← Book details Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 95 OF 138

Sashe 95

Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lokacin da aka dama furar har asibiti Amaan ya kai musu shi da Zaytoona, suka sha har da santi, shi dai bai ce kome ba sai dariya da yake yi. "Amaan babu kari ne?" "Yana gida idan ka dawo sai ka sha."
"Tow me yasa ka kawo min kad'an?" Harararshi Amaan yayi yana faɗin. "Kuma ajiye ni kayi da zan na maka hidimar kawo maka abinci?" Banza yayi da shi.
"Maganar gaskiya kinda din nan ya min dad'i."
"Ai fa!" Ya faɗa yana kunshe dariya, haka ya zauna har Majid din ya gama suka dawo gida, ya nufi kitchen din Hajiya yana dube-duben kinda. "Ai ba sai ka duba ba, bari na duba maka." Haka ya dauko mishi, Hajiya ta kara gyara kindirmon har da kwakwa da dabino, mutuminku yasha tass abincin da bai ci ba kenan, ya kuma diba ya kaiwa Nana, kallonshi tayi tana faɗin. "Ai Aliyu ya kawo ashe yarinyar nan yar arziki ce?" Zama yayi yana ajiye mata kofin da kunshin kilishin da ya sayo mata. Fuskar shi dauke da son jin karin bayani yake kallonta.
"Yarinyar nan dai da Aliyu yake tare da ita, ta marad'i nan." Ta shiga mishi bayani, ai Zahra ce ta dawo daga Bauchi ta kawo musu kindirmon. Wani irin abu ne ya tokare mishi kirji, ya mike fuuuuuu ya nufi gidan Hajiya. "Ka ji da shi dai Gulmamme!" Nana ta ja kunshin kilishin ta fara ci abinta, tana kurbar fura me sanyi ina zata iya da takaicin Majid, don ta lura babu babban dan hassada irin Majid, ita bata ga wani illa akan yarinyar nan me dan karen kirki ba.
Tsaki tayi daidai shigowar Hajiya Hadiza, "Hajiya Nana." Wani haɗe rai Nana tayi tana faɗin. "Wannan dai mugun hali ne da mugun abu, taya zaki tawo babu labari."
"Ayya Nana don nazo ganinki!"
"Ina Abdul Majidu, ina son abin duniya ya rufe mishi idanu, a tow ga Alhajin Allah nan baya gajiya da hidima da ni."
"In sha Allah zai yi hidima dake."ta faɗa tana rarrashinta.

A can gidan Hajiya kuwa,Majid yana shiga ya kurawa Amaan idanu. "Wato kai da hannunka zaka ciyar dani guba."
"Innalillahi'wa'inna'ilaihi'raji'un! Nana ta gaya maka ne?" Ya tambaye shi yana zaro idanu, cire takalminshi yayi zai bi Amaan da gudu ai kuwa ya koma bayan Hajiya ya tsaya. "Lafiya!?" Ta tambaye su, "Hajiya Fisabillahi har ni Amaan zai bawa abu." "Wani abu ya baka?"
"Da yanzu na mutu fa."
"Ban gane da ka mutu fa?"
"Hajiya wai don Zahrah ta kawo min, kinda mun sha har na kai mishi asibiti shine yaji labarin a wurin wancan tsohuwar yazo yake jaraba."
"Yanzu akan kasha furar kake ihu."
"Hajiya na zauna a cikin hausawa da fulani yarinyar nan mayya ce." Ya ce ba tare da ya fahimci me zai fada ba. "Kana nufin ta lashe kurwan mu kenan." Yarda takalminshi yayi yana me barin falon ya ce musu waye ya sani, idan ma kun dauko abin da ya dame ku, can zata kare muku." Ya wuce cike da takaici, Hajiya da Amaan da Aryan suka kwashe mishi da dariya, sake hawa yayi kamar yeast. Don dama haushi ya ishe shi. "Hajiya idan ya gano ita ce sakatariyarshi ya za'a yi da shi?" "Ba zai tab'a bijirewa umarni na ba."
Murmushi da farinciki suka yi, ana saka ran za ayi board meeting next month, haka Hajiya take jin zata ja zarenta da kyau. Sai dai kuma ba haka abin yake ba, kamar yadda take da karfin gaske akan kamfanin suma masu hannun jari a kamfanin suna da yadda za su yi, musamman da Tani suka sake kulla wani makirci akan wannan gabar, ai sun san Majid bai da experience akan tafiyar da kamfanin idan suka yi nasarar sako sakatariyarshi daga ɓangaren members na kamfanin. Duk wanda aka hada shi da ita zata zame mishi alakakai. Wannan abin sun yi ne a tsakaninsu, amma sun jima suna kullawa a gaban Amaan, shi yasa Shekara ɗaya da aka dauko maganar sakatariya ya zauna ya gayawa Hajiya shirin Sajjd da wasu membobin kamfanin.
Idan har shirinsu ya tafi yadda ya dace, ba makawa Majid zai shiga tashin hankali. Domin zasu yi amfani boycott suyi ta Blackmailing Majid har sai ya yarda ba zai iya ba. Wannan yasa da kanta tayi ta bin manyan jami'oin ƙasar tana bibiyar dalibai masu hazaka, har ta samu Zahrah tare da taimakon Hajiya Zainabu Isma'il Wodabbe. Ta hada ta da Zahra sannan bayan sun ga Zahra basu mata magana ba, shine ta tura Amaan, shi kuma yaje bai san shirin Hajiya ba ya dauko Zahra don kanshi. Sai ya kasance daga shi har Hajiya buri daya suke da shi akan kamfanin, kuma lokacin da aka kawota da aikin da tayi ya kawowa Hajiya tare da bata shawarar ko zasu dauki Zahrah a matsayin sakatariyar Majid, duk da itama da nata gudunmawar amma kuma sai.ta biye mishi don kada ya fahimci itama tana ƙoƙarin taimakon Majid, ta bar mishi yayi na shi ƙoƙarin.
Lokacin da zai tafi wurin Zahrah a marad'i, sai da ya kuma gaya mata da takardar daukar aikin kuma ta goya mishi baya, ya je wurin Zahran haka yasa shi kara jin lallai yana da abin da zai yi. Murmushi Hajiya tayi a karo na babu adadi. "Kuyi ƙoƙarin tunzura shi yace baya buƙatarta tunda kun ga yadda yake a birkice."

