Sashe 59
Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read
*028*
A rikicewa Amaan ya ce . "Sajjid me nayi maka da zafi haka? Nace na daina sai ka kyale ni dole ne sai nayi yadda kake so?" Dariya Sajjid yayi yana faɗin. "Wai tow lokacin da ka saka muka fara baka san cewa haka zai faru bane?"
Zufa ne ya shiga karyo mishi, jikinshin na rawa ya mike tsaye. Duk ya rikice. "Sajjid don Allah ka saurare ni!" "Kit ya kashe wayarshi." Kiran wayar sajjid din yakara yi, amma yaki dauka karshe ma kashe wayar yayi, hannu Amaan yadors a kai kamar ya fasa ihu, ya rasa yadda zai yi da ranshi. Turo kofar da aka yi yasa shi d'ago kai da sauri yana kallon Aryan da yazo tambayarshi. Amma da yake yana cikin tashin hankali, bai iya sauraran Aryan din ba, ya bangaje shi ya fita yana kallon agogon hannun shi.
Sake kiran layin Sajjid yayi ya ce mishi. "Don Allah ka rufa min asiri gani nan zuwa."
"Ba zan rufa maka asiri ba, kawai ka san yadda zaka yi idan ba haka ba. Hmmm!" Sajjid ya faɗa yana kashe wayar. Kamar zai saki fitsari a wandon shi haka yake ji, don dole ya ja motar shi da gudu, Aryan yana kallonshi ta office. "Me ya same shi?" Ya tambayi kanshi yana me kare kankance idanunshi. Kafin ya sauke ajiyar zuciya.
------
Har inda Sajjid yake boye kanshi ya isa domin ya sani, amma yaki faɗa kuma yasan ana niman sajjid ɗin. Lokacin da ya shiga cikin gidan, Sajjid yana tare da wasu mutane. Amma koda Amaan din ya isa zubewa yayi akan gwiwarshi, a gaban Sajjid din. Dariya suka saka tare da kallon yadda yake durkushe a gabansu. "Don Allah ka rufa min asiri, ka gaya min duk abinda kake so."
Kallonshi Sajjid yayi yana juya kofin wine na hannun shi. "Bana bukatar kome, ya cikin naka?" Kamar ya fashe da kuka ya ce mishi. "Da sauki.", "Ka wuce zuwa asibiti duk abinda aka rubuta ka gaya min."
Kasa yayi da kai yana kallon kasa, kafin ya ce. "Idan na tafi asibiti za a iya ganina, sannan mutane zasu ta yawo damu. Ina son fita Najeriya ne naga likita a can." "Shi kenan jeka!" Girgza kai yayi yana faɗin. "Ba zan iya zuwa ba, sai da yardarka da izininka zan tafi."
Tashi Sajjid yayi ya nufi inda Amaan yake zaune, shima ya zauna yana kurbar wine din shi ya ce masa. "Idan haka ne kafin ka tafi asibiti bakidayanmu sai mun more ka." A razane Amaan ya zame zaune daga durkushen da yake, ya zubawa Sajjid idanu. "Wallahi idan kuka min zan sha wahala, don Allah ka rufa min asiri." Tab'e baki Sajjid yayi yana faɗin. "Idan kana tsammanin zaka sha ne, tashi ka je amma ka tanadi amsar da zaka bawa danginka da press!" Ya fada yana d'aga kafadarshi. Wani abu ne ya tsayawa Amaan a rai, ya kasa cewa Uffan domin Sajjid ya kashe shi. "Na gaya maka bani da lafiya, da ace ina da lafiya da zan maka yadda kake so, amma yanzu bani da lafiya."
"Tashi ka tafi dan uwarka, maza fita min a gida dan shegiya!" Kasa motsawa yayi yana zaune a wurin, Sajjid ya cigaba da zagin shi, karshe da yaji haushi daukar kwalba yayi ya wurgawa Amaan a goshinsa sai da ya fasa mishi goshi, duk da haka Amaan bai motsa ba, yana durkushe a wurin, "ka fita min a gida kafin na kashe dan iska irinka." A hankali Amaan ya mike yana dafe da goshinsa ya fita, yana shiga motarshi ya saka tissues yana goge jinin. Haka ya gama ya fita sai da ya bar unguwar ya kifa kanshi a kan sitiyerin motar, ya saki wata irin ajiyar zuciya. Bai san makomarshi ba, matukar Sajjid ya saki videon da yake kokarin sakewa bai san yadda zai fuskanci Hajiya ba, ciwon cikin ne ya murde shi, taka motar yayi da gudun bala'i.
