin Hajiya mutuwa. "Wani irin kalamai ne haka Aliyu?" "Hajiya kina tsoron kada na mutu ne?" "Ko ba mutuwa ba, da farar safe zaka dakushewa Alhajin Allah sa'arshi. Kaga Amaan ka fita idanuna na rufe, ban da zancen banza dan kaniyarka yaushe ka isa mutuwar? Ko ni nan da saura na balle kai, mara mutunci na sake jin ka ambaci mutuwa, sai na zabga maka mari kada ka ganka kato kayi tsammanin zan kyale ka, wallahi sai na ci damara muyi dambe." Inji Nana ta mike tana cin dammara, "kuma sai kiyi dambe da shi?" Inji Aryan da ya shigo, domin Majid ya bar musu falon. "Dan banza me mugun nufi, ban da rashin sanin ciwon kai ana zaune kalau,