← Book details Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 138

Sashe 81

Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

Haka muka cigaba da karatu har aka yi jarabawa, daga wannan hutun ba zamu kara dawowa ba, sai bayan wata shida idan muka dawo zamu dauki wata tara kafin mu gama makarantar gaba daya..

Algers
A hankali ya fito rike da sandarshi, yana takawa a hankali sanye yake da kaya irin na sarakai. Kyakkyawar balaraben Algeria.
"Sultan" murmushi yayi ya ce mishi. "Zuwa yanzu ta daina kuka don kada a cutar da ita ko?"
"Sai dai kewa da kaɗaici yasa har yau taki yarda da kowa."
"Na kusan bayyana a gareta, na kusan na mallaki abinda nake tunanin nawa ne."

"Majid ya kamata ka ajiye maganar lalurar nan ka fuskanci rayuwarka. Kayi auren ko za a dace."
Murmushi yayi yana rike da Mug din Black tea,yana kurba.
"Na kusan isa ga wacce take manne da duniyata, rayuwata da farincikina yana tare da na ta, na kusan isa gare ta, a da can baya ina jin kamar tana kara nisanta da ni, amma, a yanzu ina jin kamar duk bugun dakika kara kusantowa take gare ni......................
Tofah ! Da wa za'a yi ne? Dan sarki ko mai kudin ba'are😘 Kodayake jarumi Sajjid ma yana cikin yan gasar 💃💃💃💃💃💃🤣🤣
Anan book one ya kare sai Allah ya had'a mu a book 2 domin jin yadda za a kayya... Taku har kullum.
RamlatManga
Mai_Dambu.
300₦
0016341139 unity bank zahra'u yahaya Ali
Katin MTN 400
#Mai_Dambu ce

BOOK TWO

[5/29, 07:47] Hlm: BHB241
"Kana nufin matarka tana kusa kenan?" Murmushi yayi yana faɗin,a da can hasashe nake amma a yanzu na tabbatar da tana kusa dani, tana dab da ni sama da yadda nake jin tazarar sama da kasa." Murmushi ne me kayatarwa ya kwace a fuskar shi. "Amma wacece haka me sa'a?" Lumshe idanunshi yayi yana faɗin. "Kawai Imagining ne, amma babu wacce zata auri yar uwarta mace." Yana fadar haka ya mike kamar bashi ya gama murmushi ba, domin baki daya, sai ya tsume musamman da aka yi knocking kofar office din, Afiyyah ce sanye da wani irin suit riga da wando pink, bakiɗaya surarta a bayyane yaƙe.
"Hammani ga report din da ka sani na maka."ta faɗa tana ajiyewa akan table din gabanshi. Dauke kai yayi yana wani haɗe fuska, domin mutum yana iya hango tsakankanin kirjinta, ajiyewa tayi cikin salo da jan hankali, Mahdi Abubakar Abzin yana lura da shi, murmushi yayi yana bin ta da wutsiyar idanu, har ta fita ya ce. "Ba'are yarinyar nan ta haɗu fa." "Ka je gare ta mana." Ya faɗa yana bude files din, kwankwasa kofar aka yi, "shigo!" Mahdi ya faɗa. A hankali ya zuro kafarshi da yake sanye da hill sheo na gucci, hannun shi sakale da jaka shima na gucci, fuskar shi ta sha fenti, gashin dokin nan har gadon baya.
"Assalamu alaikum!" Ya faɗa yana kareraya kamar maciji. Kunshe dariya Mahdi yayi yana kallon ikon Allah. "Sannu sir ga report din da kace na kawo maka, kayi hakuri bana nan ne wancan satin." Ya faɗa yana ajiyewa. "Saurayi ya kake?" Washe baki Mahdi yayi ya ce . "Lafiya lau ya sunanka?" Tuni ya haɗe rai, ya ce mishi. "Sunana Sahiba." Gyaran murya Majid yayi da sauri ya fita kamar kugunshi zata karye,. Wato asalin ko Sahiba duk wanda ya san James brown wannan shahararren dan daudun nan. Gashi kamar one haka yaƙe. Amma don jaraba ya daurawa kanshi masifar daudanci.
"Ba'are a ina ka samu 2sim?" Ya tambaye shi cikin dariya da tsokana. Banza Majid yayi mishi don baya kaunar abin da zai saka shi maganar dan daudun nan, "Gaye ko kana cikin ne da Sahiba?" "Idan na zage ka ba zaka ji haushi ba?" Dariya Mahdi ya saka mishi, irin na niman faɗa, "oh kodai shine bugun zuciyarka?" "Idan ban ci ubanka ba Allah ya min albarka "
"Zan gayawa Hajiya, kayi budurwa saurayi budurwa.". "na rantse da Allah sai na ci ubanka." "Oho dai sai na gaya mata."
Haka Mahdi yayita zolayar shi yana dariya.