Bayan fitar shi, daya daga cikin mutanen Sajjid ya ce mishi. "Me yasa ka kyale shi." Murmushi yayi yana me busa sigari hayaki na tashi sama. "Ina da shiri ne, ka tab'a ganin yadda aka jefi tsuntsu uku da dutse daya?" Girgiza kai suka yi, ya saki murmushi yadda yayi mishi, "ina kan shiri na, kuma ina shirya abin da zai min kyau ne, idan har nayi nasara sauke da tsuntsaye uku lokaci guda bana jin duniya zata waiwaye ni, domin kuwa na shirya tsaf." Ya fada yana kurbar wine din. "Bamu fahimci abinda kake nufi ba."
"Zaku fahimta amma yanzu ku fara kai mana, mutanen mu ma'aikatan yadda suna shiga cikin aikinmu zai tafi daidai da lissafinmu."
"Ban gane me kake nufi ba!" Inji daya mutumin. Gyara zama Sajjid yayi sannan ya dauko abin wasan chased ya saka yan statue din guda uku, sannan ya ce musu. "Kamar haka nake nufi." "Au min fahimta yanzu."
"Bayan nan akwai abin da nake so ya gaya min. " Ya fada yana murmushi, "idan ya gaya min dole na saka kome akan inda ya dace, domin ina son bazata."
"Amma kai shege ne, yawwa ya batun dila ne? Kwaro ya kawo mana manyan kaya, kuma kayan nan har mun wuce da su. Scotland da France."
"Hmm! Haka Julie take gaya min, Kwaro bai tab'a kawo kaya masu kyan wanan kayan ba, musamman na bayan yafi kowanne kyau. Gaskiya labarin ya min dad'i."
Lashe baki daya mutumin yayi, yana faɗin. "kuma abin dad'i, irin wanda Mr Williams yake so, ya turo kuɗin aka ce, naso da an bani kayan na gyara kaina kafin a saka kasuwa, karshe duniya ce zata fara morar kayan kafin kai ka samu ragowar yan iska."
***
Wasu takardun da Aryan ya kaiwa Hajiya take dubawa, hankalinta ya tafi sosai ga takardun aka yi sallama, sai da ya kara yi a karo na biyu Hajiya ta amsa tana faɗin ."Barka da shigowa Alhaji kai ne da kanka?" Zama Alhaji Haladu yayi yana kallon takardun gabanta, ya saki murmushi yana ce mata. "Duk da kin sauka, har yanzu baki huta ba?"
"A'a ina duba abubuwa masu muhimmanci ne, sannan sauka nayi ba barin aikin nayi ba. A matsayin Uwa nake taya shi aiki sannan yana da damar ya bani aiki a kamfanin domin na kara taya shi da wasu abubuwan."
"Gaskiya ne amma kuma ai kin wuce lokacin da." Kara kallonshi tayi kafin ta ce mishi. "Na wuce lokacin me?" Dariyar renin hankali yayi ya ce mata. "haba yaushe zaki daina goya su?"
Zare medical glass ɗinta tayi tana murmushi. "Idan ban goya su ba wa zan goya? Wa nake da shi da zan goya idan basu ba? Sune dole na, kuma karfina sune suka sani tsayawa da kafaffuna idan ban tsaya musu ba, gaya min waye zan tsayawa?"
Gyad'a kai yayi yana faɗin .
"Tow Allah ya kyauta, tunda kin mai dasu rauninki." Gyara zama tayi ta ce mishi. "Su ba raunina ba ne, nice nan rauninsu domin tari kawai zan yi su dakatar da abinda yake ransu." "Au tow kice babu wanda ya isa ya tab'a ki, ba tare da sun matsa ba." Ranta ne ya fara b'aci. "Idan babu abin arzikin da ya kawo ka, zaka iya tafiya ina da abin yi."
"Tow Allah ya huci zuciyarki don naga ranki ya fara b'aci dama na kawo takardun Afiyyah ce." Gyara zama tayi tana faɗin. "Au ashe bani ɗaya bace nake son Yaran? Kenan idan har haka ne tow wallahi ka sake gaya min sai na sab'a maka, ko dan uwanka aure ya bashi damar tozartani ba wai don ya isa ba, kuma ko yanzu ba za a sake maimaita abin da ya faru ba, don haka ka sami Amaan Mamman Ba'are, shine yake da alhakin daukar ma'aikata ba ni ko Aryan ko Aneesah ba."
Shiru yayi yana kallon yadda ta maida hankalinta kan aikin gabanta, "tow babu yar wata alfarmar da zan samu ne?" Juyawa tayi ta kalle shi, "ok ajiye a can" ta nuna mishi inda ya dace ya ajiye takardun, ta cigaba da aikinta. "Mun gode Allah ya saka da alkhairi." Ya fada mata, bata amsa ba illa aikin da yake gabanta da take yi, kuma ai tasan yana zaune.
"Sa'adatu baki da burin aure ne? Da sauranki har yanzu idan har mutum ya nutsu zai dauka Majid da Amaan da yan uwansu kannenki ne, sannan a wannan lokacin da kike da sauran kuruciyarki aure ya dace dake ba wani abu ba."