Muna waya da SK Lamido, sosai har yake gaya min zai zo nijar wurin Princess. Don dama ya gaya min akwai aikin da zai kawo shi, amma sai ya fara sauka a Niamey kan yazo mana, nay matuƙar jin dadi don ko ba kome kai ma kana da masu zuwa gare ka. Don ko bayan dawowata Ya Babangida ya ce zai zo amma sai ya samu kudi, na ce mishi idan zai zo ya gaya min kawai na tura mishi kudin zuwa. A wannan rayuwar me ya fi maka dad'i kai da danginka da al'ummar Musulmi da suke yin ka.
Haka na sha zaman gida, a lokacin na gama kome, kirana aka yi a makaranta, abubuwa dai har da bikin gama makaranta suka shirya mana. Kasa da sati biyu.
Haka yasa muka yi ta shiri,babu kama hannun yaro. Kaina ya dauki zafi bana gane kome sannan babu wanda nake da shi da zai taya ni, na gayawa Ya Babangida halin da nake ciki, a lokacin ya ce zai zo da Amaryarshi, ba karamin murna nayi ba. Haka dake bikin ya rage kwana uku, SK Lamido yazo ai tunda yazo Amirah ta makale mishi, shi kenan na samu hutu na turawa Hamma Amaan sakon bikin gama makaranta, a kan lokaci ya gaya min zasu zo. Haka kuwa ranar bikin duk mun tafi makaranta, Amirah tana wurin Sk Amaan da Hajiya sun zo, uban yan girman kai bai zo ba, abin burgewa har da tsohuwa Nana. Har wurinsu naje na gaida su. "Fadime ya baƙi yi kwalliyar zamanin nan ba?" Ya Babangida da suka gaisa, na gabatar musu da shi a matsayin babban Yayana. Hango Amirah Amaan yayi ya bude baki. Sauka tayi da sauri ta tawo wurina ya dauke ta, dressing ɗinmu iri daya. Don rigima ta saka na saya mata yadin aka dinka mata, har da hular da ta saka. Haka farin code lace din da yake jikina riga da skirt, ita kuma aka yi mata short gown da shi, ba karamin kyau yayi mata ba.
"Yar nan, amma kin yi kyau ina ta Addu'a akan Alhajin Allah. Ina ga sai na hada da Umara domin Alhajin Allah kamar an saka mishi hannu akan lamarin aure." "Nana lokaci ne aure da mutuwa, da haihuwa idan lokacinsu yayi sai ki ga anyi?"
Haka muka koma rumfa, ni na koma wurin mu,inda muke zaune aka fara gabatarwa har zuwa kan yadda aka kafa makarantar da kome da kome, kafin aka fara kiran department da ɗaliban da suka yi kokari, department ɗinmu ne na uku, ban yi tsammanin za a kira ni ba, sai jin nayi Fatima Abubakar, wani yarrrrr naji wato ni. Kallona aka fara yi lokacin da na mike, na nufi inda pro din yake ya mika min shaidar kammala jami'a, da matsayin First class, wani irin kuka ne ya kwace min sannan manyan kamfanonin irinsu GOLDEN EMPIRES da wasu kamfani suna son na saka musu hannu zasu dauke ni aiki. Sannan batun shaidar halin da Kyakyawar fata da nutsuwa da kamun kai na same shi, haka nayi ta samun kyauta a wurin mutane.
Bayan an tashi taro aka yi ta hotuna, ina tsaye Abdullahi yazo, bayan mun gaisa ya mika min wani katon kwando. "Ina taya ki murna, ina Baby Mirah." Nuna mishi ita nayi a wurin SK, shi kuma na shi ƙaddarar kenan ya saka Amirah a gaba su yi ta hira sai ka dauka abin arziki suke fada nan kuwa shiririta ce zalla. Haka aka gama taro. Aka watse Yan Niamey suka koma washe gari Ya Babangida da SK suka bar marad'i, nima kuma saboda rokon da Amaan yayi min na saka hannu zan fara aiki da su, na nemi Aseem ban same shi ba, gidan da ya saya min na Niamey na tattara kayana na koma can, nan din na barwa su Maman Barakatu,da muka sha kuka kamar me. Don shakuwa na kuma gaya mata don Allah idan suna son abu kada ta boye min ta gaya min. In sha Allah idan bai fi karfina ba zan yi.
Chapter 95 · 0% Book details