Ranar talata na shigo garin Niamey, a gajiye likis domin ban san kan garin ba, kuma ba karya Niamey babban alkarya ce, sannan naji daɗin yadda Maman Barakatu suka bani shawarar na fara zuwa naga yanayin wurin kafin na zo da Amirah ba don haka ba,da na shiga uku, don koda na isa sai da nayi ta yawo, kafin na isa babban office dinsu, ina isa aka ce sun tashi haka yasa dole na nemi masauki, na kwana, washegari da safe na isa kamfanin.
Sanye nake da doguwar Jallabiya, sai mayafin da na rufe jikina ruf, ta cikin mayafin na saka hula me kyau da ta dauke sumar kai na, ina tsaye akai ta budewa ma'aikatan kamfanin get suna shigowa ni kaina nayi mamakin uban sammakon da nayi, amma kuma ai ban yi a banza ba, tunda ina zaune wurin karfe tara aka kira ni. A bakin kofar shiga naga an rubuta CEO Aryan Mamman Ba'are.
Buga kofar nayi, "shigo!" Aka ce min. A hankali na tura kofar bakina yana me dauke da sallama. "Wa'alaikimun Salam." Ya amsa min, cikin sakin fuska. Kujera ya nuna min, na zauna. "Ina kwana yallabai?" "Lafiya!" Ya ce min hankalinshi yana kan aikin gabansa. "Daga Jami'ar marad'i ko?" "Eh" ya d'ago kai yana me kallona, yadda nake takure. "Tow gashi nan, kije office din AG na maaikantan zai had'aki da Admin, ban sani ba ko zaki bukaci ganin Store amma ga dai takardu nan ki mika musu." "Na gode sosai." Na mika mishi nawa takardun da na kawo, na mike zan fita ya ce min. "Fadime Abubakar?" "A'a Fatima Abubakar dai." Shiru yayi domin dai abin da yake gani a gaban computer din shi daban, wanda ta faɗa daban. "Maybe an samu matsala ne daga makarantarku nake tunani."
"Hmm!" Haka na fito na nufi waje,. ina duba takardun, a ina aka samu matsala. A hankali nake dubawa, ji nayi an wani bangaje ni sai da takardun suka watse a ƙasa. Shima waya yake wayar ta fadi can, "Kayi hakuri don Allah, kayi hakuri don Allah." Haka nayi ta nanatawa, ban ma san waye ba, amma kuma kaina kamar zai tab'a kasa, haka na dauko wayar na mika mishi, na kwashe takardun na mike, yana tsaye har zuwa lokacin bai tafi ba, a hankali na juya kaina a sunkuye na ce mishi. "Don Allah kayi hakuri, ni bakuwa ce a cikin maaikantan nan."
Juyawa yayi ya tafi bai jira na gama mishi bayani ba, wucewa nayi na nufi inda aka tura ni, amma na jima ina yawo kafin na hadu da wani mutumin ya kai ni office din Admin. "Assalamu alaikum!" Bai ji ni ba ne, ko wani abu yake ban sani ba, sake shiga cikin office din nayi can ciki naji ana magana a hankali. "Hajiya na gaya miki, babu wani motsi sai dai idan da wani abu zan miki magana, amma a yanzu babu motsin da Yara ukun suka yi." Ja da baya nayi kamar xan fita na ji ya ce. "Kada ki manta wutan da kika umarce ni na saka, har yau mayen sojan nan yana bincike a kai, don ma nayi ƙoƙarin kauda hankalinshi a kai."
