Sashe 118
Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Murmushi yayi min,irin wanda ake kira yake sannan ya wuce abin shi. Yana gama shiryawa ya bar min dakin, sauya kaya nayi, ina zaune Mama da Zuzu suka shigo dakin sai Amirah da tayi tsalle ta faɗa kaina, ina dariya. "Darling zaki karya ni fa." "Ai bata da hankali meye haka?" Lafewa tayi a jikina na zabgawa Zuzu harara. "Bana son mugun hali"
"Idan kun gama ga abincinki nikan zan tafi, Zulaihah ki tabbatar taci abinci fa"
"In sha Allah Mama!" Ta fada tana kallon yadda nake tura baki. "Ni gaskiya ki saka shi ya rabu dani, na yarda ko mahaukaci..." Buge min baki tayi, tare da cewa. "Sai na fasa bakin rashin kunyar nan;" inji Zuzu kenan, "Kan Uban can, marin bakina kika yi fa." "Allah ya miki albarka, Zulaihah bari naje na dawo."
"Ki dawo lafiya Mamanmu!" Kuka na saka Mama ta fita tana dariya, sun mai dani mahaukaciya, sai manna min hauka zuzu take. "Ban da mahaukaciyar baban lagaje haba Allah ya baƙi hadadden gaye irin Majid ki ce zaki mana bakinciki ai sai yayar uban mutum."
Ban san lokacin da kuka ya kwace min ba, atoh ni dai na zama a koke. Tun daga lokacin sai rigima ya k'aru shi kan shi ya rasa yadda zai yi dani, tunda na lura idan nayi a gabansu basa damuwa, sai na addabi rayuwarshi da fitina, har aka sallame ni kwananmu daya aka kawo ni marwa tunda muka zo, aka shiga gyara mana jiki ni da Zuzu, shi kuma ya wuce nijar, ashe tun zuwansu Hajiya aka tafi da Zaytoonah.
Tana can tana hauka da tashin hankali, waye ya damu da ita, sai dai ta haɗu da Nana tayi mata wankin babban bargo. Haka aka yi ta gyara min jiki, har tsawon kwanaki duk da bana so amma haka suka matsa min da gyaran nan, tsawon wata guda ana min gyaran jiki duk sati sai mama tazo duba ni. Sati na hudu ne taso lallai muje ayi min sayayyar aure. Amma fir naki da ta dame ni na fashe da kuka. Da Zuzu suka tafi, ni suka bar ni gida, haka suka yi ta sayayya kusan wata biyu suka dauka ana sayayya, ashe akwai gidan Majid din anan Marwa, gidan yana bayan na malam, anan akayi min jere. Su Baraka da Aamirah suna cikin Alkhairi dumu-dumu, domin sun fi kowa farincikin auren da zan yi, haka suka gama jere sati daya muka wuce Nigeria a can aka yi biki da Shagali har angon yazo da shi da Aryan da Amaan, daga nan aka kawo ni Nijar aka cigaba da bikin ranar da aka yi dinner a ranar Yazid yazo. Naci kuka kamar raina zai fita, haka aka gama bikin da zai tafi ya bani kyautatta masu yawan gaske. Sannan ya bar garin, ba zan manta da Yazid a rayuwata ba, yayi min halaccin da babu wanda yayi min ya mai dani mutum ya kuma sayamin farinciki da walwala.
Zuzu da take makale dani, don ta ji labarin jinyar Addah yarinyar nan bata zauna ba, karshe Ummi ta ce mata ta je abinta zata cigaba da kula da ita, nan kuwa azaba take gana mata. Kamar kowacce amarya haka aka kai ni gida na, inda ya gaji da haduwa. Bayan tafiyar kowa ina zaune ni daya aka shigo gidan kamar an diro daga sama. Kallon juna muka yi kafin nace mata. "Ki fahimce ni Zaytoonah." Dariya tayi kafin ta ce min. "Da kenan mai cin amana ashe rufe ni kuka yi keda Mamanki."
"Zaytoona wallahi ban san kome ba." Dake bata da kunya zuwa tayi zata kara tsinka min mari, na rike hannunta. "Ya isa haka don Allah." Na fada da karfi wanda ban san ina da muryar ba. "Ni ban nufe ki da sharri ba, asalima tunda na ganki naga jinina. Amma babu batun cin amana a tare da ni, wallahi Malam da mama suka yi wannan aikin ko shi Majid bai san da haka ba, sai dai kiyi hakuri na miki alƙawarin dole zan rabu da shi ya aure ki, koda kuwa da mutuwata aurenki zai tabbata a tare da shi."
