Sashe 125
Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yayunshi kuwa ido suke bina da shi, gani da tsayi sai cikina ya kara min cika da wani irin girma,.kafin wani lokaci cikin wata biyar ya fito, a lokacin aka yi bikin Munaisah mun sha shagali anan Ummi suka hadu da Abdul B, dan gidan Hajiya Hadiza Mamman Ba'are, da fari taso tayi bori Nana tayi tsalle tace ya ga mata, haka aka saka bikin bayan na haihu za ayi.
Bayan kome ya lafa, ya dube ni a hankali ina sauke ajiyar zuciya. "Zahra!" "Na'am! Sojana!" Shafa fuskata yayi yana faɗin. "Ina sonki matar soja."
Kwanciya nayi a kirjinshi ina dariya, magana yake son yayi amma ya kasa fada. Ya kuma kasa cewa kome. "Ina son na rakaki lebo room!" Mintsinin shi nayi ina faɗin.." kaga labor room a kanka!" Shafa cikin yayi, yana dariya. "Allah ka daina razana ni." "Da aka yi me? Kawai dai baki yarda da kanki bane, cewa zan yi miki oya push!" Ture shi nayi ina faɗin. "kyale ni da fushin."
"Zan tafi Mali maganar wasu golden dinmu da suka makale."
"A'a babu inda zaka, ka tura wasu dai."
"Nafi son zuwa da kaina, ba zan wuce two weeks ba baby girl." Idanuna ne suka cika da kwalla, na ce mishi. "Allah ya gani ba da son raina xaka tafi ba " na fashe da kuka, kusan raba dare muka yi ina kuka yana rarrashina, har da murmushinsa.
Washe gari na tashi na taya shi shiri, haka ya tafi office ya bawa Aryan rikon kamfanin. Sannan ya dawo gida ya haɗa kayanshi. Haka kawai jikina yabani na duba wurin kayan sojojin shi na samu babu kodaya. Bin shi nayi falon shi. "Na ga kayan Army dinka babu ko daya." Dafe goshi yayi yana faɗin. "Oh sorry love na kwashe nayi kyauta da su ne." Ya zo ya kanenaye ni yana zuba min kauna, kamar me.
Haka muka raka shi har airport, Nana har da kukanta. "Alhajin Allah yadda ka bani amanar Magaji ba zaka ji kunyar dawowa ka same mu lafiya lau ba."
Kallon Hajiya yayi yana faɗin. "Gobe a wuce da ita Kamaru, a can zata haihu haka na gayawa Mama."
"Ba sati biyu kace zaka yi ba."
"Eh mana, amma ki haihu a gaban Mama yana da muhimmanci." "Kaifa? Cewa kayi zaka raka ni lebo room a ko wane yanayi kuma zaka kace a kai ni wurin Mama? Gaya min akwai abinda kake boye min ne?"
Juya baya Hajiya tayi ta bar mu, amma itama hawaye take sharewa. Aryan ma barin wurin yayi shida Nana Amaan ne ya bari daga baya, ganin xan birkice mishi ya sumbaci goshina. "Ba zan jima ba, zan dawo in sha Allah."
Duk yadda naso ya gaya min gaskiya yaki, Mijina ne da na.mishi wani irin sani lokaci kalilan na san fushinsa na san dariyarshi, sai da aka fara kiran sunayen su ya kara sallama da kowa, nima ya tsaya ya rungume ni, sannan ya juya ya tafi. Kasa kuka nayi na zuba mishi idanu, hawaye na zuba min kamar famfo.
Dafe cikina nayi da yayi mugun nauyi, mutumin nan ko tausaya min bai yi ba, haka ya tafi ko waiwayawa bai yi ba, da yasan yadda yake a rayuwata ba zai min haka ba. Kuka nayi ta yi da karfi tare da ihu da sauri Nana tazo ta ja hannuna, muka bar airport din Da na shiga mota kuwa kuka nake tsakanina da Allah kamar raina zai fita, har muka iso gidan kuka nake........