Shiru yayi ya ce mata. "Shi kenan kawai ki saka Aljan yayi kome mana, ai nasan zai so yin haka." Ya faɗa yana kara kasa da murya, tow meye nawa na sauraron abin da ake, a hankali na fito na tsaya a bakin kofar. Ina tsaye a wurin ban shiga ba, kunnena basu daina amsa kuwa da abin da ya faɗa na karshe ba, sai na tsinci tsoro a cikin kalaman shi, kamar zan juya na koma sai na fasa, ina tsaye haka mutane suka yi ta wucewa, sai na je kamar zan buga kofar sai na fasa, kada yayi tsammanin na ji yo sirrinshi, haka yasa na kasa kome, na kashe minti ashirin a tsaye, "Baki shiga ba ne?" Naji Muryar mutumin da ya turo ni, jikina ne ya dauki rawa kamar wacce ta aikata wani, "Lafiya?" Ya tambaye ni, "a'a babu kome, kawai zan tafi ne nayi sallama ba a amsa ba." Na fada zan juya, "dawo mu shiga i think yana ciki." Ya wuce gaba bai gama jin me zance ba, ya shiga office din yana d'aga murya. "Hamza!" Ya kwalla mishi kira, "Na'am yallabai Aryan" ya fito yana sharce zufan da yake ta karyo mishi.
"Ya na turo bakuwa a bata, key din estate tayi sallama baka amsa ba?"
"Kayi hakuri waya nake, daga gida gyatumata ba lafiya, ban ji ba kuma." Ya juya yana kallona, cikin wani irin murdewar ciki na ce mishi da sauri. "Nayi sallama da buga kofa baka amsa ba, amma ban shigo ba."
Wani zuba min idanu yayi, sai da CEO ya ce mishi. "Ka amshi takardunta daga nan ka kaita Office din Amaan, za tasaka hannu." Ya faɗa yana me fita, ji nayi kamar ya barni cikin mutuwa, "kin kai minti nawa a wajen?"
"Ban wuce minti biyar ba." Sauke ajiyar zuciya yayi cikin fara'a ya ce min. "Kin san mutumin da yake da abubuwa dayawa dole ya zama me yawan sabgogi."
"Eh haka ne!" Na fada, ina kallon kasa domin wani irin tsoro yake bani, haka ya gama ya mika min key nasa hannu zan amsa ya mai da hannunshi. "Kina da kyau." Ji nayi kamar zan mutu, mika min key din yayi yana faɗin. "Muje ko." Haka ya sako ni a gaba, har Office din da aka ce ya kawo ni, ina shiga na samu office din da mutane,
"Hamza bakuwa muka yi?" Ya tambaye shi, cikin kulawa. "Eh yallabai yanzu mai gida Aryan ya turo min ita." Mikewa yayi cikin kulawa da fara'a kamar wanda ya tab'a gani na, ya wuce da ni cikin office din shi, ya ce min. "Zauna ina zuwa." Ya ajiye min ruwa da lemo, ya fito ya gama.musu bayani, sannan ya shigo office din. Wuce ni yayi wurin zaman shi, yana kallon File dina da yake laptop din shi.
"Fatimah Abubakar?" Ya kira sunana. "Na'am!" Na mike, girgixa kai yayi ya ce. "A'a kawai na kira sunan ne, daga marad'i ko?"
"Eh!"
"Anani fulfube?"
"Na'am" na ce mishi.
Dariya yayi yana faɗin. "Kin yi magana da Fulani ne, kuma ga shi abin da aka rubuta a personal information ɗinki kenan." Daga haka ya gama cike-ciken shi ya ce min. " Zamu yi aiki dake a bangaren tattalin arzikin kamfanin nan, idan kina da wani abu na cigaba kiyi kokarin fito min da shi mu gina kamfanin nan."
"In sha Allah."
Daga haka na mike ya ce min. "Ki dauki abin shan ki mana" "A'a na gode." Dauka yayi ya saka min a cikin wani leda, ya rako ni har waje, ƙara wayarshi tayi ya ce. "Yawwa Abdul na turo maka sako, sannan ga ɗaliban nan."
"Allah ya yaye maka, shi kenan." Ya faɗa yana kashe wayar, wani babban hall ya tura ni, inda da alama anan ake aikin duk wani data information na kamfanin, sai ɓangaren masu zanen zinari, abubuwan dai gasu nan.
Chapter 81 · 0% Book details