Na fada mata ina kallon yadda ta sauko, domin ina son naga tayi farin ciki sosai. Ita ɗaya ce cikinmu ɗaya idan ban bata abin da take so ba na rasa ta fa? Gara na saka ya sake ni sai ya aure ta Indai da gaske yana sona. Haka nayi ta rarrashinta kafin ta juya ta fita, bayan fitar ta da wani lokaci Amaan da Aryan suka rako shi, ban da zolaya babu abinda suka yi sannan suka fita, zama nayi ina faɗin wallahi sai ya sake ni.
Har ya dawo zai zauna kusa dani na mike, ina banka mishi harara. Share ni yayi ya fita daga dakin, ban kara ganin shi ba sai da na kwanta cikin barci naji kamar an k'ank'ame ni. "me ya kawo Aamirah nan kuma? Mirah ta matsa ki bani wuri kin takura ni." "Shiiii!" Aka fada min, gyara kwanciya yayi tare da k'ank'ame ni. "Kambu!". Na fada da ƙarfi, ina ture shi da sauri na diro daga gadon, na wuce can kuryar gadon, "dawo ki kwanta abinki!" Haka ya sauka tare da ɗaukar pillow ya bar min dakin, na cigaba da barcina har gari ya waye. Nayi sallah da wanka na sauya kaya sannan na koma na cigaba da barci. Shigowa yayi ya samu ina barci cikin salama, mutumin nan baya jiran kanshi ko yaga barci yayi gaba da ni ne sai ji nayi kamar ana d'aga min rigana sama. Buɗe ido nayi na ganshi a kaina, ban san lokacin da na fasa ihu ba. Tare da ture shi ya fadi can, na kare kirjina. "Me zaka min?" Na tambaye shi ina harararshi. "Sadakina zan gani." Da gudu na fada ban daki, ban kuma fitowa ba har ya fita, ina dalili, zai kawo min iyayi.
Tun daga ranar muka shiga wasan buya da shi,ranar da na cika sati biyu ya ajiye min takardar komawa aiki, nayi ta mita don ban so komawa ba, haka ranar na wuni sukuku. Washe gari zai fita kusan tare muka fita, sai uban dokokin da ya labta min, Ni ce hijab har kasa, kai na gaji da azabar da Majid yake bani na kare mutuncin aurena ba kaɗan ba ne shi yasa bana gajiya da zabga mishi harara a cikin nikab din da ya kankama min.
Ina kallonshi yadda ya mike yana waya, kafin can na ga ya fito daga office, wurin Aryan ya nufa can sai gashi ya sake fitowa Aryan ya biyo shi, suka fita bai tsaya ba har suka fita ya zo ya same ni. "Don Allah kada ki tafi wani wurin ko ban dawo ba, ki shiga office dina ki rufe kanki."
"Hmm!"
Ya saka kai ya fita, haka na gama kome har wurin karfe biyar na yamma. Kallon wayar dake gabana nayi. Ashe abin da ya faru Amaan ake tunanin an sace shi, tun safe aka samu wayar shi a bakin wani gidan mai, har zuwa lokacin babu labarinsa, anyi anyi a san inda yake babu labarin shi. Sai wurin karfe shida ina zaune a office Majid din ya kuma shigowa. "Na zata kin tafi ne taso muje gida." Tashi nayi na bishi, a bakin Majid naji labarin abin da ya faru. Murmushi yayi yana faɗin. "Ya za ayi tow?" Kiran Majid din aka yi da wata number.
"Wa ke magana?"
"Ku sake Sajjid ko kuma matar kusa da kai, ta mutu bayan an kashe Amaan Mamman Ba'are." Dube -dube Majid ya fara, a ka ce mishi. "Kada ka damu kanka da niman wanda yake bibiyarku, ina sane da kai kaji Muryar Amaan!"
"Majid kada ka saurare su." Duka aka kai mishi y fasa ihu. "Shi kenan ku bani nan da awa ashirin da huɗu,." Kashe wayar suka yi, a hankali ya zuba min ido yana kallona, "Muje na ajiye ki a gida?" A hankali naji wani irin tashin hankali, ya kamani. "Kai ina zaka?" Murmushi yayi yana furzar da iskar bakinshi. "zan tafi wani wuri ne!" "A'a babu inda zaka, muje gidan kawai a kira yan sanda."
"Akwai abubuwa da ba a bukatar yan sanda a cikinsu." Kallon shi nayi baki sake, cikin wani irin tsoro da tashin hankali nake ji kamar zuciyata zata buga. Lokacin da muka isa gidan, hankalin kowa ya tashi. Kiran Aryan yayi zasu fita na rike hannunsa. "Ina jin tsoro." Na fada kamar zanyi kuka, "ki tsaya a wurin Hajiya da Nana babu abinda zai faru kin ji ko." Jikina ne ya yi sanyi na zauna a gaban Hajiya ina me buga tagumi.