*Kuyi hakuri ba yawa*
300₦
0016341139 unity bank zahra'u yahaya Ali
Katin MTN 400
#Mai_Dambu ce
[5/29, 07:47] Hlm: BHB270
Kwanaki goma da suka wuce, tun bayan dawowar mu daga biki, ina kwance yake gaya min." Yan mata zan yi baƙi ko zasu samu abinci a kai musu office ɗina." Kallonshi nayi kafin kace mishi. "Me yasa ba zasu zo nan ba?" Karamin murmushi yayi ya ce "min sojojin ne zan bari su shigo min cikin gidana." Zumbur na tashi zaune tare da zuba mishi idanu. "Amma wasa kake min ko?"
"Ban gane wasa nake miki ba? Zan miki wasa ne don jin dadina?" Ya faɗa yana gyara zaman tie ɗinshi. Cikin fushi na mike zan fita ya riko ni. "Wani abu aka miki mara daɗi ko bakin ne bakya son zuwansu?" Ban san me yasa na tsani harkar sojojin ba, kawai na fashe da kuka. Na gaya mishi. "Ni harkar sojojin ne bana so, kuma bana sha'awar kayi." Shiru yayi kafin ya ce min. "Ok idan na fahimta bakya son hidimar soja kawai na zauna a matsayin civilian?" Gyada kai nayi, murmushi yayi sannan ya ce min. "Shi kenan dama sun zo min Allah sanya alkhairi ne, amma tunda bakya so a yi abincin a kai musu."
Gyada mishi kai nayi, ina nufar hanyar kitchen, shi kuma ya fito yana kallon yadda nake tura baki. "Allah ya huci Maman Mamman Abdul Majid Mamman Ba'are." Watsa mishi harara nayi, na ci-gaba da aikina, shigowa Zaytoonah tayi ta gaishe shi cikin girmamawa sannan ta ce min. "Girki zaki yi?"
"Eh baki zai yi anjima za a kai office din shi." Zuwa yayi ya rungume ni ta baya. "Madam ayi musu kome special." Kwantar da kai nayi a jikinshi, ina dariya. "Na ji amma sake ni kada na sangarce na ce na fasa!" Da sauri ya fita, mikawa Zaytoonah aya nayi ta wanke, yana tsaye yana sani magana. Kai hannu yayi zai tab'a min danyen kazar da na Ciro na dauki muciya na ce mishi. "Oya muje ko na ma ka maka!" Zaytoona sai dariya take min tare da gyara tafiyar shi wai yana koyan yadda nake tafiya.
"Allah na ganinka ai!"
"Tow Aunty Zahra!" Ya faɗa yana sauka a step din. "Zaka dawo ka same ni."
"Zan wuce wurin Uwargida Nana!" Share shi nayi ina me cewa. "Takaici bai tashi gaya min aikin ba sai yanzu." "Ba mamaki shima da safe nan suka mishi magana." Haka na cigaba da aikina, ina kallon yadda take min aikin itama, tana wanke ayar ta rege, nasata ta nika min, ni kuma na wanke shinkafar tuwo na saka a cikin tunkuya, na duba fridge na debo kayan miyar ganye. Na bata ta gyara min ni kuma na dauki zallar kayan miya na raba biyu, na nika sannan na sake daura jollop din cus-cus wanda ya ji kayan lambu, na zuba musu sai dan meat pie da yar cake, kafin karfe biyu da rabi, mun kulla tuwo a leda, muka saka a manyan kulolina. Idan ina wani aikin ita karbar wani aikin take.