"Idan ka gama bayaninka, zaka iya tafiya." Ta ce mishi tana cigaba da aikinta. "Ina dai kara tuna miki, zama haka ba naki ba ne idan da hali ki bawa wani dama ya goge miki tabon da Mamman ba'are ya miki."
Murmushin da bai kai zuci ba, tayi tana faɗin. "Kuma da yake an gaya maka namiji ne a gabana ko? Idan har wannan tunanin shine a ranka tow ka cire ni bana tunanin wani namiji, don Allah tashi ka fita." Mikewa yayi yana murmushi. "Nasan zaki so kiyi tunani ina jiran duk abinda kika yanke."
"Kana son naci mutincinka ne? Ka fita ka bar min gidana." Ta fada a fusace, shigowar Amaan bai hana shi magana ba. "Kina da sauran damarki, a matsayinki na mace mai lafiya da jini a jika don haka ina kara baki shawara ki yi tunani da kyau. A shirye nake na wanke miki zuciyarki." Cikin wani irin fushi Amaan ya cakumi wuyarshi. "Wallahi sai na karya wuyarka, kai na rantse ka kara cewa kana son Hajiya, sai na kashe ka." Ya janyo shi kiiiiii kamar kayan wanki, ya watsa a waje yana faɗin. "Na rantse Hajiya ta fi ƙarfinka na sake ganin, kiraren sawunka sai na ballaka."
Ya fada yana hayagaga, Amaan kishi yake taya Ubanshi. Domin baya kaunar Hajiya ta kebe da wani. Musamman lokacin da ta amshi kamfanin idan tayi baƙi masu saka hannun jari, tow bake-bake yake zuwa yayi yana kallon ko zata mika musu hannu su gaisa, duk da mugun halinshi yana matukar kishin Ubanshi sannan abinda ya faru a kuruciyarsu da Hajiya yana nan a memory din shi bai manta ba, haka yasa baki daya yake kara jin haushin ganin Hajiya da wani namiji, domin bayan faruwar lamarin abin da wasu suke ta faɗa yasa shi cikin rud'ani haka yasa wani lokaci yake ganin, yunwa da wahala.yasa Hajiya aikata wancan abin. "Kai meye haka?" Hajiya ta tambaye shi tana watsa mishi harara. "Hajiya cewa yayi fa."
"Sai me? Zama zan tayi? Ba zan yi aure ba kenan?" Ware idanu yayi cike da takaici. "Aure kamar ya? Fisabilillahi Hajiya da tsufarki, ki ce aure zaki yi? Ke Hajiya haka ya dace dake?"
Sakin baki tayi tana kallon shi cikin mamaki da takaici. "Kasan ni ba mutum ba ce da zaka ce aure xan yi. Sannu isasshe jikan mallaka'u, aure zanyi kuma na gaya maka idan kaso kada na ƙara ganin kafarka a gidana."
"Wallahi kika yi aure sai na kashe shi, haka kawai don janyo mana abin kunya da magana kice aure zaki yi, Hajiya idan kin manta abinda ya faru wallahi ban manta ba, ba zaki tab'a aure ba, domin cin amana ne, taya zaki..."
Kura mishi idanu tayi tana son jin me zai ce. "ban fahimce ka ba, meye na manta da ku baku manta ba?" Hadiye yawu yayi ganin yadda ta kura mishi idanu. "Babu kome." "Da kome mana, Amaan idan da babu kome mai zai kawo wancan maganar, shi yasa kake min rashin kunya da fitsara? Akan wancan abin da ya faru kake had'a kai da mutanen da suke bi na da sharri."
Murmushi tayi mai sauti tana kallon yadda yake zufa, ga goshinsa da ya sha bandegi. "Kada ka damu, su din zasu maka abin da na kasa maka, amma ka sani duk lokacin da ta kwabe maka bana fatan haka , amma a lokacin zan iya barrata kaina da kai har abada. Ga takardu can ka dauka na Afiyyah zata yi aiki a kamfanin mu."
"Hmm!" Ya fada yana jin wani irin ciwon ciki, da tsoron abin da zai je ya dawo tabbas idan hakan ta faru kwananshi ya ƙare. Da sauri ya haura sama da gudu dakin Majid Mamman Ba'are ya wuce da sauri ya faɗa ban daki, sai da ya katsiye abinda yake cikinshi, ga wani irin ciwon cikin da yake damunshi wanda ya saka shi kasa gane kanshi. Dakyar ya daure wandon shi ya fito yana nishi, koda ya sauko kasa, takardun ya dauka ya fita bai cewa Hajiya kome ba. Itama tana son yi mishi magana amma da yake ya bata haushi sai tayi banza da shi.