"Assalamu alaikum, mutanen sama me ake ta mana ne gida ya bude da kamshi." Inji Anisah, wacce nayi imanin tana cikin masu zuga Zaytoonah, ganin yadda taki daukar zugarta yasa ta dawo jikina. Dauke kai Zaytoonah tayi tana cigaba da aikinta. "Auta ya kike?" "Hmmm lafiya lau, Aunty Zahra." Ta fada tana kallon yadda nake shirya kome a cikin basket. "Babu tab'i ne?" "Nan aka fi auki!" Inji Zaytoonah. "Koma me mutum ya fada nan dai gidan Ubana ne." Ko ta manta cewa cikin mu daya da ubanmu ɗaya. Kafin na bude baki nayi magana sai jin Muryar Amaan muka yi yana faɗin. "Wannan wani irin jahilci ne? Ke wata irin mahaukaciya ce wawuya kawai." Shiru tayi tasan halin shi mutuncin shi kaɗan ne a da can, shi yasa bata amsa ba da wani ne ramawa zata yi.
"Kyale ta Amaan, idan ta gama rashin kunyarta ta bar min part dina." A fusace ta bar part din, Ni kuwa ban san lokacin da zafin rai ya kwashe ni na bita ba. Suna kirana amma ko kula su banyi ba, na sauka kasa na samu tana fadawa Hajiya wai mun mata rashin mutunci. Hajiya ta ce. "Karya ne wannan zancen da Zaytoonah kika ce xan yarda ban da Zahra sai dai idan akwai abinda kika mata."
Ina sauka na zauna ina haki. Fulatanci na juyawa Hajiya don sau dayawa muna sakewa muyi, yadda nake hakin yasa jikin Hajiya yayi sanyi na ce mata tabbas Zaytoonah zata bar gidan, amma ba don maganar Anisah ba. Don takaici girkin da ba a kare da ni ba kenan, Zaytoonah ta karasa don ba zan iya komawa sama ba.
Ina zaune suka sauko da kome har da Na Hajiya da Nana aka kai mata Amaan ya wuce da na Office, anan nayi sallar Isha, tow tun da ya dawo na fahimci yana cikin damuwa, lokaci guda na ga ya je ya saka kayan sojojinshi a gaba, cikin jin haushi don ni yanzu abu kad'an yake harzuka ni, kuma da yake likita ne sai baya biye ni.
Haka na gama kallon shi na juya na bar mishi dakin shi na tafi nawa, ina zaune don na kasa barci sai gashi nan. "Lady lafiya kika dawo?" "Amma kasan haduwar kaddara ce a barikinku?" Zama yayi a kusa dani. "Na sani!" "Kasan nasan cewa saboda ni wannan mutumin yayi ta bibiyarka?" A hankali na fashe da kuka me cin rai. "Ban ga laifinka ba, amma aikin soja na tsane shi."
Rungume kaina yayi yana shafa bayana. "Kiyi hakuri ba zan koma aikin soja ba, ina kallon kayan ne." Haka ya gama rarrashina, sannan ya bude wani babi na daban yana daura min karatunsa me saukin dauka da wuyar aiwatarwa.
Wannan shine abin da ya faru, na kara fashewa da kuka, a lokacin da naji Nana tana faɗin , "suma sojojin nan munafukai ne, akan me zasu ce yazo ya taimaka musu da wani aiki tunda sun san ya bar aikin sojan!" Wani irin kuka na fasa ina rike cikina. "Wato yaudarata yayi ya ce min ya bar aikin soja ashe ba haka ba ne." Nayi ta surutu, haka muka isa gida a daren ranar a asibiti na kwana, har da drip aka saka min.
Kwana biyu ina jinya, Zaytoonah ce a kaina, Mama tazo da kanta kamar yadda ya ce a kai ni. Sai gashi tazo. "Ke baki da hakuri ne?" Kallonta nayi sai ga hawaye. Fada ta shiga min kafin tayi kasa da murya alamar rarrashin. "Kiyi hakuri, bukatar haka ce ta taso, ya sha gaya min yadda yake son ki haihu a hannunshi, idan kika saka damuwa a ranki zai tab'a cikin jikinki."